Hesperian Health Guides

Jarirai sabuwar haihuwa dakuma shayar da mama: Magunguna

likita||notforsale=true|booktitle=Sabon littafin A inda babu likita }}

Jarirai Sabuwar Haihuwa dakuma Shayar da Mama

Antibiotics suna yakar cuta

Ampicillin da amoxillin


Ampicillin da amoxillin antibiotics ne masu faɗin aiki, wannan yana nufin suna iya kashe ƙwoyoyin cutar bacteria masu yawa sama da sauran magungunan da suke cikin dangin penicillin. Su biyun ana iya musayarsu. Idan kika ga ance ayi amfani da ampicillin a wannan littafin, to sauda dama za'a iya amfani da amoxillin a maimakonsa ta amfani da ka'idar da aka bayar (duba ƙasa).

Ampicillin da amoxicillin suna da matuƙar rashin katsari kuma suna da amfani na musamman ga jarirai da ƙananan yara. Dukkanninsu ana amfani dasu wajan warkar da cutar sanyi ta pneumonia ko cututtukan kunne. Ampicillin kuma ana iya amfani dashi wajan warkar da cutar sanƙarau meningitis da sauran mugwayen cututtukan jarirai sabuwar haihuwa.

Green-effects.png Illolin (sa)
Dukkanin waɗannan magungunan musammam ma ampicillin suna iya sa a riƙa jin amai da gudawa. Kada a bawa yara da suke gudawa, za a iya basu wasu antibiotics ɗin maimakon su.

Wata kuma illar itace ƙuraje. Ƙuraje masu tashi da ƙaiƙayi waɗanda kan iya fitowa su koma bayan 'yan sa'o'i kaɗan na iya zamowa dalilin yin amfani da penicillin ne. A dakata da bada maganin nan take. Kuma kada a sake bawa yaron penicillin. Domin nan gaba illar zata iya fin tabaya ko kuma ma ta zamo mai barazana ga rayuwa. Idan an sami matsala za'a iya amfani da erythromycin maimakon sa.

NBgrnimportant.png A lura
Rashin tasirin waɗannan magungunan yana daɗa yaɗuwa. Ya dogara da inda kiki zaune, ba dole bane su iya kashe staphylococcus, gonorrhea, shigella, ko sauran cututtuka.

NBgrninjectpill.png Yadda ake amfani (da shi)
Ampicillin da amoxicillin sunfi aiki idan aka bada su ta baki. Domin bada ƙwayar maganin ko kafson ga jariri, sai a niƙa ƙwayar maganin ko a zazzage kafson kuma a raba hodar (maganin) domin samun addadin maganin da ake buƙata. Sannan a cuɗanya ta da nono ɗan kaɗan. A bawa jaririn nonon mai ɗauke da maganin da cokali ko kofi. Kuma ana iya yin allurar ampicillin, amma ana alluranne kaɗai ga matsananciyar rashin lafiya kamar sanƙarau, ko kuma idan yaro yana amai ya kasa riƙe komai a cikinsa. Amma antibiotics kuma akwai iyakar tsahon lokacin da za'a iya bada su. A cigaba da bada maganin har sai dukkan alamomin cutar (har da zazzabe) sun tafi da akalla sa'o'i 24. Idan jaririn yana da ƙanjamau a bada maganin iya cikakkon kwanakin da aka nuna (a kasa). Haka kuma akwai iyakar yawan da za'a bayar. A taƙaice, sai a bada kaɗan na iyakar da aka ƙayyade ga siririn yaro ko kuma wanda cutar bata yi tsamari ba, kuma a bada dayawa na iyakar da aka ƙayyade ga yaro mai ƙifa ko kuma wanda cutarsa tayi tsamari.

AMOXICILLIN
Ga yawancin cututtukan jarirai sabuwar haihuwa:
Sai a bada mg 62 , sau 3 a rana har tsahon kwana 3 zuwa 7. Kowacce bayarwa tana ɗauke da
¼ na 250 mg na kafso KO
½ na ƙaramin cokalin shayi (2.5 ml) na mg 125 /ml 5 na maganin ruwa KO
¼ na ƙaramin cokalin shayi (1.25 ml) ) na mg 250 /ml 5 na maganin ruwa.

Ayi ta bayarwa har sai bayan sa'o'i 24 da tafiyar dukkan nin alamomin cutar.

AMPICILLIN
Domin cututtuka masu yaɗuwa na jarirai sabuwar haihuwa
A bada mg 125 , sau 3 a rana har tsahon kwanaki 3 zuwa 7. Kowacce bayarwa tana ɗauke da:
½ na kafso mai nauyin mg 250 KO
Ƙaramin cokali (ml 5) na maganin ruwa mai nauyin mg 125 /ml 5.

Ayi ta bayarwa har sai bayan sa'o'i 24 da tafiyar dukkan nin alamomin cutar.

Ga cututtuka matsananta na jarirai sabuwar haihuwa, irin su cewon sanyi (pneumonia) ko sankarau (meningitis)
Ayi allurar haɗin ampicillin da gentamicin a jikin cinya ɗaya. Duba Magunguna, Gwaje-gwaje da Hanyoyin Waraka (ana kan aikinsa) domin sanin yadda ake allura. Duba bayanin da akayi a sama akan ampicillin, domin ganin gargaɗin da akayi akan gentamicin.

