Hesperian Health Guides

Ƙunuwar sinadarai

A wanna kashin:

Ha NWTND fa Page 40-1.png

Ka kare kanka da farko: Saka riga mai dogon hannu da safar hannu ko kuma wata jaka akan hannayen ka. Ka rufe bakinka da hankici. Ka wanke jikinka da kayanka sosai bayan ka taimakawa duk wanda ya bayyana ga sinadarai (ma'ana wanda hatsarin shafar chemicals).

Hanya mafi kyau ta kare kai daga ƙonuwar sinadari shi ne kauda sinadarin da gaggawa gwargwadon iyawa.

  1. A cire kayan sawa ko yarin dake kusa da ƙunar.
  2. Idan sinadarin mai maƙalewa ne a jiki, to nan-da-nan a cire shi da itace mai faɗi,ko gefen wuka, ko wani abin mai ƙarfi.
  3. Bayan ka cire dukkan sinadarin da zaka iya, sai a wanke kewayen wurin da ruwa mai yawa. Ruwa kan saka waɗansu sinadaran su fara ƙuna, to ka tabbatar tun farko an cire sinadarin sosai yadda zaka iya. Idan sinadarin mai maiko ne, yi amfani da sabulu da ruwa. Yi amfani da mesa ko famfo idan da akwai. Idan fiska ta taɓu, to a fara wanke ta. Kuma a tsaftace duk wani yanka ko kofa dake jikin fata. Iya sauri dakuma daɗewar da akayi wurin wanke wa iya damar ƙaranta illa ga fata.


Bayan ka tsaftace dukkan sinadarin daga jikin mutumin, to ayi wa ƙunar magani kamar yadda ake yi wa sauran kuna.

A wanke ko a jefar da dukkan wani kaya da sinadaran suka taɓa, saboda suma zasu iya haifar da illa.

NWTND fa Page 40-2.png
Idan sinadarin ya shiga ido, a kwara ruwa a cikin idon (kusa da hanci) ya rika fitowa ta gefen idan (kusa da kunne).



This page was updated:05 Jan 2024