Hesperian Health Guides

Magungunan ciwon zuciya

A bada aspirin nan take ga wanda ciwon zuciya ya buge. A hanyar asibiti a bada nitroglycerine idan da akwai.

Zaka kuma iya bada morphine domin magancie raɗaɗin dakuma tsoro, kuma ya sauƙaƙawa zuciyar wajan turo (jini).

Nitroglycerine (glyceryl trinitrate)


Ana amfani da nitroglycerine wajan magance zafin ƙirji na ciwon zuciya. Yana taimakawa wajan kara faɗin hanyoyin jini wanda zai sa zuciya ta sami sauƙi wurin turo jini.

NBgrnimportant.png A lura
Kada a bada nitroglycerine ga wanda bugun jinin sa yayi ƙasa ko kuma wanda ya sha sildenafil (Viagra) a cikin sa’o’i 24 da suka wuce. Haɗin waɗannan magungunan zai iya sa bugun jini yayi kasa sosai har ya zamo hatsari, kuma zai iya kisa.

Green-effects.png Illolin (sa)
Zai iya kawo matsanancin ciwon kai, jin zafi ko kuma jiri.

NBgrnpill.png Yadda ake amfani (da shi)
Sai mutumin ya zauna ko ya kwanta, kada ya tashi tsaye, saboda jiri.

A bada ½mg (0.5mg) a narkad dashi a karkashin harshe, kada a bada sama da sau 3, a jera mintina 5 tsakanin kowanne magani. Idan ciwon kirjin dakuma sauran alamomin sun gushe, to ba’a bukatar karin wani maganin. Kada a tauna ko a hadiyi kwayoyin maganin nitroglycerin. A lokacin da maganin yake narkewa a karkashin harshe, zakaji yana kuna a hankali.