Hesperian Health Guides
Maganin (cutukan) ido da antibiotic
Kundin bayanan lafiya na Healthwiki > Sabon littafin A inda babu likita > Jarirai sabuwar haihuwa dakuma shayar da mama > Maganin (cutukan) ido da antibiotic
Yadda ake amfani (da shi)
1% na tetracycline KO 0.5% zuwa 1% na erythromycin na shafawa ana amfani dasu wajan kariya daga kamuwa da cuta bayan anyi haihuwa, kuma ana (amfani dasu) ga matsakaiciyar cutar ido wadda bacteria ke haifarwa. To abada wannan sau ɗaya, acikin sa'a 2 bayan haihuwar.
Ɗigo1 na 1% na ruwan silver nitrate a kowanne ido. Silver nitrate yana daɗa tsumuwa idan ya ɗauki dogon lokaci, harma ya bi iska gaba daya-sabodahaka. Kada ayi amfani da silver nitrate ɗin daya daɗe. Zai kona idanuwan jaririn. Idan ana kokwanto, to kada ayi amfani da silver nitrate kwata-kwata.
Domin yin amfani da man (kwantsar), a hankali gwale fatar kowanne idan sannan a matsa ɗan man kaɗan cikin (idon) daga wajen ƙarshen fatar idon. Domin amfani da na ɗigawa kuma, a jawo fatar idon ta ƙasa a matsa ɗigo biyu cikin ta. Kada a bari jikin mazibin maganin ya taɓa idan.