Hesperian Health Guides

Gajeran suma dakuma jijjigaa

A wanna kashin:

Gajeran suma shine fita daga hayyaci ko kuma canjin tunani na ɗan taƙaitaccen lokaci, dakuma yin ‘yan fizge-fizge.

Gajeren suma zai iya faruwa a sanadiyar zazzaɓi mai zafi, rashin ruwa a jiki, rauni, zazzaɓin cizon sauro, cin guba ko kuma waɗansu dalilan. Gajeren suman da yake yawan faruwa shi ake kira da farfaeɗiya — duba Matsalolin kai dakuma ƙwaƙwalwa (ana kan aikinsa). Idan ɗaya daga cikin waɗannan bai zamo dalilin yin gajeren suma ba, to yin gajeran suma sau ɗaya ba wata matsala bace babba (duk da abu ne mai ban tsoron gani). Idan gajeren suma ya sake faruwa, to aga ma’aikacin lafiya.

Magani

Lokacin da wani yayi gajeren suma, to a tsaftace inda yake domin kada ya cutar da kansa. A juya shi ta gefen jikinsa domin kada ya ƙware idan yayi amai. Kada a yi ƙoƙarin riƙe mai gajeren suma a kasa ko kuma ayi ƙoƙarin riƙe harshensa.

Idan gajeren suma ya faru saboda rashin-ruwa, to a nemi taimakon likita. Bayan ya farfado daga gajeren suman sai a bashi ruwan-gishir-da-siga (ana kan aikinsa).

Idan gajeren suma ya faru saboda cutar sanƙarau (ana kan aikinsa), to a nemi taimakon likita.

Idan gajeran suma ya faru saboda zazzaɓin malaria, to a nemi taimakon likita. A kan hanya a bada diazepam. Sannan a bada magungunan (zazzabin cizon sauro duba Magungunan: Waɗansu daga cikin ucuttuka masu yaɗuwa –ana kan aikinsa).

Idan gajeren-suma ya wuce minti 15, a saka diazepam na ruwa a cikin dubura ta amfani da sirinji ba tare da alluraba. Duba Bayani akan adadin magunguna. Kada a bada sama da ka’idar da aka kayyade kuma kada a bada sama da sau 2

Sassanƙarewar da ake yi sanadiyar cutar tetanus za’a iya zaton gajeren suma ne. Muƙamuƙai su kulle gam, sannan jiki ya lanƙwashe baya. A koyi yadda ake gane alamomin cutar tetanus.

Bayan gajeren-suma, mutum zai iya kasancewa cikin ruɗu ko kamar me jin bacci. Sabodahaka, a kwantar masa da hankali.

NWTND fa Page 50-1.png


This page was updated:05 Jan 2024