Hesperian Health Guides

Domin tsaida zubar jini ga (jarirai) sabuwar haihuwa

Jarirai Sabuwar Haihuwa dakuma Shayar da Mama

Vitamin K, phytomenadione, phytonadione


Jiki yana yin amfani da vitamin K ne domin tsaida zubar jinni. Amma jarirai ana haifar su ne ba tare da isashshen vitamin K ba. Sabodahaka, idan suka fara zubarda jini saboda wani dalili sai akasa shawo kansa. Idan (jariri) sabuwar haihuwa ya fara zubar da jinni ta kowanne ɓangare na jikinsa (wato ko ta baki, ko cibiya, ko ta takashi), za a iya bashi vitamin K domin kare zubar jini dayawa. Za a iya kuma bawa bakwaini da kananan jarirai (wanda nauyinsu yake kasa da kg 2) domin kare zubar jini, saboda sun fi kowa damar zubar da jini.

NBgrninject.png Yadda ake amfani (da shi)
Yi allurar mg 1 (mg 1 ampule guda ɗaya, ko ½ na mg 2 ampule) ta vitamin K daga ɓangaren waje na cinyar (jariri) acikin sa'o' i 2 na farkon bayan haihuwa.

Kada a ƙara yin allurar, bazata taimakaba sai dai ta cutar.



This page was updated:05 Jan 2024