Hesperian Health Guides

Taimakon farko

A wanna kashin:

A samar da nutsuwa da tasarifi

Idan abin gaggawa ya faru, bin matsalar da kake fuskanta daki-daki zai taimaka maka kayi tunani mai kyau, da kuma kulawa da matsalar data fi muhimmanci da farko.

1. Ja dogon numfashi. Harkokin gaggawa su kan zamo masu ban tsoro. Amma, iya nutsuwar ka iya amfanin ka (a irin wannan lokacin). Kasancewa cikin nutsuwa shima zai taimaka wajan kwanciyar hankalin wanda ko waɗanda suka ji raunin dake a kiwayanka.
2. Tambayi kanka: shin wannan wurin bashi da wani hatsari? Ka nesantar da kanka dakuma marar lafiyar daga wuta ko hanyoyi masu yawan zirga-zirga ko kuma waɗansu wuraran hatsarin. (Idan wataƙila mutumin yana da raunin wuya ko na baya, a matsar da shi a cikin kulawa tayadda baza a motsa wuyan nasa ba.)
3. Fara duba matsala mafi hatsari. Koma me ya jawo raunin, a duba numfashi nan take. Shi ne abinda akafi buƙata domin rayuwa. Duba matsalar numfashi.
4. Bayan an duba numfashi, sai a duba zubar jini. Zubar jini mai tsanani tana iya kisa.
5. Idan mutumin yana numfashi kuma aka tsaida zubar jinin mai tsanani, to sai ka duba duk sauran jiki ko da waɗansu raunikan ko karaya. A fara daga kai sannan a duba duk sauran jiki, gaba da baya, ƙasa har zuwa ‘yan yatsun ƙafa. Ayi tambayoyi a cikin nutsuwa, a duba mutumin, kuma a tattaɓa jikin a hankali domin ganin koda rauni a ciki a ɓoye. Abu ne gama gari a sami sama da rauni ɗaya, kuma wadansu ba’a iya ganin su a duban farko.
6. Yi ƙoƙari ka kasance cikin tausasawa da nutsuwa gwargwadon iyawarka. Watakila wanda yayi raunin a tsorace yake kuma cikin raɗaɗin ciwo. Ta hanyar kwantar masa da hankali, zaka iya taimaka masa numfashinsa da bugun zuciyarsa su dawo dai-dai.

A rika yawan binkicen numfashi da zubar jini. Idan za’a iya gwada karfin gudanar jininsa (blood pressure) to a rika yawan gwada ta. Wanda yaji rauni da farko zai iya zamowa kamar babu abinda ya dame shi, kuma cikin dan lokaci kaɗan abubuwa sai su rikice. A rinƙa yawan gwajin wadannan muhimman alamomin rayuwar, har sai an tabbatar babu wata matsala. A cigaba da yi masa magana. Wannan zai taimaka maka wajan sanin ko a ruɗe yake ko kuma ruɗewarsa ta ƙaru.

Wata mace tana yiwa wani mutum magana acikin taro, alhalin tana taimakon wani wanda yaji rauni.
Tana cewa ku maida mutane baya. Zan taimake shi.


Mutanen da suka taro bayan anyi hatsari yana da kyau a riƙa ƙara musu ƙwarin gwiwar taimakawa. A saka mutane masu ƙwazo da babbar murya da su samar da sarari a wurin da waɗanda suka yi hatsari suke. A sami wani ya kirawo ma’aikatan lafiya. Ko kuma ya samo kayayyakin jiya, kamar su ƙyallaye (domin yin bandeji), ko mayafai. A rabawa kowanne mai taimako aiki, domin a samar da nutsuwa kuma a kammala ayyukan dake buƙ atar gaggawa. Idan mutane dayawa sun sami rauni, a duba Masifu da kaura (ana kan aikinsa) domin sanin yadda ake yanke shawar wanda yakamata a fara taimakawa (idan anyi hatsari).