Ga jariran da suke ƙasa da sati 1
AMPICILLIN: Ayi allurar mg 50 ga dukkan nauyin kg 1(na jariri), sau 2 a rana har tsahon kwana 5 a taƙaice,
KUMA
GENTAMICIN: Ayi allurar mg 5 ga dukkan nauyin kg 1(na jariri), sau ɗaya a rana har tsahon kwana 5 a taƙaice.
Ga jaririn da yake sati 1 zuwa watanni 2
AMPICILLIN: Ayi allurar mg 50 ga dukkan nauyin kg 1 (na jariri), sau 3 a rana har tsahon kwana 5 a taƙaice.
KUMA
GENTAMICIN: Ayi allurar mg 7.5 ga dukkan nauyin kg 1(na jariri), sau ɗaya a rana har tsahon kwana 5 a taƙaice.

Erythromycin


Erythromycin yana kashe irin cututtukan da penicillin yake kashewa amma, ya ɗan fishi tsada. A ɓangarori da dama na duniyar nan, yanzu erythromycin yafi aiki sama da penicillin ga waɗansu nau'uka na ciwon sanyin pneumonia. Ana kuma iya amfani dashi akan (matsanantan cututtukan sanyi) diphtheria da pertussis.

Ga mutanen da penicillins take musu illa, erythromycin kyakkyawan magani ne, dakuma sauran cututtuka dayawa. Kuma ana iya amfani dashi a maimakon tetracycline (ja-da-yalo).

Green-effects.png Illolin (sa)
Erythromycin yakansa yawan jin amai dakuma gudawa, musamman ga yara. Kada ayi amfani dashi sama da sati 2 zai iya haifar da cewon shawara.

NBgrnspoon.png Yadda ake amfani (da shi)

Ga jarirai sabuwar haihuwa har zuwa shekaru 3
A bada mg 30 zuwa 50 ga dukkan kg 1(na yauyin jariri) a kowacce rana, a raba shi zuwa kashi uku a rana. A bayar har zuwa kwanaki 10 zuwa 14.
Ga jariri sabuwar haihuwa mai matsakaicin nauyi kamar kg 3, kowacce bayarwa tazamo:
0.75 ml (wanan ya ɗan fi ⅛ na cokalin shan shayi) na mg 250 /ml 5 na erythromycin na ruwa,KO
&188; na ƙwayar mg 250 wadda aka niƙa acikin ɗan nono kaɗan ko ruwa.
Domin cewon nono ga mai shayarwa
A bada mg 250 zuwa 500 (kwaya 1 ko 2 na mg 250 ), sau 4 a rana har tsahon kwanaki 10.

Gentamicin


Gentimicin antibiotic ne mai ƙarfi wanda ke cikin dangin aminoglycoside. Ana iya bada shi ne ta hanyar allura kadai ko ta jijiya. Wannan maganin zai iya lalata koda dakuma jin sauti, sabodahaka za'a iya amfani dashi ne kaɗai idan ana gaggawa.

Domin cewon sanyin pneumonia ko sanƙarau na jarirai da sauran yara a bada haɗin gentimicin da ampicillin.

NBgrnimportant.png A lura
Dole ne a bada gentamicin iya yadda aka ƙayyade. Badashi dayawa zai iya kawo lalacewar koda ko kuma kurumta ta dun-dun-dun. A bada iya yawan da ake bukata gwargwadon nauyin yaro, kada a bada maganin ta dogaro da shekarun yaro. Kuma kada a bada gentamicin sama da kwanaki 10. A guji bada tsimamman maganin (wato awan dayakai mg 10 /ml yafi rashin illa akan mg 40 /ml).

Ceftriaxone


Ceftriaxone Ceftriaxone antibiotic ne mai ƙarfi da za'a iya amfani dashi wajan (magance cutukan) sepsis da sankarau, amma zaɓi na biyu ne ga waɗannan cututtukan saboda yana da haɗari ga (jarirai) sabuwar haihuwa. Ceftriaxone yana da amfani na musamman ga cutar sanyin gonorrhea, wanda ya haɗa da cutar gonorrhea dake kama idanuwan (jarirai) sabuwar haihuwa.

Green-effects.png Illolin (sa)
Ceftriaxone yana da zafi wajan allura. Bubu laifi idan an haɗa shi da 1% na lidocaine idan an iya haɗawar.

NBgrnimportant.png A lura
Kada a bawa jaririn da yake ƙasa da sati 1 ceftriaxone. Kuma a guji yin amfani dashi ga bakwainin jarirai ko ƙanana (jarirai). Kada a bayar idan da akwai (cutar) shawara.

NBgrninject.png Yadda ake amfani (da shi)

Ana samun allurar ceftriaxone ne kaɗai ko kuma allurar jijiya.
Domin (ciwon sanyin) gonorrhea ga (jarirai) sabuwar haihuwa 'yan kwana 7 ko sama da haka.
Yi allurar mg 50 ga duk kg 1(na nauyi) sau ɗaya. Kuma:<brGa (jariri) sabuwar haihuwa mai matsaƙaicin nauyi kamar kg 3, ayi allurar mg 150.
Ga matsanancin yanayi na jariri ko kuma yaro ɗan sama da kwanaki 7 idan babu sauran antibiotic
Yi allurar mg 75 ga (duk nayin) kg 1, sau ɗaya a rana har kwanaki 7 zuwa 10. Kuma:
Ga (jariri) sabo mai nauyin kg 3, yi allurar mg 225 sau ɗaya a rana.
Ga jaririn daya kwana biyu mai nauyin kg 6,yi allurar mg 450 sau ɗaya a rana.


This page was updated:05 Jan 2024