Hesperian Health Guides

A rika yawan binkicen jaririn a watanni 2 na farko

NWTND Newb Page 11-2.png


Ungozoma ko kuma wata ma'aikaciyar lafiya ta cigaba da kula da mahaifiya dakuma jaririn bayan haihuwa. Masu jego da jariransu zasu iya zuwa a dubasu a asibiti, amma idan da hali a duba su a gida, domin kada suye tafiyar da zata saka jariransu su haɗu da marasa lafiya a asibiti. A duba jariri dakuma mejego washegarin haihuwa, bayan kwana 3 da haihuwa, dakuma bayan sati 1 da haihuwa. Kuma wani duban bayan sati 6 zai taimaka. A riƙa yawan zuwa duba (asibiti) musamman ma idan da alamun matsaloli. Yawan zuwa (asibiti) ita ce mafi kyawun hanyar gano matsalolin lafiya kafin su zamo hatsari.