Hesperian Health Guides

Cutar yis ta baki

Shanshan bale, GV, crystal violet, methylrosanilinium chloride


Shanshanbale magani ne marar tsada na cutar yis ta baki, ko kan nonon mai shayarwa, ko matuci. Kuma yana aiki wajan warkar da wasu cututtukan bacteria na fata.

Green-effects.png Illolin (sa)
Shanshanbale kan iya sa raɗaɗin fata yakuma haifar da 'yan ƙuraje idan akayi amfani dashi a baki ko matuci. A dakata da amfani dashi idan ya haifar da ƙuraje.

NBgrnimportant.png A lura
Shanshanbale yana canza launin duk wani abu zuwa shuɗi. Yana fita daga fata a 'yan kwanaki kaɗan amma zai iya ɓata launin kaya dun-dun-dun.

NBgrneyedrop.png Yadda ake amfani (da shi)

Yi amfani da ruwan 0.5% na methylrosanilinium chloride (shanshanbale).
A shafa a jikin fata, ko baki, ko saman matuci sau 2 ko 3 a rana.
Idan cutar bata fara warkewa ba acikin 'yan kwanaki, to a gwada wani maganin.

Nystatin


Nystatin yana aiki sosai ga duk yawancin cututtukan yis na baki, ko na kan nono ko na fata ko na matuci. Na baki yana zuwa a ruwa-ruwa, ko mai, ko hoda ko kuma na cusawa domin matuci.

Green-effects.png Illolin (sa)
Idan akayi amfani da nystatin a jikin fata zai iya yin birɗin-birɗin. Wannan ba wata matsalabace. A daina amfani dashi idan ya sa ƙuraje. Wani lokacin kuma yana sa gudawa.

NBgrnimportant.png A lura
Cutar yis data ƙi warkewa da yin amfani da nystatin, ko kuma ta cigaba da dawowa zata iya zama alamar cutar ƙanjamau.

NBgrneyedrop.png Yadda ake amfani (da shi)

Nystatin na ruwa yana zuwa a ma'aunin 100,000 duk ml (ko kuma wani lokacin yazo a 500,000 duk ml). Mafi yawan mutane sai suyi amfani da 100,000 zuwa 200,000, amma masu cutar ƙanjamau suna buƙatar har zuwa ma'auni 500,000 a duk amfani ɗaya.
Domin jariri mai cutar yis a baki
A bada 200,000 units na ruwan (maganin) (wato, ya gaza ½ cokalin shayi da ml 2), sau 4 a rana. A yi amfani da ɗan ƙyalle ko abin ɗigawa domin baza nystatin a cikin bakin. Acigaba da bada maganin har kwanaki 2 bayan cutar yis ɗin ta warke,domin wataƙila zata iya dawowa.
Domin mahaifiya mai shayarwa wadda take ɗauke da cutar yis akan nononanta (kaikayi, jaja-jaja, ko zafi)
A saka 100,000 zuwa 200,000 unit na nystatin na shafawa, ko hoda, ko ruwan maganin akan nonon sau 4 a rana.