Hesperian Health Guides

Ciwuka dakuma raunukan ciki

A wanna kashin:

Idan ciki ya bugu, kamar saboda faɗuwa mai ƙarfi, hatsarin abin hawa, ko duka ko kuma zunguri, to a duba inda jini ya taru a cikin jiki. Yawan taruwar jini acikin jiki zai iya haifar da girgiza. Kuma a lura da waɗannan alamomin na matsanancin rauni a ciki:

Alamomi masu hatsari
  • Matsanancin ciwo.
  • Ruɗewa.
  • Taurin ciki kamar katako, ko kuma yana ƙara girma.
  • Alamomin rashin jini wato: suma, ɗashewa, saurin bugun zuciya.


Ga kowanne daga cikin waɗannan alamomin, ayi maganin girgiza kuma a nemi taimako. Kada a bada abinci ko abinsha. Duba Ciwon ciki, gudawa, dakuma tsutsotsi (ana kan aikin) domin ƙarin bayani kan Cututtukan ciki masu buƙatar gaggawa.

ga rauni dawani ɓangare na hanji ya fito ta cikinsa.
Idan wani ɓangare na hanji ya fito waje, to a rufe shi da ƙyalle mai tsafta wanda aka tsoma shi a cikin ruwan gishiri sannan a nemi taimako. Kada a tura hanjin ciki.

Wani abu daya cake a cikin jiki

Ga wani abu daya cake a cikin ciki, yafi kyau a barshi a nemi taimako. Koda kuwa taimakon za’a same shi nan da kwanaki, kada a cire abin. A daure shi a jiki da bandaji ko kyalle.

a man bleeding from a wound caused by a stick in his abdomen.


This page was updated:05 Jan 2024