Hesperian Health Guides
Ciwuka dakuma raunukan ciki
Kundin bayanan lafiya na Healthwiki > Sabon littafin A inda babu likita > Taimakon farko > Ciwuka dakuma raunukan ciki
Alamomi masu hatsari
- Matsanancin ciwo.
- Ruɗewa.
- Taurin ciki kamar katako, ko kuma yana ƙara girma.
- Alamomin rashin jini wato: suma, ɗashewa, saurin bugun zuciya.
Ga kowanne daga cikin waɗannan alamomin, ayi maganin girgiza kuma a nemi taimako. Kada a bada abinci ko abinsha. Duba Ciwon ciki, gudawa, dakuma tsutsotsi (ana kan aikin) domin ƙarin bayani kan Cututtukan ciki masu buƙatar gaggawa.
![ga rauni dawani ɓangare na hanji ya fito ta cikinsa.](https://pool.hesperian.org/w/images/thumb/8/80/NWTND_fa_Page_26-1.png/200px-NWTND_fa_Page_26-1.png)
Wani abu daya cake a cikin jiki
Ga wani abu daya cake a cikin ciki, yafi kyau a barshi a nemi taimako. Koda kuwa taimakon za’a same shi nan da kwanaki, kada a cire abin. A daure shi a jiki da bandaji ko kyalle.
![a man bleeding from a wound caused by a stick in his abdomen.](https://pool.hesperian.org/w/images/thumb/f/fb/NWTND_fa_Page_26-2.png/350px-NWTND_fa_Page_26-2.png)