Hesperian Health Guides

Shayar da nono

In this chapter:

NWTND Newb Page 18-1.png

Mai jegon (da bata taɓa haihuwa ba) zata iya buƙatar taimako wajan shayarwa. A taimake ta ta sami nutsuwa. A tallafe ta da abin shimfiɗa da filo domin ta zauna sosai cikin jin daɗi. A faɗawa 'yan gida da sauran baƙi da su ɗan barta ita kaɗai tare da jaririn. A ƙara mata ƙwarin gwiwa. A hankali shayarwar zata yi mata sauƙi.

Nonon uwa yafi duk wani nau'i na abinci ga jariri.

Kare kai daga tsagewar nono mai ciwo ta hanyar shayarwa a yanayin daya dace. A juya dukkan jikin jariri zuwa ga mahaifiyar a tabbatar wuyansa bai lanƙwashe ba. A tsaya har sai ya buɗe bakinsa sosai. Sannan a sadashi da nonon. Kan nonon dakuma kewayen (nonon) ya kasance a can cikin bakin (jaririn).


NWTND Newb Page 18-3.png
Baki a buɗe sosai
Kan nonon a can cikin bakin jaririn
Leɓen ƙasa a naɗe daga ƙarƙashi
Jariri a riƙe kusa da jikin mahaifiyarsa
NWTND Newb Page 18-2.png
Kamar haka. Ba kamar haka ba. Yanayin riƙo marar kyau zai iya kawo tsagewar kan nono.

Nonon farko kamar ruwan zinare yake

Nonon farko wanda ake kira da colostrum yana zuwa ɗan kaɗan, amma ya wadace jariri sabuwar haihuwa. (Cikin jariri yakan iya riƙe 'yan cikin cokula ne na madara). Colostrum yana da danƙo kuma launinsa rawaya-rawaya ne, amma duk da kamarsa da ban take, shi ne mafi can-cantar abinci ga jariri sabuwar haihuwa. Yana ɗauke da antibodies (garkuwar jiki) - wato wani abu da jikin mahaifiya ke samarwa wanda yake kare jaririn daga kamuwa da cuta. Kada a zubar da nonon farko. Yafi kowanne irin magani kima a wurin jariri. Shayar da nono a kwana biyu na farkon (haihuwa) shima yana da muhimmanci, shi yake samarda nono na asali wanda mahaifiya take fara samarwa acikin kwana 3 na bayan haihuwa. Iya yawan shan maman da jariri keyi iya yawan nonon da mahaifiyarsa zata samar.

Shin jaririn yana samun isashshen nono?

Kada ki bari wani ya gaya miki ai baza ki iya samar da isashshen nono ga jaririn ki ba, musamman ma a 'yan kwanakin farko lokacin da jikin ki ya fara samar da nonon.

Saboda takura daga waɗansu, dakuma kokwanto, masu jego suna bawa jarirai sabuwar haihuwa abincin yara na gwangwani ko kunu ko kuma wani nau'in na abinci. Irin wannan nau'in na abinci ɓata kuɗi ne kawai, kuma zai iya haifar da gudawa ga jariri. Gudawa tana sa jariri ya rage nauyi ya kuma yi rauni. Kuma amfani da irin wannan nau'in na abinci yanasa samar da nonon mahaifiyar ya ragu. Wannan zai sa ta daɗa tabbatar da cewa bazata iya shayar da jaririn da nono ba kaɗai. Idan ke ma'aikaciyar lafiyace zaki iya hana yaɗuwar wannan matsalar ta hanyar nunawa masu shayarwa zasu iya shayar da jariransu. Ki taimaka musu wajan sanin yadda ake riƙe jariri, amma ki ƙyale mahaifiyar ta koyi shayarwa da kanta ita kaɗai. Ki tausasa wajan magana kuma kiyi haƙuri.

Samar da isashshen nono

  • Yawan shayarwa. Iya yawan shayarwarki iya yawan nonon da zaki samar.
  • Ki riƙa yawan shan abu mai ruwa-ruwa kuma ki ci abinci mai yawa. Ciyar da jaririn ki ta hanyar ciyar da kanki!
  • Yawan hutu. Lokacin da mahaifi da sauran dangi suke taimakawa da 'yan ayyuka mai jego zata fi kula da sabun jaririnta.

Iya yawan shayarwaki, iya yawan nonon da zaki samu..


