Hesperian Health Guides

Kamuwa da cuta

A wanna kashin:

Kowanne irin rauni zai iya kamuwa da cuta

Alamomin kamuwa da cuta

Rauni ya kamu da cuta idan:

  • Ya kumbura, yayi ja kuma yake zafi.
  • Idan yana fitar da ruwa/ɗiwa.
  • Idan ya fara wari.


Cutar tana yaɗuwa zuwa sauran sassan jiki idan:

  • ya haifar da zazzaɓi
  • kaluluwa ta kumbura kuma tayi laushi


Kaluluwa — wata yar matattara ce ta ƙwayoyin cuta wadda ke yin dan ƙunshi ƙarami a ƙarƙashin fata idan an sami kamuwa da cuta. Kaluluwar data kumbura tana nuna alamar kamuwa da cuta.
jikin mutum, ana nuna wurare guda 5 da kaluluwa take fitowa.
Kaluluwar ƙasa da haɓa tana nufin cutar haƙori ko maƙogwaro.
Kaluluwar bayan kunne tana nufin cuta a kai ko fatar kai, wanda sau dayawa kurjewa ko ƙwarƙwata take haifarwa. Ko kuma ƙyandar Jamus (rubella) ta jawa.
Kaluluwar ƙasan kunne dakuma ta kan wuya tana nufin cutar kunne, fiska ko kai. Ko kuma zata iya zama alamar cutar TB.
Kaluluwa a hammata tana nufin cutar hannu, kai ko nono. Ko kuma wani lokacin tana nuni da Sankaran mama. (duba Cutar daji-ana kan aikinta).
Kaluluwa a
jikin al’aura
tana nufin
cutar sangalalin kafa, tafin kafa, al’aura ko dubura (takashi).
Maganin kamuwa da cuta

A tsaftace raunin sosai. Wataƙila kana da buƙatar ka bude raunin domin ɗiwa ta fito ko kuma ka cire ɗinki. Domin ƙarin bayani akan rauni mai ɗiwa duba Matsalolin Fata (ana kan aikin). In dai ba wurin da ya kamu da cutar ƙarami ba ne kuma ana samun sauƙi cikin hanzari, to yafi kyau a bada antibiotics. A bada dicloxacillin, cephalexin, KO clindamycin. Idan raunin yana da zirfi, a bada rigakafin tetanus (duba Rigakafi – ana kan aikin) da kuma tetanus immunoglobulin.

Idan cutar bata yi sauƙi ba, za ta iya yaɗuwa ta cikin jini. Wannan shi ake kira da sepsis.



This page was updated:05 Jan 2024