Hesperian Health Guides

Magungunan ƙuna

Ƙuna suna da zugi sosai. A bada maganin rage zugi mai ƙarfi kamar codeine KO morphine, musamman kafin a tsaftace ko canza abinda aka lulluɓe ƙunar da shi.

Kuna suna da dama mai yawa wurin kamuwa da cuta, sabodahaka a bada antibiotic kamar dicloxacillin, clindamycin, cephalexin, KO ciprofloxacin idan da akwai wata alama ta kamuwa da cuta.

Idan ƙuna tana warkewa, sai a bada antihistamine kamar chlorpheniramine KO diphenhydramine domin rage ƙaiƙayi.

A bada rigakafin tetanus idan ba’a sabunta wa mutumin rigakafinsa ba (duba (sashin) Rigakafi-ana kan aikinsa).

Idan lokacin da mutumin yake cikin wuta ya shaƙi hayaƙi sosai, salbutamol zai iya taimaka masa domin yin numfashi cikin sauƙi.