Hesperian Health Guides

Magungunan kariyar cutar tetanus

Taimakon farko

Antitetanus immunoglobulin (ta dan Adam)


Idan ba a sabuntawa mutum rigakafinsa na cutar tetanus ba (gabaɗaya allurai 3, dakuma allurai masu ƙara ƙarfin rigakafin duk bayan shekaru 10), to sai ayi masa antitetanus immunoglobulin a cikin gaggawa bayan jin raunin da ka iya jawo tetanus. A bada antitetanus immunoglobulin kafin alamomin cutar tetanus su fara (bayyana). Idan za a bawa mutum dukkanin rikafin tetanus (duba sashin) Rigakafi-ana kan aikin sa) dakuma antitetanus immunoglobulin a lokaci daya, ayi amfani da allura daban-daban kuma ayi alluran a wurare daban-daban na jiki.

Kada ayi rigakafin ƙwayar cutar virus mai-rai a cikin watanni 3 bayan anyi wa mutum antitetanus immunoglobulin domin zata iya rage ƙarfin rigakafin.

Green-effects.png Illolin (sa)
Za a iya jin zafi dakuma kumburin wurin da akayi allurar.

NBgrnimportant.png A lura
Antitetanus immunoglobulin zai iya jawa alaji mai tsanani ga waɗansu mutanen. Sabodahaka, koda yaushi ya zamo akwai epinephrine (adrenaline) koda za a sami alaji.

NBgrnpill.png Yadda ake amfani (da shi)
Idan ana allurar a sokata can cikin tsoka.

Ga raunin da aka ji a ƙasa da sa’o’i 24.
Ayi allurar units 250 sau ɗaya.

Ga raunin da aka ji a sama da sa’o’i 24, ko kuma raunin da ake kyautata zaton kamuwa da tetanus.
Ayi allurar units 500 sau ɗaya.

Har’ilayau kuma a bada antibiotic kamar metronidazole KO penicillin G.