Hesperian Health Guides

Jan wutar lantarki

A wanna kashin:

Jan wutar lantarki zai iya haifar da ƙuna ko kuma ya tsayar da zuciya.

ga mutum yana kwance akan daɓe hannunsa kuma ya taɓa waya.
A matsar da mutumin ba wayar ba domin kare kanka.
  1. A matsar da mutumin daga inda wutar lantarkin take, kuma inda babu tarin ruwa. Idan mutumin yana riƙe da wayar to yi amfani da ɗan itace domin matsar da wayar. Kada a taɓa wayar wutar lantarki kai tsaye, har sai ka tabbatar an kashe wuta.
  2. Jan wutar lantarki zai iya tsayarda numfashi. A bada numfashin ceto.
  3. Idan babu bugun zuciya yi kokarin tayar da zuciyar ta hanyar danna kirji- danna tsakiyar kirjin da ƙarfi kuma da sauri. Zai iya ɗaukar dogon lokaci. Cigaba da gwadawa.
  4. Idan mutumin yana numfashi kuma zuciyar tana bugawa, to sai a duba alamun ƙuna. Kamar harbin bindiga, yakamata a sami ƙunar shiga da ta fita.
  5. A duba wasu raunukan. Ruɗewa, lalacewar jijiyar (kai sakwanni) (wato matsalolin jin taɓi ko motsi), rashin jin sauti, ko matsalar kewayawar (jini a cikin jiki) duk zasu iya faruwa. Idan kuma mutumin ya faɗi (lokacin da wutar ta ja shi) to watakila ya sami rauni a ka, ko karaya ko zubar jini.

Idan wutar da ta ja shi marar ƙarfi ce, kuma mutumin bashi da wata alamar matsala bayan ‘yan sa’o’i to watakila babu wata matsala. Idan jan wutar na wutar lantarki mai ƙarfi ce ko walƙiya, ko kuma idan mutumin ya nuna alamar matsala, to sai a lura sosai. Ƙunar a cikin jiki tafi illa akan ƙunar kan fata inda wutar lantarkin ta shiga dakuma inda ta fita daga cikin jiki. Za’a iya buƙatar ƙarin ruwa da wasu magungunan. Zai iya ɗaukar kwanaki ko satuttuka kafin a san ainihin matsalar.


This page was updated:05 Jan 2024