Hesperian Health Guides

Fyaɗe

A wanna kashin:

Yin jima’i ta ƙarfi, ko yin jima’i ba tare da amincewa ba shi ake kira da fyaɗe. Babbar mace ko yarinya wadanda suka sansu zasu iya yi masu fyaɗe, ko wadanda basu sansu ba, ko danginsu ko mazansu na aure ko samarinsu. Maza manya ko kanana ana iya yi musu fyaɗe. Domin ƙarin bayani kan fyaɗe, duba sashi akan Tashin hankali (ana kan aikinsa).

Duk wanda aka yi wa fyaɗe yana buƙatar taimakon gaggawa domin raunin daya bayyana. Kuma tana da buƙatar tallafi na kwantar da hankali dakuma kulawa. A mu’amalanceta da jinƙai da kuma fahimtar halin da take ciki. Kada a zarge ta.

NWTND fa Page 36-1.png

Fyaɗe kan iya samar da juna-biyu. Bada maganin hana ɗaukar ciki mai yawa kan iya kare samun juna-biyu. Duba Tsarin iyali (ana kan aikinsa). Fyaɗe kuma kan iya jawo yaɗuwar cututtukan jima’i. Duba Matsaloli da cututtukan al’aura (ana kan aikinsa). Domin kariya daga kamuwa da Cutar Ƙanjamau bayan anyi fyaɗe, duba HIV da AIDS (ana kan aikinsa).

Zaki iya samun matsala wajan duba ta ko taɓa jikinta, sabodahaka, sai ki yi mata bayanin abinda zaki yi mata a lokacin da ki ke dubata, ko kuma yi mata magani, kuma ki tambayi izininta kafin ki tabata.

Idan matucinta ya yage, ko yanke, ko akwai taruwar jini to wannan zai haifar da jin zafi. Sabodahaka, a bada acetaminophen ko ibuprofen. Idan akwai zubar jini mai yawa ta baya ko matanci,to a matse wurin domin tsaida jinin. Ki koya mata yadda zata iya yi dakanta,domin ko jinin zai sake dawowa daga baya.

Domin yanka ko yagewa ‘yar kadan, ayi ruwan dumi sau 3 a rana. Kwarara ruwa akan matanci a lokacin da ake yin fitsari zai taimaka wajan rage jin zafi. Manyan yanka ko yaga suna da buƙatar ɗinki.

rahoton asibiti, wanda ya kunshi zane na jikin mutumin da guraben raunukan.
Yi alamar duk wani rauni da ka samu kuma a ɗauki hoto idan ta bada izini. Wannan zai taimaka maka idan kayi bibiya domin tabbatarda cewa tana samun sauki. Kuma za’a iya amfani dashi idan tayi nufin zuwa wurin ‘yansanda.

A duba raunuka a sauran sassan jikinta, kuma a duba waɗansu ɓangarorin wannan sashin domin magance waɗansu matsalolin. Rubutaccen bayani na binciken zahiri na raunukan da aka samu, abune wanda ya zama dole, idan matar ta kai rahoto wurin ‘yan sanda, ko da kuwa ta kai rahoton ne bayan faruwar abun da daɗewa.
Sake bibiyar matar bayan ‘yan kwanaki domin lura da halinda take ciki a zahiri dakuma hankali. Duba yanka ko yagar da ta samu domin ganin alamomin kamuwa da cuta. Cututtukan mafitsara (duba Wahala wurin yin Fitsari-ana kan aikinsa)) sau dayawa sukan faru bayan fyeɗe.


This page was updated:05 Jan 2024