Hesperian Health Guides

Numfashi

A wanna kashin:

Shaƙewa

NWTND fa Page 4-1.png

Idan mutum zai iya tari ko magana, (to) zai iya numfashi



Mutumin daya shaƙe wanda ba zai iya tari ba ko kuma bazai iya magana ba to ba zai iya numfashi ba. Zaka iya ceton rayuwar ta hanyar taimaka masa cikin hanzari.

Dake shi a baya
Ka lanƙwasar dashi ta ƙogunsa, sannan ka dake shi kamar sau 5 a tsakiyar gadon bayansa, tsakanin allunan kafaɗunsa. Yi amfani da tafin hannunka (wajan dukan).

Idan hakan bayyi amfani ba:
hoton dake sama: ana dukan baya.
Yi matsar ciki (ta wannan hanya da aka ambata a kasa)
Ka tsaya a bayan mutumin sanan ka kewaye hannayenka a kogunsa.

Saka dunƙulallun hannuwanka akan cikinsa, sama da cibiya kaɗan kuma ƙasan haƙarƙari.

Lulluɓe dunƙulallan hannunka da ɗaya hannun, sannan kayi amfani da dukkan hannayen ka ja sama da ƙarfi. Yi amfani da ƙarfi sosai har ka ɗaga mutumin daga kafafunsa. (amma kayi amfani da karfi kaɗan wajan karamin yaro). Mai-maita hakan har kamar sau biyar a jere.
hoton dake sama: yadda ake yin matsar ciki.


Idan da akwai wani abu dayake tushe iska ta shiga cikin huhuna ko maƙogwaro, to ƙarfin iskar da aka tura sosai zai fito dashi waje.

Ga mace mai-ciki ko kuma wani wanda yake da ƙiba, saka hannayenka kiwaye da tsakiyar ƙirji (saka dunƙulallen hannunka tsakanin nonowan ta). Sannan ka tura ciki.

Idan mutum ya fita daga hayyacinsa

Kwantar dashi a hankali a rigingine sannan ka duba cikin bakin. Idan zaka iya ganin abinci ko wani abu wanda yake toshe maƙogwaron, sai ka fito dashi da lanƙwasashshen ɗan yatsa. Amma kada ka tura sosai domin zai iya sa abin ya ƙara shigewa ciki. Sanna ka tura tsakiyar ƙirjinsa da ƙarfi kuma da sauri da sauri har sai ya fara numfashi.

Ga jariri ƙasa da shekara ɗaya

Idan jariri ya shaƙe kuma baya iya kuka ko tari, yi kokarin fitar da abinda ya toshe maƙogwaron ta hanyar dukan baya dakuma danna ƙirji.

Nutsewa (cikin ruwa)

A fitar da mutumin daga cikin ruwan da sauri ,kuma nan take a fara yi masa busar numfashin ceto dakuma dannar ƙirji. A fara yin busar numfashin ceto da farko domin iska ta shiga cikin jikin mutumin.

Idan mutumin yayi amai, a juya shi ta gefen jikinsa sanan a hankali kayi amfani da yatsanka ko wani ƙyalle ka goge aman domin kada ya shaƙe shi.

Busar numfashin ceto

Mutane zasu iya rayuwa ne tsahon minti 4 ba tare da numfashi ba. Zaka iya ceto rayuwar wani da busar numfashin ceto idan baya numfashi saboda shaƙewa ko kuma idan an doke shi aka ko kuma idan ya kusa mutuwa a ruwa ko kuma idan wutar lantarki ta ja shi ko kuma idan yasha wani magani sama da ƙa’ida ko kuma idan hypothermia (tsananin sanyi) ya kama shi. Idan numfashin mutum ya tsaya zaka iya ceton rayuwarsa ta yi masa busar numfashin ceto nan take.


This page was updated:10 Yun 2024