Dayawa daga cikin jarirai sabuwar haihuwa nauyinsu yakan ragu a satin farko, wannan babu komai. Bayan nan raguwar nauyi yana nuna alamar rashin samun isashshen hutu. Haka kuma jarirai basa yawan yin fitsari a ranar farko, amma bayan nan yakamata su fara yin fitsari duk bayan ‘'yan sa'o'i. Idan jariri bai yi fitsari dayawa ba bayan kwanaki biyu, to, baya samun isashshen nono. To yaya kuma idan jariri yana yawan shan nono amma baya yawan yin fitsari ko baya girma? To, a irin waɗannan halayi masu wuyar faruwa, to kina da buƙatar samar masa da wata madarar. Kada ki bashi suga ko ruwan shinkafa. Kada ki bashi wani abincin gwangwani har sai kin tabbatar zaki iya bashi irin yadda ake bukata (ƙara masa ruwa kuma yana haifar da gudawa dakuma rashin lafiya). Kuma kada kiyi amfani da bilinboti (feeding bottle), su na da wahalar tsaftacewa, sabodahaka suna yaɗa kwayoyin cutar gudawa.

Dole ne a bawa jariri wani nonon idan mahaifiyarsa ta mutu, ko kuma basa tare, ko kuma bata samar da isashen nono da gaske, wanda ba kasafai yake faruwa ba. Za'a iya sa wata matar ta shayar da jaririn nono. Kuma tana (mai shayarwar) da bukatar ayi mata gwajin cutar ƙanjamau, saboda kariya, domin jaririn zai iya kamuwa da cutar ƙanjamau ta hanyar shan nono. Wani zaɓin kuma shi ne a bawa jaririn madarar dabbobi.

Kaso 2 na madarar saniya ko ta akuya da
NWTND Newb Page 20-1.png
Kaso 1 na ruwa
Ƙara babban cukali 1 na suga

OR
1 part sheep milk
1 part water
1 large spoonful of sugar

KO
Kaso 1 na madarar tinkiya
Kaso 1 na ruwa
Cikin babban cokali 1 na suga

Ki ɗan tafasa haɗin domin kashe ƙwayoyin cuta. Sanan ki bari ya huce sai kibawa jaririn da kofi ko cokali

Tatsar nono da hannu

NWTND Newb Page 20-2.png

Idan ya zama dole ki je aiki ko kuma zaki bar jaririn saboda wani dalili, zaki iya tatsar nonon domin idan ba kya nan wani ya bawa jaririn.

  1. Ki wanke hannuwanki dakuma ɗan mazubi. Ki tafasa mazubin idan zai yiwu.
  2. Tatsar nono acikin mazubi.
  3. Kama kewayen baƙin nan dake jikin nonon ki da 'yan yatsunki. Ki danna ƙirjinki (da nonon a hannun). Sannan sai ki matse 'yan yatsunki kina murzawa har zuwa kan nono. Ɗan saki kaɗan sanan ki riƙa tuna jaririn alhalin kina tatsar nonon-wannan yana taimakawa nonon ya fito.

    Nono zai iya kaiwa sa'a 8 idan babu zafi sosai (bai lallace ba). Idan kuma da sanyi ne zai iya fin haka.


Thrush

NWTND Newb Page 21-1.png
Yi amfani da ɗan ƙaramin ƙyalle mai tsafta domin shashshafa maganin cikin bakin jaririn.

Wani roɗe-roɗe ajikin harshe ko kuma daga cikin kumatu wanda yake faruwa saboda shan nono, zai iya kasaancewa alamar cutar yeast wadda take kama baki, kuma ana kiranta da thrush (da turanci). Irin wannan cutar tana iya yaɗuwa zuwa kan nonon mahaifiya kuma zata iya haifar da jan (baki), ƙaiƙayi dakuma zogin (baki).

Yi ƙoƙarin ɗauraye kan nonon da ɗan ruwan khal (vinegar) sannan da ruwa. Ko kuma idan baki da ruwan khal, sai ki rika ɗauraye kan nonon ki kuma goge shi duk bayan shayarwa. Idan wannan baiyi magani ba to sai ki shafa shan-shan-bale ɗan kaɗan akan nonon sau 2 ko 3 a rana. Kuma a shafa a bakin jaririn sau 1 a rana. Wannan zai sa launin komai ya koma ruwan bula, amma babu komai (da faruwar hakan).

Idan shan-shan-bale bai taimaka ba, to sai a bawa jaririn nystatin.

Idan cutar yis ɗin baki ta cigaba da dawowa, to jaririn zai iya kasancewa yana da wata matsalar wadda take ragewa (garkuwar jikinsa) karfin yaƙar cutar.

Cewo, kumburi, tushewa ko cutar nono

NWTND Newb Page 21-2.png

Wani lokacin nono yakan toshe ƙofar dayake fitowa (wato 'yan magudanan dake cikin mama wadanda suke dauke da nono). Wannan sai yasa maman yin kumburi, yayi ja kuma da zafi. Ba daɗewa kuma sai cuta ta fara.

