Hesperian Health Guides

Magungunan cizon dabbobi

Taimakon farko

A tsaftace cizon dabba sosai da ruwa da sabulu. A bada antibiotics saboda gurbin cizon dabba sau dayawa yana kamuwa da cuta.

Amoxicillin da clavulanic acid shi ne zaɓi mafi kyau domin maganin cizon dabba.

Idan babu amoxicillin da clavulanic acid to a bada ɗayan waɗannan: DOXYCYCLINE KO
COTRIMOXAZOLE KO
PENICILLIN V

DAKUMA ɗayan waɗannan:
METRONIDAZOLE KO
CLINDAMYCIN

Idan cizon kare ne, har’ilayu sai a bada rigakafin cutar rabies dakuma rabies immunoglobulin (duba kasa).

Rabies immunoglobulin


A inda ake da dabbobi masu cutar rabies,duk wani cizo ko yakushi wanda ya fasa fata yana bukatar tsaftacewa sosai da ruwa dakuma sabulu har na tsahun a kalla mintina 15, kuma yana bukatar rigakafin cutar rabies, kuma idan cutar rabies tayi yawa to ana da bukatar allurar rabies ta immunoglobulin.

A kwai nau’uka biyu na rabies immunoglobulin, ɗaya ana yinta daga abinda ake kira da human serum (HRIG) (wato ruwan jikin mutum), dakuma wadda akeyi da horse serum (ERIG) (wato ruwan jikin doki). HRIG tafe rashin hatsari, amma tafi tsada kuma ba kasafai ake samunta ba.

Green-effects.png Illolin (sa)

Za a iya jin zafi dakuma kumburin wurin da akayi allurar.

NBgrnimportant.png A lura
Rabies immunoglobulin zata iya jawa alaji mai tsanani ga waɗansu mutanen. Sabodahaka koda yaushi ya zamo akwai epinephrine (adrenaline) koda za a sami alaji.

NBgrninject.png Yadda ake amfani (da shi)
Yi allurar rabies immunoglobulin a ciki da kuma kewayen tsaftataccen rauni. Idan adadinta bazai isa ayita a kewayen rauninba, a yi allurar sauran a gefen tsokar cinya.

Idan baka da ishasshiyar allurar da zaka yi a kewayen raunukan, to a ƙara saline domin ninka adadin. Tahaka sai dukkan raunin ya sami rigakafin.

Amfani da Human Rabies Immune Globulin (HRIG)
Yi allurar units 20 ga dukkan kg (na nauyin mutum) sau daya.

Amfanida Equine Rabies Immune Globulin (ERIG)
Yi allurar units 40 ga dukkan kg (na nauyin mutum) sau ɗaya.

Amfani da rigakafin cutar rabies

Idan za’a bada allurar cutar rabies ta immunoglobulin, to sai a hada da rigakafin cutar ta rabies. Amma ayi amfani da wata sabuwar allurar kuma ayi allurar a wani bangaran na jiki. Ayi alluara gabadayanta (wato ko dai 0.5ml ko 1ml dogaro da yadda kamfanin dayi allurar ya samar da ita). Ayi allurar a nama saman dantsen hannu a ranar da akayi cizon. Sannan a sake yi a rana ta 3 data 7. Daga nan sai ayi allurar ta hudu tsakanin kwana na 14 (sati 2) dakuma na 28 (sati 4) bayan cizon. Ga yaro dan shekara 2 ko kasa, ana yin allurar ne a naman cinya daga sama (ba a duwawu ba).

Koda babu allurar immunoglobulin, wanke fatar sosai nan take dakuma bada jiren rigakafin cutar rabies zai iya hana kamuwa da cutar.This page was updated:05 Jan 2024