Hesperian Health Guides

Jarirai sabuwar haihuwa dakuma shayar da mama

Kundin bayanan lafiya na Healthwiki > Sabon littafin A inda babu likita > Jarirai sabuwar haihuwa dakuma shayar da mama

A wanna kashin:

Kulawar bayan haihuwa


A sa'ar farko ta haihuwa, zaki iya taimakawa wajan wanzuwa dakuma samar da lafiya mai ɗorewa ga jariri ta bin waɗannan hanyoyin;

  1. Ki tabbatar jaririn yana numfashi sosai.
  2. Ki bashi ɗomi ta hanyar rungume shi fata-da-fata da mahaifiyarsa.
  3. Ki taimake shi (jaririn) ya fara shan mama.

Shin jaririn yana numfashi da kyau?

Lokacin da aka haifi jariri,kuma a lokacin da ki ke ƙoƙarin gogeshi kuma ki ke sada shi da maman mahaifiyarsa, sai ki duba kiga, ko yana numfashi da kyau. Idan kika yi hanzari wajan kulawa a irin wannan lokacin zaki iya ceto rayuwar jaririn da baya numfashi.

NWTND Newb Page 1-1.png
Ƙafafu da hannuwa masu ƙarfi
Launi mai kyau

Yana numfashi sosai ko kuka
NWTND Newb Page 1-2.png
Gaƃoƃi sunyi sharaf suna reto
Launi ja mai duhu, ko ya canja zuwa shuɗi, ɗashewa ko rawaya-rawaya

Da ƙyar yake numfashi ko, kuma babu alamar numfashi ko kuka
Wannan jaririn yana da lafiya Wannan jaririn yana buƙatar taimako.


Idan jariri baya mutsi, Yayi shuɗi, ko kuma baya numfashi..

To kada ki dake shi (maimakon haka, bi waɗannan matakan kamar haka:

  1. Cire majinar da take cikin bakin jaririn, ta hanyar share ta a hankali da yatsan ki wanda kika nannaɗe shi da ɗan ƙyalle mai tsafta. Ko kuma kiyi amfani da sirinjin (allura), ko kuma abin zuƙowa domin cire majina daga bakin (jaririn), sannan kuma hancin sa.
  2. Hoton dake sama, yana nuna yadda ake cire majina da yatsa
    Jariri a kwance, kumatunsa yana taƃa kirjin mahaifiyarsa.
  3. Riƙa shafa bayan jaririn a hankali: Yi amfani da tawul mai tsafta domin ɗumama dakuma busarda shi (jaririn), a lokaci guda kuma ki riƙa shafa ƙarƙashin ƙafarsa. Wannan zai taimaka wajan saka shi (jaririn) yaja ƙaƙƙarfan numfashi.

    To idan jaririn har yanzu bayyi numfashi ba, ko kuma ya daina numfashi, to anan dole ayi masa Busar Numfashin Ceto.


Numfashin Ceto: Yadda ake yinsa shi ne

  1. Kwantar da jaririn akan wure mai tauri, teburi ko daƃe, ki saka zani a ƙarƙashinsa, kuma ki ɗan rufe shi da shi domin ya sami ɗumi.
  2. Ki ɗan ɗaga haƃar jaririn kaɗan, ta riƙa kallon sama, kuma zai taimaka idan aka saka dan nannaɗaɗɗen zani a ƙarƙashin kafadarsa (jaririn). Wannan zai sa maƙogwaronsa ya buɗe domin numfashin (shigar iskar da za'a busa).
  3. Ga jariri haƃarsa tana kallon sama.
    baby with chin touching her chest.
    Jaririn ya kalli sama kamar haka. Kar ayi haka.
  4. Buɗe bakin ki sosai. Lulluƃe hanci dakuma bakin jaririn da leƃukanki.
  5. Fuskar jariri, ana nuna wajan da zaki rufe da leɓunanki.
    Ki lulluɓe inda aka zagaye da bakinki.
    Zaki iya amfani da jakar leda ko abin rufe baki, maimakon bakinki
  6. Busa iska cikin jaririn a hankali. Ki riƙa busawar kaɗan-kaɗan da sauri-da-sauri duk bayan daƙiƙa 1 ko 2. Ki yi a hankali karki busa da ƙarfi domin gujewa rauni ga 'yan huhunan jaririn.

