Hesperian Health Guides
Babu bugun zuciya
Kundin bayanan lafiya na Healthwiki > Sabon littafin A inda babu likita > Babu bugun zuciya
A saurari bugun zuciya a wuya, kamar yadda aka nuna a ƙarƙashin (hoton) Busar numfashin ceto. Ko kuma a saurara a bangarin hagu na ƙirji, a inda aka sa alamar X.
Idan babu bugun zuciya, to yi ƙoƙarin fara shi da danniyar ƙirji. Yana da muhimmanci a fara danniyar ƙirji a cikin gaggawa, saboda idan baka da tabbas din samun bugun zuciya ko kuma bugun zuciyar bashi da ƙarfi yafi rashin illa ayi danniyar ƙirji.
Ayi danniyar ƙirji
Tura tsakiyar ƙirji da ƙarfi kuma da sauri sau 30. Tura ƙasa kamar cm 5 (in 2). Gwada ƙara yawan dannawar, aƙalla kamar sau 100 a minti ɗayahaƙiƙance yawan bashi da wani muhimmanci. Danna da ƙarfi kuma da sauri!
Yi busar numfashin ceto
Bayan danniyar ƙirji kamar sau 30, sai a yi busar numfashin ceto sau 2 wannan zai sa ƙirjin ya ɗaga.
Cigaba da danniyar ƙirji dakuma busar numfashin ceto
Cigaba da rabawa tsakanin dukkan danniyar ƙirji guda 30 sai ayi busar numfashin ceto guda 2. Wataƙila zakayi ta yin hakan har dogon lokaci. Yi ta yi har sai mutumin ya fara numfashi kuma ya faɗaka. Ko kuma har sai an tabbatar ya mutu.
Nemi taimako
Wannan zai farfaɗo da mutum bayan wuta ta ja shi, ko kuma ya nutse a ruwa ko kuma anyi masa duka mai ƙarfi a ƙirji ko kuma hypothermia (sanyi mai tsanani) ya kama shi ko kuma yasha magani sama da ka’ida.
Ba kasafai danniyar ƙirji take taimakon mutum ba idan ya sami bugun zuciya, amma za’a iya gwadawa, musamman ma idan za’a iya samun ƙarin taimakon ma’aikatan lafiya. (Duba ƙarin bayani akan bugun zuciya.)
Wata na’urar likita wadda ake kira da ‘defibrillator’ ta na iya bada ƙarfin jan wutar lantarki wanda zai iya taimakawa wajan tasar da zuciya bayan an sami bugun zuciya. Ka duba ko da akwai wannan na’ura mai suna defibrillator a wurin al’umar ko kuma a ina aka ajiye su kafin buƙatar gaggawa ta taso. Wanni lokacin akan same su acikin motar ɗaukar marasa lafiya, ko kuma inda mutane suke taruwa, kamar ofishin ‘yan sanda ko kuma babban otal.