Hesperian Health Guides

Tetanus (sarƙewar muƙamiƙi)

A wanna kashin:

Tetanus cuta ce mai matuƙar hatsari wadda take shiga cikin rauni ko cibiyar (jarirai sabuwar haihuwa), daga nan sai ta yaɗu zuwa duk sauran jiki.

wani mutum yana kwance bayansa a ƙandare kuma ‘yan yatsunsa a dunƙule.
Alamomin cutar tetanus suna iya farawa bayan kwana ɗaya ko kuma sati da jin ciwo.
Alamomi
  • Gumi.
  • Bugun zuciya da-sauri-da-sauri.
  • Diddinƙulewar tsokar (jiki).
  • A lokacin ɗinkulewar, numfashi zai iya tsayawa.
  • Dinƙulewa mai ƙarfi ta tsokar jiki wadda ke faruwa sannan ta lafa.
  • Sarƙewar muƙamiƙi (wadda ke sa baki yaƙi buɗuwa cikin sauƙi.)
  • Sanƙarewar wuya dakuma sanƙarewar ruwan ciki.


A nemi taimakon likita cikin gaggawa idan an ga waɗannan alamomin!

Kare kai ko Riga kafi

Cutar tetanus tafi sauƙin yin rigakafi akan yi mata magani. Allurar rigakafi dakuma kyakkyawan tsaftace rauni su ne mafi kyawun kariya daga gareta. Domin tsara yin rigakafin, duba Riga kafi (ana kan aikin).

Irin raunukan da ka iya kamuwa da tetanus

  • Raunukan huda ko suka.
  • Raunukan harbin bindiga.
  • Karyewar ƙashi, idan ƙashin ya fito
    ta cikin fata (buɗaɗɗiyar karaya).
ƙafa mai buɗaɗɗiyar karaya.
  • Muguwar ƙonuwa ko raunin ƙanƙara.
  • Zubar da ciki mai hatsari dakuma yin allura ko huda da allura wadda aka yi amfani da ita, kuma ba a kashe ƙwoyoyin cutar dake jiki ba, za su iya kawo kamuwa da cutar tetanus.


ƙafa ta taka ƙusa wadda ta fito ta cikin katako.
wata budurwa tana yi wa kanta allura da sirinji a lokacin da wani saurayi yake magana.
Karɓa ta ce.
waya mai kayoyi.
allura tana huda fatar kunne.


A tsaftace waɗannan raunukan sosai sannan a bada antitetanus immunoglobulin idan alluran rigakafin tetanus tsofaffi ne.
Kuma a bada metronidazole.

Cutar tetanus ta sababbin haihuwa

Sababbin haihuwa suna kamuwa da cutar tetanus ta cibiya. Za’a iya kare jarirai ta hanyar yanke cibiyar da tafasashshiyar wuka, ta hanyar tsaftaci cibiyar dakuma yin allurar riga kafi ga uwa mai ciki. Duba Riga kafi (ana kan aikin sa).

This page was updated:05 Jan 2024