Hesperian Health Guides

Nan da sa'o'i kanan

In this chapter:

Bayan kamar sa'a ɗaya ko biyu da haihuwa, bayan jariri ya sha mama kuma kin tabbatar mahaifiyar bata zubarda jini kuma komai yayi dai-dai. To daganan sai ki bada duk wasu magunguna da ake bukata. Kuma ki duba jaririn a nitse daga kai- zuwa-dan yatsan ƙafa domin ki ga ko da wata matsalar da take da buƙatar kulawa. Kar ki bari jaririn ya kamu da sanyi a lokacin da kike duba shi.

Magungunan (jarirai) sabuwar haihuwa.

Idan uwa tana da ciwon (sanyi nau'in) gonnorhea ko chlamydia(cututtuka guda biyu na al'aura masu yaɗuwa). Wannan zai iya shafar jaririn a lokacin haihuwa, ya kuma haifar masa da matsalar ido mai tsanani dakuma makanta. Abu ne gama gari mace na ɗauke da cutar al'aura mai yaɗuwa amma bata saniba. Hanya mafi kyau dan ganin cewa gonorrhea ko chlamydia basu yaɗu zuwa idanuwan jaririn ba shi ne, A gwada mata dakuma maza kuma ayi musu maganin waɗannan cutuka masu yaɗuwa ta jima'i. Domin koyon alamomin waɗannan cututtu masu yaɗuwa dakuma hanyoyin warkarda su, duba (kashin dayake magana akan) Matsalolin Al'aura dakuma Cututtuka (ana kan aikinsa). Domin kare ido daga kamuwa da gonorrhea ko chlamydia a saka erythromycin ko tetracycline ointment a kowanne ido na jaririn a sa'a ta farko ko ta biyu da haihuwarsa.

A wuraren da cutar jejin hanta wato ‘hepatitis B’ ta zama gama-gari. To yana da kyau ayiwa jariri rigakafin cutar a rana ta farko bayan haihuwarsa. Wannan zai hana yaɗuwar cutar daga uwa zuwaga jariri. Kuma abu ne gama-gari uwa na dauke da cutar hepatitis B (jejen hanta) amma bata saniba.

Duba jaririn

NWTND Newb Page 6-1.png
  • Shin jaririn yayi kama da sauran jarirai?
  • Shin ɓangaroron jikinsa na dama dana hagu girmansu da siffarsu da wurinsu ɗaya?
  • Shin fatarsa a haɗe take?A duba, musamman ma ƙasan baya. Wani lokacin akan sami 'yar ƙaramar ƙofa anan wadda take bukatar tiyata ba tare da bata lokaci ba.
  • Shin yayi fitsari? Wani lokacin jariri baya yin fitsari ranar farko. Amma yakamata yayi fitsari sau dayawa a rana ta biyu, sannan duk bayan 'yan sa'o'i bayan nan. Idan baya isashshen fitsari, ko kuma fitsarin yana da launi mai duhu da ware mai ƙarfi, to yana buƙatar ƙarin shan nono sosai. Ko kuma wataƙila yana da matsalar ƙoda.


Waɗansu banbance-banbancen ba masu muhimmanci bane, wadansu kuma zasu iya zama alamar babbar matsala. Idan jariri yana da wani banbanci, to alura wataƙila akwai waɗansu kuma wani lokacin acikin jiki suke. A lura da irin waɗannan jariran sosai aga ko suna numfashi ko kuma launinsu ko fitsarin su dai-dai yake.

Surar Kai

Kan jariri a kumbure.

Babu wata matsala idan kan jariri yayi tsini ko kuma a sami wani babban kumburi kamar haka (yadda yake a hoton ƙasa). Musamman ma idan anyi doguwar naƙuda. A 'yan kwanaki kaɗan kumburin zai baje.

NWTND Newb Page 7-3.png
hematoma
(kwantaccen jinin kai)

Wadansu jariran suna da kwantaccen jini a ƙarƙashin fatar kansu wanda ake kira da hematoma. Yana da laushi idan an dannan. Waɗannan basu da hatsari, amma zasu iya ɗaukar wata ko kuma sama da wata basu baje ba.