Alamomi

  • Wani waje ja, mai tauri ajikin nono.
  • Cewon nono, dakuma lokacin da ake shayarwa.


Idan da akwai zazzaɓi, to hanyar data toshe ta kamu da cuta.

Magani

  • Hutu dakuma shan abu mai ruwa-ruwa.
  • Ki riƙa shayarwa aƙalla duk sa'a 2. Shayarwa da maman daya kamu da cuta bashi da illa ga jariri kuma ita ce hanya mafi kyau wajan fitar da cutar.

Ga mace tana matsa nononta ta ƙasa alhali tana shayarwa.
Rinƙa dannawa a hankali domin tausasa wurin da yayi tauri
  • Ki tabbatar kin yi zaman bada nono daya dace. Wato gabaɗaya jikin jaririn yazama yana kallo mahaifiyar. Bakin jaririn kuma a buɗe yake sosai, kuma kan nonon ya shiga bakin jaririn sosai.
  • Ki shayar da jaririn da nonon dake cewon, har sai ya ƙarar dashi.
  • Dannawa da ƙyallen da aka jiƙa da ruwan ɗumi zai taimaka, ko kuma wanka da ruwan zafi. A ɗumama nonon tsahon minti 15 ko 20, aƙalla sau huɗu a rana. Ko kuma a saka ƙyalle mai sanyi ko ganyen kabeji akan nonon domin rage kumburin.


Idan da akwai zazzaɓi, a bada mg 250 na erythromycin sau 4 a rana.

Cutar Ƙanjamau dakuma shayar da nono

A halin yanzu akwai magungunan da suke sa masu ciki kuma masu cutar ƙanjamau su zamo cikin ƙoshin lafiya kuma su hana yaɗuwar cutar zuwaga jariran su. Domin kare mata dakuma ƙananan yara, kowacce mai ciki yakamata ayi mata gwajin cutar ƙanjamau. Idan kuma tana da cutar a samar mata da magani a lokacin da take ɗauke da cikin dakuma lokacin da take shayarwa, dakuma bayan nan idan tana da buƙata. Duba Cutar Kanjamau (HIV and AIDS) - ana kan aikinsa.

Shin babu hatsari shayarwa idan kina da Ƙanjamau?

Magungunan ƙanjamau suna hana yaɗuwar cutar a lokacin da ake shayarwa. Ko dai mahaifiya ko kuma jaririn dole ta/ya rika shan magani kullum har sai anyi yaye. Kuma lafiyar jaririn ana iya daɗa kareta ta bashi nono kaɗai a watanni 6 na farko (ko kuma har sai ya fara hakori). Kunu da sauran kayan sha baza su taimaki lafiyar jaririn ba.

Magungunan Kanjamau ga uwa dakuma jaririnta. Zasu taimaka musu su sami koshin lafiya. .


Idan babu magungunan Ƙanjamau, akwai hatsarin yaɗuwar cutar ta cikin nono. Amma hatsarin kamuwa da cuta saboda bada abincin gwangwani yafi illa. Dayawa daga iyaye (mata) masu ƙanjamau basu da, tsaftataccen ruwa, makamashi ko kuma kuɗin da zasu iya saye ko haɗa abincin jarirai. Akwai damar jariransu su zamo masu rashi lafiyar rashin isashshen abinci mai gina jiki wanda zai haifar da gudawa kuma zasu iya mutuwa. Duk wannan yana nufin shayar da mama shi yafi ko da uwa ko jaririn basa shan magungunan ƙanjamau.

Ga jarirai da iyaye (mata) a ko ina, shayar da mama shi yafi

Shayar da nonon (uwa)

NWTND Newb Page 23-1.png
  • Shi yafi rashin tsada. Baki da bukatar ki sayi wani sanadari, bilinboti ko wani abu.
  • Yana taimakawa wajan tsaida jinin haihuwa.
  • Yana taimakawa wajan hana ɗaukar ciki a 'yan watannin bayan haihuwa.
  • Yana kare uwa daga kamuwa da cewon jeji dakuma raunin kashi a karshin rayuwar ta.
  • Kullun a tsaftace yake ga dumi kuma ba wahalar ci.
  • Yana dauke da dukkan nau'in abinci da jariri sabuwar haihuwa yake buƙata..
  • Yana taimakawa jarirai wajan hana kamuwa da gudawa, pneumonia dakuma sauran cututtuka.
  • Yana bada doguwar kariya akan cutar suga, cututtukan yanayi dakuma cutar jeji a sauran rayuwar jaririn.
  • Jariri yana samun kariya dakuma ɗumi daga mahaifiyarsa
  • Yana ƙara danƙon soyayya tsakanin uwa da jaririnta.
NWTND Newb Page 23-2.png


This page was updated:05 Jan 2024