Hesperian Health Guides

Magungunan kashe wuri

Taimakon farko

Lidocaine, lignocaine


Lidocaine anesthetic ne (wato nau’in magungunan dake kashe wuri su hana jin zafi) wanda ake allurar sa a kewayen geffan rauni domin ya kashe wurin ya hana jin zafi. Wannan yana da amfani kafin a tsaftace ko kuma a ɗinke rauni.

Lidocaine sau dayawa yana zuwa a nau’in ruwa-ruwa wanda yake ɗauke da kaso 2% wato mg 20 na lidocaine a duk ml. Idan kana da ruwa-ruwan lidocaine wanda yawansa ya banbanta da wanda aka ambata, to ka dai-daita yawan wanda zakayi amfani da shi.

NBgrninject.png Yadda ake amfani (da shi)
A hankali yi allurar ta hanyar soka ta ƙarƙashin fatar dake kewayen inda za’a yanka ko ɗinke, a wurare masu nisan cm 1 da juna. Yi allurar lidocaine ɗin daf da saman fata. Yi amfani da ml 1 na lidocaine ga duk cm 2 ta fata. Kada ayi amfani da sama da ml 20.


This page was updated:05 Jan 2024