Hesperian Health Guides
Magungunan hana damuwa
Kundin bayanan lafiya na Healthwiki > Sabon littafin A inda babu likita > Taimakon farko > Magungunan hana damuwa
Diazepam
Za a iya amfani da diazepam domin sakar da tsoka dakuma hana jin zafi. Za kuma ana iya amfani da shi domin tsayarda fyarfyaɗiya ta farar ɗaya. Domin mutane masu fyarfyaɗiya mai gudana, yi amfani da wani maganin daban, wanda za a iya sha a kullum.
Illolin (sa)
Jin bacci
A lura
- Yawan diazepam zai iya rage numfashi ko kuma ma ya tsayarda shi. Kada a bada adadin sama da sau biyu kuma kada a bada sama da mg 30 a rana daya.
- Diazepam ƙwayar magani ce mai kama mutum. Dan haka, a guji amfani da ita na tsahon lokaci ko kuma akai-akai
- Kada asha lokacin da ake da juna biyu ko kuma sanda ake shayarwa sai dai idan da akwai matsanciyar pre-eclampsia ko fyarfyeɗiya.
- Kada ayi allurar diazepam a cikin tsoka ko jijiyar jini har sai idan ka iya ko kuma an koya maka. Yana da wahala ayi allurar ta lami-lafiya. Maimakon haka, a lokacin fitar hankali sai a saka ta ta cikin dubura (duba kasa).
Yadda ake amfani (da shi)
Domin sakin tsokokin jiki dakuma tausasa mutum
Ƙasa da shekara 5: bada mg 1.
Sama da shekaru 5: bada mg 2.
Domin fyerfyaɗiya
Ƙasa da shekaru 7: bada mg 0.2 ga duk kg 1 na nauyi, sau ɗaya.
Shekaru 7 zuwa 12: bada mg 3 zuwa 5, sau ɗaya.
Sama da shekaru 12: bada mg 5 zuwa 10, sau ɗaya.
Idan ba’a shawo kan fyerfyeɗiyar ba har bayan mintina 15 da bada maganin, to a maimaita adadin. Kada a maimaita sama da sau ɗaya.
Lorazepam
Lorazepam kusan dai-dai yake da diazepam. Za a iya amfani da shi wurin sakar da tsokokin jiki dakuma nutsar da mutum. Kuma za a iya amfani da shi wurin tsayar da fyerfyeɗiyar farar ɗaya. Ga mutane masu fyerfyeɗiya mai gudana (epilepsy), a yi amfani da wani maganin daban, wanda za a iya sha kowacce rana.
Illolin (sa)
Jin bacci.
A lura
- Yawan lorazepam zai iya rage numfashi ko kuma ma ya tsayarda shi.
- Lorazepam ƙwayar magani ce mai kama mutum. Dan haka, a guji amfani da ita na tsahon lokaci ko kuma akai-akai.
- Kada asha lokacin da ake da juna biyu ko kuma sanda ake shayarwa sai dai idan da akwai matsanciyar pre-eclampsia ko fyarfyeɗiya.
- Kada ayi allurar lorazepam a cikin tsoka ko jijiyar jini har sai idan ka iya ko kuma an koya maka. Yana da wahala ayi allurar ta lami-lafiya. Maimakon haka, a lokacin fitar hankali sai a saka ta ta cikin dubura (duba sama).
Yadda ake amfani (da shi)
Domin sakin tsokokin jiki dakuma tausasa mutum
Wata 1 zuwa shekaru 12: bada mg 0. 05 ga duk kg 1 na nauyi, sau ɗaya.
Sama da shekaru 12: bada mg 1 zuwa 2, sau ɗaya.