Wanda yaji rauni shima zai iya taimakawa kansa. Yawancin mutanen da suke zubadda jinni (idan sunji rauni) za su iya matse raunikan nasu (domin hana zubar da jini). Wannan zai iya sawa ya (mai raunin) ya nutsu, kuma ya baka dammar duba sauran raunikan ko kuma waɗansu mutanen da suka ji rauni.

? Ka tambayi me raunin ko yana jin ciwo, ko dindiris ko wahalar motsi.
NWTND fa Page 3-1.png
To waɗannan alamomi ne na gurɗewa ko karyewar kashi. Ka duba bayani akan karyayyun haƙarƙari da karyayyun ƙasusuwa. Ida ana jin dindiris ko kuwa wahalar motsa kasan jiki ko kuma dukkan jikin, to watakila akwai raunin ƙashin baya.
Ka tambaya ko kuma ka lura, ko suna da matsalar yin numfashi, ko kuma suna shaƙewa.
NWTND fa Page 3-1.png
Matsanancin zafi wajan yin numfashi zai iya zamowa alamar karyayyen hakarkari.
NWTND fa Page 3-1.png
Daukewar numfashi, matsiwar ƙirji, dakuma kusur-kusur (wajan yin numfashi) alamomi ne na asima (a duba Matsalolin yin numfashi da tari-ana kan aikinsa).
NWTND fa Page 3-1.png
Matsalar yin numfashi zata iya kasancewa a dalilin sinadarai masu guba ko shan magani samada ka’ida.
A lura idan suka zamo a ruɗe ko kuma suna samun matsala wurin yin magana sosai. Wannan zai iya taimaka maka kasan irin tsananin rauninsu. A duba me yakamata ayi idan mutum baya cikin hayyacinsa.
NWTND fa Page 3-1.png
Yawancin mutane sukan ruɗe idan anyi hatsari. Amma rashin yin magana sosai, fita-daga-hayyaci dakuma ruɗewa ta dogon lokaci zasu iya zama alamomin raunin kai ko kuma buguwa saboda shan ƙwayoyi ko giya.
NWTND fa Page 3-1.png
Surutai ko maganganu marasa ma’ana zasu iya zama alamar stroke (mutuwar barin jiki). Shin wani ɓangare na fuska ko jiki ya shika ko kuma kamar yayi rauni? A duba Matsalolin kai da kwakwalwa (ana kan aikinsa).
NWTND fa Page 3-1.png
Ruɗewa ko kuma canjawar tunani zai iya kasancewa alamar ciwon suga mai buƙatar kulawar gaggawa. Duba abin da yakamata ayi idan mutum ya kamu da rashin lafiya kwatsam.
? A duba da kyau: Shin akwai zubar jini, kumburi, kujewa, ja-ja ja-ja ko bacin kamannin wani ɓangare na jiki? Danganta bangare ɗaya na jiki da ɗayan. Misali, idan ƙafa ɗaya tafi ɗaya to zai iya kasancewa akwai karaya a ɗayar.
NWTND fa Page 3-1.png
A duba abinda yakamata ayi saboda zubar jini.
NWTND fa Page 3-1.png
Domin sanin koda karaya, a duba bayani akan karyayyun haƙarƙari da karyayyun ƙasusuwa.
NWTND fa Page 3-1.png
Kujewa, kumburi da kuma ja-ja ja-ja zai iya zamowa alamomin taruwar jini a cikin jiki. (saboda haka) A zauna cikin shirin samun girgiza.
? Shafa kai, fiska, wuya, baya, gaba, hannayi, da ƙafafu a hankali, Shin akwai ciwo, dundurus ko kuma gucewar ƙashi? Idan wataƙila akwai raunin baya ko na wuya, to a taɓa kowanne ɗaya daga cikin ƙasusuwan bayan tun daga ka har zuwa tsakanin ɗuwawu.
NWTND fa Page 3-1.png
Duba abinda yakamata ayi ga alamomin raunin kai.
NWTND fa Page 3-1.png
Duba abinda yakamata kayi idan kana zatun akwai rauni a kai, wuya ko baya kafin ka motsa mutumin (majiyacin).


This page was updated:05 Jan 2024