Hesperian Health Guides

Taimakon gaggawa ga ciwon siga

A wanna kashin:

Ciwon suga wata cuta ce dake hana jiki sarrafa sikarin dake cikin abinci. Mai ciwon suga zai iya kamuwa da rashin lafiya kwatsam idan jikinsa na ɗauke da siga mai yawa ko kuma kaɗan, a cikin jininsa. Ciwon suga an fi samunsa a wurin mutane masu nauyin jiki, amma kowa ma zai iya kamuwa da ciwon suga. Domin ƙarin bayani akan ciwon siga duba sashin Matsanantan cututtuka (ana kan aikinsa).

Idan kasan wani yana da matsala saboda ciwon siga, amma baka da tabbas ko matsalar ta ƙaraci ko kuma yawan siga a cikin jini ce to; ka yi masa magani a matsayin mai ƙarancin siga, sannan ka kaishi domin samin taimakon likita.

Ƙarancin suga (a jiki) (hypoglycemia)

Sikarin dake jinin jikin mutum zai iya yin ƙasa sosai idan mutum yana amfani da sinadarin insulin ko kuma wani maganin na ciwon siga, idan yana shan maganin dayawa kuma baya cin abinci isashasshe ko kuma yayi aikin ƙarfi dayawa ko kuma ya sami jinkiri mai yawa na cin abinci ko yana shan giya.

Wanda yake da ƙarancin siga a cikin jini zai iya fiskantar tsananin kasala, ya ruɗe ko kuma ya hasala nan-da-nan. Zai iya yin gumi ko karkarwa. Idan hakan ta faru, to dole ne ya samu ya ci abinci. Idan bai ci abinciba halinda yake ciki zai iya ƙara taɓarɓarewa kuma ya sami waɗannan alamomi masu hatsari:

ga wani mutum ya kasa tafiya wata mata kuma tayi biris da shi.
Matsalar ƙarancin siga a jini nasa mutum yayi yanayi da wanda ya bugu (da giya), sabodahaka, za’a iya biris da shi ayi tsammanin ba abin gaggawa bane.
Alamomi masu hatsari
  • Kasa tafiya ko kuma jin kasala
  • Matsalar gani sosai
  • Ruɗewa ko yin baƙon abu (zaka iya tunanin ya bugu (da giya ne)
  • Fita daga hayyaci
  • Suma
Magani

Idan yana cikin hayyacinsa, a bashi sikari a cikin gaggawa: ruwan ‘ya’yan itatuwa, lemon soda, alawa ko kuma ruwa wanda aka hada da siga mai yawa duk zasu yi amfani. Bayannan kuma ya ci abinci isashshe. Idan har yanzu yana cikin ruɗu ko kuma bai fara jin dai-dai ba har tsahon minti 15 da ga bashi sikari, to a nemi taimako.

Idan baya cikin hayyacinsa, a saka dan danƙin sikari a ƙarƙashin harshensa. Sannan a cigaba da bashi kaɗan-kaɗan. Yana ɗaukar lokaci kafin jiki yayi amfani da siga. Idan ya farka to sai a ƙara masa.

Yawan sikari a cikin jinni (hyperglycemia)

Me ciwon siga za’a iya samun sikari yayi yawa a cikin jininsa idan yana yawan cin abinci dayawa, kuma baya yawan motsa jiki, ko kuma ya kamu da wata matsananciyar cuta, ko kuma baya shan maganin ciwon siga, ko kuma ya sami rashin ruwa a jikinsa. Wannan zai iya faruwa ga mutum ko da bai san yana da ciwon siga ba. Sabodahaka, a nemi taimako saboda waɗannan alamomin:

Alamomi
  • Yawan jin ƙishirwa dakuma shan ruwa dayawa
  • Yawan fitsari
  • Dishashewar gani
  • Ramewa
  • Yawan jin amai dakuma yin aman
  • Ciwon ciki


Idan ba’a magance shi ba yawan sikari a cikin jini zai iya zama babban hatsari kuma zai iya sanadiyar yin dogon suma (coma) ko ma mutuwa. Zaka iya ceton rayuwar mutum ta neman taimako idan ka ga waɗannan alamomin masu hatsari.

Alamomi masu hatsari
  • Bugun zuciya da sauri
  • Numfashi mai kamshin ɗan itace
  • Bushewar fata
  • Raguwar ƙarfin bugun jini
  • Ruɗewa
  • Numfashi da sauri ciki-ciki
  • Fita daga hayyaci
Magani

A ɗauke shi nan take zuwa cibiyar lafiya. Idan yana cikin hayyacinsa, a bashi ruwa dayawa ya sha. A bashi (ruwan) kaɗan-kaɗan.

Idan ka tabbatar yana da sikari dayawa cikin jini kuma kasan yawan sinadarin insulin da yake amfani da shi to a bashi insulin kaɗan a hanyar neman taimakon. Amma idan baka da tabbas kada ka bada insulin ɗin. Bada sinadarin insulin ga mutum idan yana da ƙarancin sikari a jini zai iya kashe shi.


This page was updated:05 Jan 2024