Hesperian Health Guides
Matsalolin lafiya na jarirai sabuwar haihuwa
Kundin bayanan lafiya na Healthwiki > Sabon littafin A inda babu likita > Jarirai sabuwar haihuwa dakuma shayar da mama > Matsalolin lafiya na jarirai sabuwar haihuwa
Cututtukan da zasu iya ɗaukar satuttuka su kashe manya Zasu iya kashe jariri a sa'o'i kaɗan. |
Kanun bayannai
Cuta me yaɗuwa
Cuta me yaɗuwa a wurin jariri sabuwar haihuwa aba ce mai matuƙar hatsari kuma tana buƙatar warkarwa da (maganin) antibiotics nan take. Dogaro da nisanku da cibiyar lafiya dakuma irin magungunan da kuke da su, ko dai ku nemi taimako nan take ko kuma kuyi magani da kanku-ko da a hanyar zuwa neman taimakon ne.
Alamomi masu hatsari
- Numfashi da sauri da sauri: sama da sau 60 a minti daya a lokacin bacci ko hutu.
- Ƙoƙarin shaƙar iska: ƙirji ya luɓa ciki, gurnani, hanci yana kusir-kusir domin ƙoƙarin (shaƙar iska), a lokacin bacci ko hutu.
- Zazzaɓi, zafin jiki ya wuce 37.5 0 C ko kuma yayi ƙasa da 35.5 0 C
- Matsanantan ƙuraje da ƙuraje masu ruwa. (ƙananan ƙuraje ba matsala ba ne)
- Ƙin cin abinci.
- Farkawa da ƙyar, ko kuma yayi kamar baya jin ki.
- Shiɗewa: fita daga hayyaci dakuma shure-shure.
Duk ɗaya daga cikin waɗannan alamomin na nufin jaririn yanada cuta me yaɗuwa. Idan jaririn yana da samada alama ɗaya, to yana cikin babban hatsari kuma yana buƙatar (maganin) antibiotics nan take. Idan kuma yana da alama guda ɗaya kuma amma baya samun sauƙi to yana buƙatar magani. Idan mahaifiyar tayi zazzaɓi lokacin naƙuda, to a lura sosai da alamomi masu hatsari a wurin jaririn. Haka kuma jaririn da yayi kashi acikin mahaifa, wani lokacin yakan shaƙi wannan kashin a lokacin haihuwa. (kuma ruwan mahaifar zai kasance yana ɗauke da gutsatstsarin kashi ruwan ƙasa ko kure-kure. Ko kuma fatar jaririn ta ɗanyi rawaya a lokacin haihuwa). Wannan zai iya haifarda cuta a huhu a 'yan kwanakin farko. Sabodahaka, a zauna cikin shiri domin magance waɗannan jariran cikin gaggawa ana ganin alama ta farko ta kamuwa da cuta.
Magani
Yi allurar ampicillin da gentimicin nan take. Acigaba da yi har kwana 5. Haƙiƙanin yawan maganin ya dogara ne da nauyin jaririn.
Jaririn zai fara samun sauƙi cikin kwana 2. Idan ba’a samun cigaba, to ana buƙatar yin amfani da wani nau’in na 'antibiotics' domin cetun rayuwarsa. A nemi taimakon (ma’aikatan) lafiya.
Yin kuka
Waɗansu jariran sukanyi kuka sama da wasu. Jaririn dake kuka wataƙila lafiyarsa ƙalau. Idan sauran alamomin lafiyarsa basu da matsala. A duba ko yana numfashe dai-dai alokacin da baya kuka.
Yawan kuka, wanda ke daɗa karuwa sau dayawa da daddare, shi ake kira da colic. Yakamata ya dai-daita bayan watanni 3. Wannan yafi takurawa iyaye akan shi jaririn. Aji ƙan sababbin iyaya (mata). A tabbatar sun sami isashshan hutun da suke bukata.
Amai
Jarirai sukan yi tunbiɗin nono. Wani lokacin dayawa har yakan fito ta baki ko hanci. Tunbiɗin nono ba matsala bace matuƙar jaririn yana yawan shan nono, kuma yana ƙara nauyi. Yi ƙoƙarin riƙe shi a tsaye bayan yasha. Wannan zai hana nonon ya fito.
Alamomin masu hatsari
- Amai ba ƙaƙƙautawa, ko kuma ya kasa riƙe komai acikinsa.
- Aman jini.
- Alamun rashin ruwa a jiki.
Rashin isashshen ruwa a jiki
Jarirai nan-da-nan suke rasa ruwa a jikinsu, kuma a wurin jarirai rashin ruwa babban hatsari ne.
Abubuwan da suke kawowa
|
Alamomi
|
Kowanne irin jariri zai iya samun rashin ruwa a jiki.
Matsanancin rashin ruwa zai iya kawo faɗawar idanuwa, faɗawar maɗigar ka, raguwar nauyi da kuma rashin ankara (da abinda ki faruwa).
Magani
Ana ganin alamar farko ta rashin-ruwa-a-jiki, ko kuma idan jariri yayi gudawa ko kuma yanata amai, to aita bashi nono iya yadda zai iya sha. A tashi jariri yasha duk bayan sa'a 2. Za'a iya kuma bashi ruwan-gishiri-da-suga (rehydration drink) - ana kan aikinsa, ɗan haɗin ruwa ne da ɗan gishiri kaɗan dakuma suga. A bada ruwan-gishiri-da-suga bayan yasha nono. Yanada wahala ace uwa tana ci tana koshi amma bata samar da isashshen nono.
