Hesperian Health Guides

Matalolin sanyi dake buƙatar gaggawa

A wanna kashin:

Hypothermia (saukar zafin jiki Kasada 35°C) matsanancin sanyin jiki

Kasancewa cikin sanyi na tsahon lokaci yana da hatsari. Nan da nan zai iya jawo ruɗewa, ya kuma shafi hankali har ya sa a kasa tunanin yadda za’a ji ɗumi.

Alamomi
 • Karkarwa
 • Numfashi da-sauri-da-sauri
 • Wahalar yin furuci sosai saboda jin sanyi
 • Ruɗewa
 • Yawan yin fitsari.


Cutar jin sanyi tana kara tsananta, bugun zuciya dakuma numfashi suna daɗa yin ƙasa-ƙasa. Mutumin zai iya zama, ya daina karkarwa, a cikin ruɗu ma harma ya fara cire kayan jikinsa. Kai a karshe zai iya mutuwa.

Magani

Ayi masa busar numfashin ceto, idan da buƙatar hakan. Wanda yaji sanyi sosai zai iya farfaɗowa bayan ya dau dogon lokaci ba numfashi. Sabodahaka kana da buƙatar ka busa masa numfashin ceto na tsahon sa’a ɗaya ko ma fiye.

 • A nemi wuri mai ɗumi kuma busasshe.
 • A cire jiƙaƙƙun kaya.
 • Ayi lulluɓa da mayafi mai ɗumi busasshe. A tabbatar an rufe kai, hannaye dakuma ƙafafu.
 • A yi duk abinda za’a iya yi domin mutumin ya sami ɗumi. A lulluɓe mutumin da kaya, a gasa duwatsu sannan a nannaɗe su a kayan ko kuma ayi amfani da kwalbar ruwa mai zafi domin ɗumama mutumin. Amma ayi hankali kada a ƙona fatar.
ana wa wani wanda ya kamu da tsananin sanyi magani.
Busassun kaya, mayafi dakuma malafa
Zafin jiki (ko kuma duwatsu masu zafi, ko kuma kwalaben ruwan zafi)
Abin sha me zaƙi me ɗimi
Nannaɗaɗɗun mayafai ko kuma kwali domin kariya daga sanyin ƙasa

Idan mutumin zai iya zama ya kuma riƙe kofi, to a bashi abinsha mai ɗumi. Kada a bada abinsha mai ɗauke da giya. Duk da zaka iya jin zafi a maƙogwaronka ko ciki, abubuwa masu ɗauke da giya suna sa jiki ya rasa zafi. Har’ilayau kuma a bada abinci. Alawa dakuma abu mai zaƙi suna da taimako na musamman. A bada abincin nan take bayan haka. A ƙarawa mutumin ƙwarin gwiwa ya sha ruwa dayawa.

Idan mutumin yana fama da matsananciyar matsalar sanyi-har yasa yanayin zafin jinkinsa yakai 32° C (90°F) ko ƙasa, kuma ya zamo ya fita daga hayyacinsa bayama iya karkarwa kwata-kwata-to a bishi a hankali wurin kaishi inda za’a taimake shi.

Frostbite (daskarewar ɓangarorin jiki)

‘Yan yatsun ƙafa, na hannu, kunnuwa dakuma waɗansu ɓangarorin jiki suna iya daskarewa. A ƙarshema su mutu, su canza launi zuwa baƙi. Idan kayi gaggawa a farkon ganin alamomin daskarewar ɓangarorin jiki, to zaka iya ceto wannan ɓangarorin waɗanda idan ba haka ba sai dai a yanke su.

Alamomi

 • Sanyin fata, kamar kyandir, ɗashewa
 • Suka, dindiris ko kuma zugi
 • Ɓangaren jiki zai iya daskarewa yayi tauri


Daskarewar gaɓa me sauƙi tana canja launin fata zuwa ja. Bayan ‘yan kwanaki sai tayi saɓa. Idan ya shiga ciki sosai, sai ya bar fata mai tauri amma daga kasa da laushi. Zai iya ɗurar ruwa washegari. Idan tsokar ta daskare, to daskarewar gaɓar tayi zirfi. Kuma kewayen wurin zai yi tauri. Zai iya ɗurar ruwa ne kawai ta geffan ko kuma ma babu. Ɗurar ruwan zata iya kasancewa cike da jini.

Magani

wata mata ta naɗe hannuwa a cikin rigarta.

Fita daga cikin sanyin sannan nan-da-nan a ɗumama wurin da ya daskare. Ga ‘yan yatsu, abinda yafi sauƙi shi ne a saka hannuwan a ƙarƙashin hammata ko tsakankanin cinyoyi. Ko kuma a nannaɗe wurin da ya daskare a cikin tufa busasshiya mai ɗumi. A ajiye wurin da ya daskare a wuri ɗaya kuma kada ayi tafiya akan ƙafafun da suka daskare.

Ga cizon ƙanƙara mai zurfi, cika wani mazubi da ruwa mai ɗumi (ba mai zafi ba). Idan kana da abin auna yanayin zafi ko sanyi, to gwajin ya kai 39° C (102°F.) Tsoma ɓangaren daya daskare a cikin ruwan. Duba ruwan sosai domin kare kai daga ƙuna.

Kada ka mirza.

Wurinda ya daskare zai narke a cikin mintina 45. Lokacin da yake ɗumi zai rika zugi. A bada maganin rage zugi. Kada a sake barshi ya sake daskarewa.

Yafi a bar inda ya daskare a halin daskarewassa da a narkar da shi sannan a sake barinsa ya sake daskarewa.


Lokacin da cizon ƙanƙara yake warkewa a cikin kwanaki dakuma satikan da zasu zo, to a kula da wurin kamar yadda za’a kula da ƙuna.

tsiron Aloe vera.
Aloe vera tana taimakawa wurin warkar da cizon ƙanƙara dakuma ƙuna.


This page was updated:05 Jan 2024