Hesperian Health Guides

Magungunan radadi (zugi)

Taimakon farko

Magungunan sauƙaƙaƙƙen raɗaɗi (zugi) dakuma saukar da zazzaɓi sun hada da paracetamol (shi ne mafi rashin hatsari kuma mafi kyawun magani ga yara), aspirin dakuma ibuprofen. Aspirin da ibuprofen suna rage kumburi (kumburi mai jini). Misali, idan ka gurɗe a idan sawu, ba wai kaɗai zasu rage zafin bane kaɗai, zasu kuma rage kumburin. Wannan zai taimaka ka warke da wuri. Amma mutanen da suke zazzaɓi da kuma rashin lafiyar da ƙwayar cutar virus ta samar to su guji aspirin.

Kada ka bada sama da ƙa’idar da aka bayar na waɗannan magungunan Dukkanin waɗannan magungunan suna da illoli idan aka sha su sama da ƙa’ida. Misali, zarce ƙa’idar shan aspirin da ibuprofen zai iya jawo cutar ulcer (gyambon ciki). Paracetamol idan yayi yawa guba ne. Domin matsanancin zazzaɓi ko zogi, zaka iya rage yawansu ta caccanjawa tsakanin paracetamol dakuma ibuprofen.

Paracetamol, acetaminophen


Paracetamol magani ne me kyau marar tsada na zazzaɓi da kuma sassauƙan zugi.

NBgrnimportant.png A lura
Kada asha sama da ka’ida. Yawan sa yana da illa ga hanta kuma zai iya kisa. A ajiye wannan maganin a inda yara baza su iya kaiwa ba, musamman ma idan kana da na ruwansa mai zaƙi.

Magungunan sanyi saudayawa suna ɗauke da parcetamol, sabodahaka kada ka bada su idan zaka bada paracetamol domin zai yi yawa.

NBgrnpill.png Yadda ake amfani (da shi)

Bada mg 10 zuwa 15 ga dukkan nauyin kg 1, duk bayan sa’o’i 4 zuwa 6. Kada a bayar sama da sau 5 a cikin sa’o’i 24. Idan baza a iya auna mutumin ba ayi amfani da shekaru.
Ƙasa da shekara 1: bayar da mg 62 (rabin ¼ na ƙwaya mai nauyin mg 500), duk sa’o’i 4 zuwa 6.
Shekara1 zuwa 2: bayar da mg 125 (¼ na ƙwaya mai nauyin mg 500) duk sa’o’i 4 zuwa 6.
Shekaru 3 zuwa 7: bayar da mg 250 (½ na ƙwaya mai nauyin mg 500) duk sa’o’i 4 zuwa 6.
Shekaru 8 zuwa 12: bayar da mg 375 (¾ na ƙwaya mai nauyin mg 500) duk sa’o’i 4 zuwa 6.
Sama da shekaru 12: bayar da mg 500 zuwa 1000, duk sa’o’i 4 zuwa 6, amma kada a bada sama da 4000mg a rana.

Ibuprofen


Ibuprofen yana maganin ciwon jiki, ciwon gaɓoɓi dakuma ciwon kai, kuma yana sauƙaƙa zazzaɓi.

Green-effects.png Illolin (sa)
Ibuprofen zai isa jawa ciwon ciki, amma shan sa da madara ko kuma abinci yana rage wannan matsalar.

NBgrnimportant.png A lura
Kada ka sha ibuprofen idan kana da alaji da aspirin. Waɗansu mutanen da ke da alaji da wani maganin to suna da alaji da ɗan uwansa. Kada a bada ibuprofen domin maganin ciwon ciki ko rashin narkewar abinci. Ibuprofen yana da acid kuma zai iya tsananta matsalar. Kuma saboda wannan dalilin masu ulcer kada su sake suyi amfani da aspirin. Kada a bada ibuprofen ga jarirai yan ƙasa da watanni 6. Kuma kada a bawa mata masu juna biyu, a watanninsu 3 na ƙarshe.