Idan jariri marar isashshen ruwa bai sami cigaba ba bayan 'yan sa'o'i, to a nemi taimakon likita domin samar da ruwa a jikin jaririn.
Kuraje
Sababbin haihuwa suna yin ƙuraje, ruɗi-ruɗi dakuma banbancin launin fata wanda sau dayawa basa cutarwa kuma suna washewa da kansu. Ƙuraje a ɗuwawun jariri suna faruwa ne saboda kasancewar su cikin danshin fitsari da kashi. A riƙa goge wurin akai-akai. A riƙa canja ƙunzugu da jiƙaƙƙon kaya suna jeƙewa ko ɓaci da kasa. Ga jariran da sukayi wayo, kuma a ranakun da ake zafi za'a iya barin ɗuwawun ya warke. Man Zinc oxide 'yana taimakawa. Idan bai warke ba acikin 'yan kwanaki to zai iya kasancewa cutar yeast ce. Sai ayi amfani da man nystatin.
Idan jariri yana da koraje masu ruwa ko masu tauri masu yawa, musamman ma idan ana ganin kamar bashi da lafiya ko kuma yana da zazzaɓi, to akwai damar yana ɗauke da cuta mai yaɗuwa. Idan baya samun cigaba acikin hanzari, ko kuma alamun cutar ya cigaba da ƙaruwa, to abada antibiotics din da aka jera a nan.
Shawara
Rawayar fata ko idanuwa shi ake kira da shawara. Ga jarirai masu duhun fata, a duba idanuwan. Shawara a tsakanin rana ta biyu zuwa ta biyar bayan haihuwa ba ta da hatsari. Mafi tasirin magani shi ne shayar da mama akai-akai.
Alamomi masu hatsari
- Shawara tana farawa nan take-cikin sa'a 24 na farkon rayuwa.
- (Kuma) tana iya farawa daga baya, amma ta rufe dukkanin jiki.
- Jariri mai shawara kullun cikin bacci yake, ko kuma yana da wahalar farkarwa domin yace abinci.
A nemi taimako domin kowanne daga waɗannan alamumin.
Idanuwa
'Yan ƙananan ramukan da suke barin hawaye da mai su tausasa idanu suna iya toshewa daga nan sai su sa idanuwan su yi kwantsa. To sai a goge su da ƙyalle mai tsafta wanda aka jeƙa shi da ruwa mai ɗumi. A yi amfani da ƙyalle daban akowanne ido. Tahaka idan ido ɗaya yana ɗauke da cuta bazata yaɗu zuwa ɗayan ba.
kumburarriyar fatar ido ja mai ɗauke da ruwa mai jinni-jini, bayan jariri yayi kwana biyar zai iya kasancewa cutar chlamydia ko gonorrhea ta kama idan. A bawa jaririn erythromycin ta baka bayan an niƙa shi an kuma haɗa shi acikin nono. Kuma da mahaifiya da mahaifin jaririn ayi musu maganin cutar chlamydia da gonorrhea. Duba Genetal Problems and Infections (Matsaloli dakuma Cututtukan Farji - ana kan aikinsa). Idan matsalar idon bata sami waraka ba a kwana daya ko biyu, to kana da buƙatar wani antibiotic ɗin domin kariya daga makanta. Sabodahaka, a nemi taimako.
Miɗiga
Maɗigar dake tsororuwar kai yakamata ta zama dai-dai. Kumburi ko faɗawar maɗiga duka alamace dake nuna babbar matsala mai hatsari matuka.
Faɗawar miɗiga alamace ta rashin ruwa. Sabodahaka, a ƙara bada mama sosai dakuma ruwan gishiri da suga. | Kumburarriyar maɗiga alamace ta Sanƙarau. Sabodahaka a bada antibiotics. |
Cibiya
Bayan an yanke cibiya, sai abar saura. Kada a (rika) rufeta. Kada a rufe ta da kaya ko kunzugu. Kada a rika taba ta, kuma idan ya zama dole a taba to a wanke hannaye da sabulu da ruwa (kafin a taba). Idan cibiyar ko cikin yayi datti, ko kuma busashshen jinni ya makalkale a jiki, sai a wanke da sabulu a kuma goge da kyalle mai tsafta.
Idan mahaifiya zata rufe cibiyar da majanye ko kyalle to a tabbatar mai tsafta ne kuma kada a daure da kyau, kuma a rika canjawa duk bayan lokaci-lokaci a kowacce rana.
Cibiyar zata bushe ta faɗi a cikin sati.
Idan kewayen cibiyar yayi ja ko zafi ko yana wari ko yana fitar da ruwa, to wataƙila ta kamu da cuta. Sai a wanke sosai kuma a bawa jaririn amoxicillin. Idan jaririn yana da matsala a fuska, baya iya shan nono ko kuma ya sandare, musamman ma idan kamar akwai cuta a kewayen cibiyar, to watakila ya kamu da tetanus. To wannan harkace ta gaggawa. Duba Taimakon Farko (ana kan aikinsa).