Hesperian Health Guides
Raunin ƙirji dakuma karayar haƙarkari
Kundin bayanan lafiya na Healthwiki > Sabon littafin A inda babu likita > Taimakon farko > Raunin ƙirji dakuma karayar haƙarkari
Raunin faɗuwa ko buguwa zai iya haifar da karayar ƙasusun haƙarƙari dayawa a lokaci ɗaya. |
Laushi idan an taɓa, ko kuma zugi mai tsanani dakuma haki ko tari bayan an sami rauni a ƙirji zai iya zamowa alamar karyayyen ƙashin haƙarƙari. Taɓa ƙashin da ‘yan yatsunka. Idan akwai wurin dake loɓawa ƙarƙashin fata, ko kuma inda ya faɗa kuma yana da laushi, to akwai karaya. Idan ƙashi ɗaya ne ya karye kuma bai turo ciki ko waje ba, to a bada maganin zogi. Sai mutumiɗɗn ya guji ɗagawa ko kuma aikin ƙarfi na ‘yan satittika. Zai warke ba tare da kulawa ta musamman ba. A tunawa mutumin ya rika jan dogon numfashi duk bayan ‘yan sa’o’i. Akwai zafi, amma zai sa huhunan sa su cigaba da aiki.
Karayar ƙasusuwan haƙarƙari masu yawa
- A manna auduga mai kauri, ko nannaɗaɗɗen ƙyalle akan ƙasusuwan haƙarƙarin da suka karye.
- A kwantar da mutumin a kowanne irin yanayi da zaifi taimaka masa yayi numfashi.
- A lura da alamomin girgiza kuma a nemi taimako.
Raunukan ƙirji masu zurfi
Harbin bindiga, suka, fashewa, ko kuma ƙashin haƙarƙarin daya sami muguwar karaya zai iya sa iska ta riƙa shiga ko fita ta huhuna.
- Nan take a rufe kofar da wani abu da baya barin iska ta shiga ko fita, kamar bandeji wanda aka jika shi da basilin, nannaɗaɗɗiyar jakar leda, ko ɓawon ayaba.
- A leƙe gefe 3 domin iska ta riƙa fita amma ba shiga ba.
- A kwantar da mutumin a kowanne irin yanayi da zaifi taimaka masa yayi numfashi. Nemi taimako.