NBgrnpill.png Yadda ake amfani (da shi)

Bada mg 5 zuwa 10 ga kowanne kg 1 na nauyi. Idan baza a iya auna mutumin ba, ayi la’akari da da shekaru.
Watanni 6 zuwa shekara 1: bada mg 50, duk sa’o’i 6 zuwa 8.
Shekara 1 zuwa 2: bada mg 75 duk sa’o’i 6 zuwa 8.
Shekaru 2 zuwa 3: bada mg 100 duk sa’o’i 6 zuwa 8.
Shekaru 4 zuwa 5: bada mg 150 duk sa’o’i 6 zuwa 8.
Shekaru 6 zuwa 8: bada mg 200 duk sa’o’i 6 zuwa 8.
Shekaru 9 zuwa 10: bada mg 250 duk sa’o’i 6 zuwa 8.
Shekaru 11: bada mg 300 duk sa’o’i 6 zuwa 8.
Sama da shekaru 12: bada mg 200 zuwa 400 duk sa’o’i 6 zuwa 8.

Kada a bada sama da mg 40 ga kowanne kg 1 na nauyi a rana. Kada a bada sama da sau 4 a rana kuma kada a bada sama da kwanaki 10 a jere.

Aspirin (acetylsalicylic acid)


Aspirin magani ne me kyau marar tsada na zazzaɓi da kuma sassauƙan zugi.

Green-effects.png Illolin (sa)
Aspirin zai iya jawa ciwon ciki ko kuma zafin zuciya. Domin maganin hakan, sha aspirin da madara, ko kuma soda ta bicarbonate, ko kuma da ruwa mai yawa ko kuma tare da abinci.

NBgrnimportant.png A lura

 • Kada a bada aspirin domin ciwon ciki ko kuma cushewar ciki. Aspirin yana da acid zai iya dagula matsalar. Kuma saboda wannan dalilin, mutane masu gyambon ciki kada suyi amfani da aspirin.
 • Kada a bada sama da adadi daya na aspirin ga wanda yake fama da rashin ruwa, har sai ya fara fitsari.
 • Zai fi kyau kada a bada aspirin ga yara ƙasa da shekaru 12 musamman ma jarirai, (paracetamol yafi rashin illa) ko kuma ga mai ciwon asma (wannan zai iya tada ciwon). Kada a bawa yara masu alamun mira, domin wannan zai iya kawo matsaloli.
 • A ajiye aspirin inda yara baza su iya kaiwa ba. Yawan adadinsa zai iya zame musu guba.
 • Kada a bawa mace me ciki.

NBgrnpill.png Yadda ake amfani (da shi)

Shekara 1 zuwa 2: bada mg 75 duk sa’o’i 6.
Shekaru 3 zuwa 7: bada mg 150 duk sa’o’i 6.
Shekaru 8 zuwa 12: bada mg 300 duk sa’o’i 6.
Samada shekaru 12: bada mg 300 zuwa 600 duk sa’o’i 4 zuwa 6.

Kada a bada sama da mg 2400 a rana. Kada a bawa yara sama da sau 4 a rana.

Domin ciwon zuciya
Bada mg 300 zuwa 325 ta baka nan take. A tauna a haɗiye.

Codeine (codeine sulfate)


Codeine magani ne na zogi wanda ke cikin dangin opiate. Ana amfani da shi wajan maganin matsanacin zogi. Yi amfani da codeine idan sauƙaƙan magungunan rage zogi suka kasa amfani.

Green-effects.png Illolin (sa)
Zai iya haifar da cushewar ciki (wahalar yin bayan gida) dakuma rashin iya yin fitsari na wani ɗan lokaci. Zai iya kuma kawo jin amai, ko yin amai, ko ƙaiƙayi dakuma ciwon kai.