Tsagaggen leɓe da Tsagaggiyar ganda

a baby with a cleft lip.

Tsaga a leɓe bata da wahalar gani. Amma tsaga a rufin saman baki (wato ganɗa) ba a sarari take ba. Saka tsumma mai tsafta acikin bakin jaririn domin ki ji, ko saman a rufe yake. Hatsarin dayake ga jariri mai tsagaggen leɓe ko ganɗa shine wahala wajan shan mama

Domin yasha mama sai ayi ƙoƙarin rufe tsagar dake leɓen da yatsa, domin bakin ya rufe nonon. Ga mai tsagaggiyar ganɗa kuma, a saka kan nonon can cikin bakin jaririn daga ɗaya ɓarin na tsagar. Idan har yanzu jaririn yana samun matsala, to sai a bashi nonon da cokali mai tsafta ko kuma abin ɗiga (magani) har sai ya girma ya fara iya shan maman da kansa. A rinƙa yawan bashi mama domin ya zamo mai lafiya. Domin koyon yadda ake tatsar nono da hannu domin shayarwa danna nan.

Ana iya gyara tsagaggen leɓe ta hanyar tiyata, bayan wata 3 uku da haihuwa. Ana iya kuma gyara tsagaggiyar ganɗa ta hanyar tiyata bayan shekara. A kasashe dayawa ana yin irin waɗannan tiyatocin kyauta, kuma zai taimaka kwarai ga rayuwar yaron. Ayi tambaya a asibiti domin samun bayani.

Wannan hoton yana nuna yadda ake duba gurɗaɗɗan ƙugu.

Gurɗaɗɗan ƙugu, gocaccan kwankwaso, 'dysplasia'

Wadansu yaran ana haihuwarsu da gurɗaɗɗan ƙugu, wato ƙafafun sun fita daga mahaɗarsu ta jikin kashin cinya. So dayawa irin wannan yana gyaruwa dakansa bayan 'yan kwanaki ko satuttuka.

A lanƙwasa kafafun, ta yadda zaki iya riƙe cinyoyin guda biyu dakuma ƙasan ƙafar tare. Kwantar da saman 'yan yatsunki akan kwankwason jaririn. Daga nan sai ki juya ƙafa ɗaya a hankali kina kiwayawa ciki da waje, ƙasa kuma a juya baya. Idan ɗaya daga cikin kafafun ta fara tsayawa, sai ki jata. Idan kika buɗe ta sosai to wataƙila (wannan ƙafar) a goce take.

Mace tana goye da jariri ƙafafunsa a ware.
Ki sa mahaifiyar (jaririn) ta goya jaririn ƙafafunsa a ware, kamar yadda aka nuna.

Ki duba jaririn bayan sati biyu. Idan har yanzu kina jin ƙara ko cijewa (a kafar), to a nemi taimakon (likita). Irin wannnan goyon da zai buɗe ƙafafun jaririn na 'yan satittika zai iya taimakawa wajan hana nakasa rayuwa.


Jariri ƙafarsa ta juya ciki.
Jariri da filasta a ƙafarsa.

Murɗaɗɗiyar ƙafa

Idan ƙafar jariri sabuwar haihuwa ta juya ciki, ko kuma tana da sura marar kyau, to ayi ƙoƙarin juya ta zuwa inda ya dace. Idan har za'a iya yin hakan batare da wata wahala ba. A kuma mai- maita sau dayawa a rana. To a hankali ƙafar (ko ƙafafun) zasu kuma dai-dai. Idan kuma baza'a iya juya ƙafar zuwa dai-dai ba to akaishi zuwa cibiyar lafiya, bayan haihuwarsa da 'yan kwanaki kaɗan. ƙafarsa tana buƙatar a miƙe ta da filasta. Idan anyi hakan da wuri, filasta tana kare yin tiyata ko kuma samun nakasa daga baya.

Cindon hannu ko na ƙafa

Hoton dake ƙasa: Ƙarin ɗanƙaramin yatsa (Cindo) kewayi da zare.

