Hesperian Health Guides

Taruwar jini

A wanna kashin:

Taruwar jini na nufin cewa naman dake ƙarƙashin fata ya sami matsala kuma jini yana fita daga cikin jijiyoyin. Taruwar jini takan yi ciwo sosai har ta haifarda damuwa ga mutum, amma so dayawa ba wata matsala ba ce. A magance taruwar jini kamar yadda ake maganin lanƙwasa ko kujewar ƙarƙashin fata, ta hanyar: hutu, saka ƙanƙara, matsewa dakuma ɗagewa.

Taruwar jini a ka ko ciki zai iya zamowa alama ta babbar matsala. A duba abinda yakamata a yi idan mutum ya sami babbar buguwa a ka ko zunguri a ciki.

Idan aka lura da wani yana yawan samun taruwar jini, ko kuma akwai taruwar jini mai yawa a matakai daban-daban na warkewa, to wannan zai iya kasancewa alamar zalunci (ta hanyar fyede ko duka). Duba Tashin hankali (ana kan aikin).


This page was updated:05 Jan 2024