    Bayan duk busa, sai ki ɗan tsaya domin jaririn ya fitar da numfashi.
    Ga wata mata tana ƙirge tsakanin busa.
    Ga wata mata tana tunani a lokacin da take busawa jaririn iska.


    Idan ki ka ga kamar iska bata shiga ko kuma ta daina shiga. Sai ki sake ɗaga haɓar jaririn sama ki tabbatar tana miƙe kuma maƙogwaron a buɗe yake. Sannan ki sake gwadawa (kamar da).

    Idan jaririn ya fara kuka, ko kuma yana numfashi a ƙalla sau 30 a minti ɗaya, shi-da-kansa, to yanzu komai yayi dai-dai. Daga nan sai ki sakashi a ƙirjin mahaifiyarsa domin yasha ɗumi. Zai kuma wartsake. Amma ki lura daga nan zuwa 'yan sa'o'i, shin jaririn yana nan a launi mai kyau? Shin yana numfashi a sauƙaƙe? Idan launin jikinsa ko bakinsa ya canza ko yana numfashi da ƙyar. To ki nemi taimako (da gaggawa).

    Idan bayan minti 20 da yin busar numfashin ceton, jaririn bai fara numfashi da kansa ba, to wataƙila ya mutu. To a irin wannan lokacin na firgici sai ki kasance tare da wannan iyali, domin suna da buƙatarki.

A baiwa jariri ɗume da fatar mahaifiyarsa



Jariri yana kwance acikin zani a kan kirjin wata mata.
A sada jariri fata-da-fata da mahaifiyarsa.
Kibiyar dake nuna kan jariri tana nufin: A A rufe kan jaririn da hula ko zani

Mafificin wuri a wajan jariri sabuwar haihuwa shi ne jikin mahaifiyarsa.


Jariri sabuwar haihuwa dole ne a ajiyeshi a waje mai ɗumi kuma busasshe. Ɗumin jikin uwa ya isa ya ɗumama jaririnta. Kada a ɗauki jariri daga wajan mahaifiyarsa domin duba shi ko yi masa wanka. Jariri baya buƙatar wanka ana haihuwarsa nan take. Kuma wanka ma na iya sa shi ya kamu da matsanancin sanyi. Bubu wani dalili da zai sa a raba jariri da mahaifiyarsa sai dai idan numfashin ceto za a yi masa.

  • Busar da jaririn a lokacin da ki ke sada shi da fatar mahaifiyarsa.
  • A ɗumama jariri ta hanyar sada shi da kirjin mahaifiyarsa tsirara. Sannan kuma a rufe su da mayafi su biyun. Kuma a riƙa saurin canja jiƙaƙƙen abin shimfiɗa da busasshe domin jiƙaƙƙen abin shimfida na iya sa jaririn yaji sanyi sosoi.

Idan ya zama dole a aika da uwa zuwa ga asibiti ko kuma domin wani dalili bazata iya riƙe jaririn ta ba, to sai uba ko wani daga cikin 'yan uwa ya riƙe shi fata-da-fata.

Ga wata mata tana riƙe da jariri a kirjinta, a ƙarƙashin kayan jikinta.

Fara bada mama

Jarirai sukan fara bacci a cikin sa'a ɗaya da haihuwar su. Saboda haka, sai a bawa jariri mama kafin ya fara bacci. Idan kuma bai sha ba nan take, sai ayi ƙoƙarin tatso 'yan ɗigo kaɗan na nonon uwar na farko a sa masa a leɓen sa ko ya buƙaci ya sha. Ko kuma a ɗan gogi kumatunsa da kan nonon barbar tasa. Babu abinda yake tabbatar da lafiyar jariri kamar shan mama. Domin ƙarin bayani akan shayarda mama dakuma muhimmancin bada nonon farko wanda ake kira da 'COLOSTRUM' (da Turanci) danna nan.

This page was updated:27 Yul 2020