Hesperian Health Guides

Girgiza

A wanna kashin:

NWTND fa Page 10-2.png

Girgiza wani hali ne mai barazana ga rayuwa, wanda yake faruwa saboda matsanancin zubar jini, rashin ruwa, babban rauni dakuma ƙuna, alaji (tawayen jiki (allergic reaction)) ko kuma sepsis (cutar cikin jini). Irin wannan girgizar tasha banban daga girgizar abin mamaki ko ban tsoro. Jiki zai fara tsayawa, saboda rashin samun damar yin muhimman ayyuka. Alamomin girgiza suna farawa, sai kuma lamari ya daɗa lalacewa a cikin hanzari. A yi ƙoƙarin warkar da girgiza cikin hanzari domin ceto rayuwar mutum (mara lafiya).

Alamomi
  • Tsoro ko rashin nutsuwa, daga nan sai ruɗewa, rashin ƙarfin jiki da kuma fita daga hayyaci
  • Gumi mai sanyi: ɗashewa, sanyi, fata mai danshi
  • Bugun zuciya marar ƙarfi da sauri-da-sauri
  • Raguwar ƙarfin bugun jini (zuciya)
Waraka

A nemi taimako. A hanya kuma ayi waɗannan:

  • A magance abinda ya haifar da girgizar da sauri: idan zubar jini ce, yi amfani da matsa. Idan rashin ruwa ne, a bada ruwan gishiri da suga. Idan abinda ya haifar da girgizar cutar sepsis ce (wata cuta wadda take yaduwa zuwa cikin hanyar jini), to ana bukatar antibiotics nan take.
  • A bar mutumin acikin dumi (ko kuma a cire masa kaya idan yana jin zafi).
  • A daga ƙafafunsa su tallafi gwiwowin.
  • Idan zai iya riƙi moɗa, a bashi wani abu mai ruwa ko ruwan gishiri da suga.
  • A nutsu a kuma ƙara masa ƙwarin gwiwa.
  • A bada ruwan dubura ko IV fluid (duba Ayyukan ma’aikacin lafiya-ana kan aikinsa) akan hanyar neman taimakon likita.


NWTND fa Page 11-1.png


This page was updated:05 Jan 2024