NBgrnimportant.png A lura

 • Codeine ƙwayar magani ce mai kama mutum. Dan haka a guji amfani da ita na tsahon lokaci ko kuma akai-akai.
 • Kada a sha giya a lokacin da ake amfani da codeine domin zai iya jawa illa mai hatsari ko kuma ma mutuwa.
 • Codeine zai iya shafar tunanka da aikin ka a lokacin da kake amfani dashi. Hattarai dai idan kana tuƙi ko kuma kana yin wasu abubuwan dake da bukatar nutsuwa.
 • Rage adadin lokaci bayan lokaci domin daina yin amfani da shi gaba daya. Tsayar da amfani da shi a lokaci daya zai iya jawo alamomin daina yin amfani da abu marasa daɗi.
 • Kada kaye amfani da codeine idan ka taɓa samun alaji da morphine.
 • Kada kiyi amfani da codeine idan kina da juna biyu ko kuma shayarwa.

NBgrnpill.png Yadda ake amfani (da shi)

Bada codeine tare da abinci.
Shekaru 3 zuwa 6: bada ½ zuwa mg 1 ga kowanne kg 1 na nauyi ta baka, duk sa’o’i 4 zuwa 6.
Shekaru 7 zuwa 12: bada mg 15 zuwa 30 ta baka, duk sa’o’i 4 zuwa 6.
Sama da shekaru 12: bada mg 15 zuwa 60 ta baka, duk sa’o’i 4 zuwa 6. kada a bada sama da mg 360 a rana.

Morphine


Morphine maganin zogi ne dake cikin dangin opiate. Ana amfani da shi wurin warkar da matsakaici zuwa matsanancin zogi.

NBgrnimportant.png A lura

 • Morphine ƙwayar magani ce mai kama mutum. Dan haka a guji amfani da ita na tsahon lokaci ko kuma akai-akai.
 • Kada a sha giya a lokacin da ake amfani da morphine domin zai iya jawa illa mai hatsari ko kuma ma mutuwa.
 • Morphine zai iya shafar tunanka da aikin ka a lokacin da kake amfani dashi. Hattarai dai idan kana tuƙi ko kuma kana yin wasu abubuwan dake da buƙatar nutsuwa.
 • Rage adadin lokaci bayan lokaci, domin daina yin amfani da shi. Tsayar da amfani da shi a lokaci ɗaya zai iya jawo alamomin daina yin amfani da abu marasa daɗi.
 • Kada kaye amfani da morphine idan ka taɓa samun alaji da codeine.
 • Kada kiyi amfani da morphine idan kina da juna biyu ko kuma shayarwa.

NBgrnpill-inject-drop.png Yadda ake amfani (da shi)
Domin matsakaici dakuma matsanancin zogi

Ƙasa da watanni 6: bada mg 0.1 ga duk kg 1 na nauyi ta baka, duk sa’o’i 3 zuwa 4. Idan baza a iya auna nauyin jaririn ba, a bada mg 0.5 ta baka, duk sa’o’i 3 zuwa 4.
Sama da watanni 6: bada 0.2 zuwa 0.5mg ga duk kg 1 na nauyi ta baka, duk sa’o’i 4 zuwa 6 gwargwadon buƙata.
Idan baza a iya auna mutumin ba a bayar ta la’akari da shekaru:
Watanni 6 zuwa shekara 1: bada mg 2 ta baka, duk sa’o’i 4 zuwa 6.
Shekara 1 zuwa 5: bada mg 3 zuwa 5 ta baka, duk sa’o’i 4 zuwa 6.
Shekaru 6 zuwa 12: bada mg 8 ta baka, duk sa’o’i 4 zuwa 6.
Sama da shekaru 12: bada mg 10 zuwa 30 ta baka, duk sa’o’i 4 zuwa 6.


Domin ciwon zuciya
Yi allurar mg 10 ta cikin tsoka a hankali har tsahon mintina 5 (mg 2 duk minti daya). Sake yin wata allurar ta mg 5 zuwa 10 idan ya zama dole.


This page was updated:05 Jan 2024