Cindon hannu ko na ƙafa, marar ƙashi a cikinsa, za'a iya cire shi ta hanyar ɗaure shi da zare da ƙarfi. Zai bushe kuma ya cire. Idan ɗan yatsan hannun ko na ƙafar babba ne ko yana da ƙashi, to ba zai cutar ba, sabodahaka sai a barshi.

Yar ƙaramar haɗewa tsakanin 'yan yatsun ƙafa kamar wannan ba matsala bace.
NWTND Newb Page 8-5.png

Idan 'yan yatsu guda biyu ko sama da biyu (na jariri) suka zo a maƙale, to ana buƙatar tiyata domin suyi aiki dai-dai.

Down syndrome (Cutar Dolantaka)

Nakasar da ta shafi tunani ko koyo za'a iya ganeta tun farkon haihuwa, ko kuma a kasa ganeta har sai yaron yayi wayo. Cutar dolanta gamagarin dalili ne na raunin hankali. Jariran dake da cutar dolantaka suna da waɗansu ko kuma dukkan waɗannan alamomin:

NWTND Newb Page 9-1.png
Idanuwa sun juya daga sama
Taɓaɓɓiyar fiska
Layi daya ne ya ratsa tafin hannun
Ƙaramin kunne da tattararriyar fata a sama.
Sakakkiyar tsokar hannu
NWTND Newb Page 9-2.png
Gurbi me faɗi tsakanin 'yan yatsun Ƙafa na farko dana biyu.
Yaro (gurgu) riƙe da sanduna kuma dauke da yarinya a kafadarsa;yarinyar tana riƙe da alama.
A binkici baiwoyin kowanne yaro.

Cutar dolanta ba wani abu da uwa ko kuma wani ya aikata ne yake kawota ba. Idan mace ta wuce shekara 35 kuma ta sami ciki, to ɗan da zata haifa akwai dama mai yawa ta samishi. Irin waɗannan jariran suna buƙatar kulawa kamar sauran yara, kuma yan wasu sauƙaƙan ayyuka zasu taimaka masa wajan koyo.

Kulawa da yara masu nakasa

Dayawa daga cikin banbance-banbance na zahiri dake haifar da matsaloli ga yara za'a iya maganinsu a gida da taimakon ma'aikatan lafiya. Kuma abin da yafi kowanne irin magani a wurin yara masu nakasa shi ne soyayya, kulawa, yin wasa, yin karatu dakuma basu matsayi kamar sauran yara. A lura da baiwa dakuma ƙwarewar da kowanne yaro ya bijiro da ita.

Mafi kyawun hanyar kula da jarirai itace kula da mahaifansu (mata).


Nakasosin haihuwar da sukafi illa

Wadansu nakasosin haihuwar suna da matukar illar da zasu haifar da mutuwar jariri. Wannan wani lokaci ne na baƙinciki ga 'yan uwa dakuma al'umma. A matsayinki na ma'aikaciyar lafiya, zaki iya taimakon dangin sa wajan tattaunawa akan abinda ya same su na baƙin ciki saboda rashi.

NWTND Newb Page 10-1.png

Tsaftacewa dakuma sakawa jariri kaya

NWTND Newb Page 11-1.png
Dayawa daga cikin iyaye (mata) suna so su kare jariransu daga iska marar kyau tahanyar sa musu kayayyaki masu yawa dakuma zannuwa. Wannan zai iya sa jariri yaji zafi sosai!Ƙarin ninki ɗaya ya isa.

Goge duk wani jini dakuma kashin farko na jaririn (wani bakin abu wanda ake kira meconium), amma kada ayi wanka.Bayan kwana biyu ko uku sai aringa yiwa jaririn wanka akai-akai, domin gusarda nono, yawu, datti dakuma kashi.

Idan zaki sawa jaririn kaya, yi amfani da kayan sawa kamar na babba, sannan a ƙara masa guda ɗaya akai. A satin farko zuwa na biyu a rufe kan jaririn. (Jarirai) Suna rasa ɗumi ta ka. A riƙa cire kaya dakuma kunzugu suna jiƙewa ! Ko suka ɓaci da kashi. Idan fatar (jaririn ) tayi ja, ko kuma ɗuwawunsa yayi ƙuraje, to a daina sa kayan ko kunzugun domin ya warke.


This page was updated:05 Jan 2024