Hesperian Health Guides

Raunuka

A wanna kashin:

  1. A tsaida zubar jinin ta hanyar matsewa.
  2. Ka wanke rauni sosai, iya iyawarka. Iya kyan wankewar iya tabbacin rashin kamuwa da cuta. Ga manyan rauni, a bada maganin rage raɗaɗi, kafin a wanke a kuma gyara raunin. Yi allurar lidocaine a kewayen raunin da kuma fatar kasa ta ciki. Ko kuma a bada wani maganin rage raɗaɗin kuma a barshi (maganin) ya fara aiki.
  3. Siturce raunin, idan kuma ƙaramin rauni ne a bashshi a buɗe ya warke.

A tsaftace kowanne rauni

Kowanne irin rauni, babba ko ƙarami zai iya kamuwa (da cuta). A tsaftace kowanne irin rauni sosai.


Wanke hannunka sosai da sabulu. Sannan ka wanke raunin da lita 1 zuwa 4 na ruwa mai kwarara. Baka da buƙatar sabulu mai kashe ƙwayoyin cuta, waɗansu sukan jirkinta warkewa. Idan raunin yana da datti, yi amfani da ruwan kumfa sannan ka ɗauraye da ruwa zalla.

Ɗaga kowacce nannaɗaɗɗiyar fata domin a wanke ƙarƙashin. Ga raunuka masu zirfi, fisa ruwa ciki da sirinji mai balan-balan, domin ruwan ya fito.

a flap of skin held up with tweezers while water is squirted on the wound.


Ko kuma cire allurar jikin sirinji sannan ka watsa ruwan dashi cikin raunin.

Ko kuma kawai zuba ruwa mai kyau akai dakuma cikin raunin.

Wanke duk wani abu daya ragu a cikin raunin, musamman datti, itace, ko kuma wani abu mai kaushi. Watakila zaka bukaci yin amfani da wani kyalle mai tsafta ko bandeji domin tsaftace raunin, sannan ka ɗauraye sosai.

Kula da raunika

Idan rauni yana warkewa, a tabatar yana cikin tsafta domin kariya daga kamuwa da cuta. Idan yayi datti, a wanki raunin da ruwa mai yawa. Lullube raunin da bandiji, ko wankakken ganyen ayaba ko kuma dan ƙyalle mai tsafta zai sa raunin yayi tsafta. Saka zuma akan raunin shima zai taimaka wajan hana kamuwa da cuta. A canja bandijin kulln, idan ya jike ko yayi tatti. Yafi ma ace babu bandiji da a saka mai datti ko jiƙaƙƙe.

A lura da alamomin kamuwa da cuta kamar ja-ja ja-ja, ƙaruwar raɗaɗi, ɗumi, kumburi, ko ɗiwa kan raunin. Idan anga kowanne daga cikin waɗannan alamomin, sai a tsaftace raunin sosai. Za’a iya buƙatar a buɗe raunin a hankali domin a tsaftace shi. A lura kada cutar ta yaɗu zuwa wasu sassan jiki.

Rufe raunika

Ƙaramin rauni yafi kyau a barshi shi kadai ya warke. Bashi da buƙatar ɗinki. Abinda yafi muhimmanci shi ne a tsaftace raunuka.

Raunin da yafi sa’a 12 sai a tsaftace shi a barshi a buɗe ya warke.

Babban raunin da ya fara haɗewa sosai zaifi warkewa da kyau idan yana rufe.

Domin rufe rauni mai tsafta marar zurfi, ayi amfani da bandeji mai surar malan-buɗe-mana-littafi, gam, ko ɗinki.

Bandeji mai surar malan-buɗe-mana-littafi

Yi amfani da bandeji mai surar malan-buɗe-mana-littafi ga ƙaramin yanka

Yadda ake yin bandeji mai surar malan-buɗe-mana-littafi.
Fatar dake zagaye da raunin dole ne ta zamo mai tsafta kuma busashshiya domin bandejin ya liƙu.

Gam

Gam (nau’in Super Glue ko Krazy Glue masu dauke da sinadarin cyanoacrylate, wani gam mai ƙarfi) yafi sauƙin amfani sama da ɗinki, kuma amfaninsu ɗaya ga yawancin raunuka. Yi amfani dashi idan ana iya ganin yadda geffan raunin guda biyu zasu iya kasancewa tare. Ba a iya aiki da shi a hannaye ko gabbai sosai saboda yawan motsin su. Kada ayi amfani da gam kusa da ido ko baki. Kuma gam zai iya sa raɗaɗi a fata.

hoton dake sama:yadda ake amfani da gam wajan rufe rauni.

Mataki na 1: A tabbatar raunin a tsaftace yake kuma fatar dake kewaye dashi a bushe take.

Mataki na 2: Jawo geffan raunin a hade su. A nesanta yatsu sosai daga raunin domin kada su maƙale a jikin gam ɗin. Wani mai taimako zai iya amfani da ‘yan tsinkaye masu tsafta domin riƙe geffan wuri guda.

Mataki na 3: Matso ruwan gam akan haɗaɗɗun geffan raunin.

Mataki na 4: Riƙe raunin har sakan 30 a rufe. Sannan a sake saka gam din. Dakata har wani sakan 30 ɗin ko sama, sannan a sake ƙarawa a karo na uku. Kowacce zubawa ya zamo ta haɗe wuri sama da ta bayan ta.

Gam zai fita da kansa. Kuma zuwa lokacin raunin ya warke.

Dinki

Za a iya jin daɗin ɗinki ne ga yanka idan bashi da zurfi kuma yana da tsaho, ko kuma idan geffan fatar dake zagaye da yankan baza su iya haɗewa dakansu ba.

Dai-daita geffan. Geffan raunin su kasance sun danye sama da fatar maimakon su shige cikin raunin.

Dai-daita zirfi dakuma tsahon ɗinkin ta kowanne ɓangare na raunin.

hoton dake sama ana nuna: yadda ake ɗinki da lanƙwasashshiyar allura.
Saka ɗinkin tacikin nan.
Ba nan ba.

Mataki na 1:
Saka ɗinkin ta cikin yankan, ba ƙarƙashinsa ba.

Idan baka da zaran ɗinki ko kuma lanƙwasashshiyar allura ta ɗinki, to sai ka wasa allurar ɗinkin (kaya). A tafasa allurar, dakuma zaran siliki ko nylon, dakuma ‘yar ƙaramar filaya ta jan zaran domin shiga cikin fatar.

an ɗauri ɗinki.


Mataki na 2:
Yi ƙulli mai ƙarfi.


Mataki na 3:

yanka da ƙullin ɗinki guda 5.

Yi ƙullinan ɗinki isasso domin so rufe yankan gaba daya.

Ayiwa rauni mai zurfi ɗinki a cikin tsoka da zaran ɗinki mai narkewa, kafin a haɗe fatar wuri ɗaya. Idan ba za a iya yi ba to kada a rufe raunini.

A bar ɗinki yayi kamar sati ɗaya (kwanaki 10 ga raunin kafa). Daga nan sai a yanke ko wanne ɗinkin a kuma zare shi. Idan ka daɗe kana ɗinkin kaya, zaka ga cewa ƙwarewar ka wajan yin ɗinkin rauni itama ta ƙaru.This page was updated:05 Jan 2024