Hesperian Health Guides
Harbi da cizo
Kundin bayanan lafiya na Healthwiki > Sabon littafin A inda babu likita > Taimakon farko > Harbi da cizo
Kada a yanka ko a buɗe wurin harbi ko cizo domin a zuƙe dafin. Har’ilayau kuma ɗaure wurin da ƙarfi ba zai tsaida yaɗuwar dafin harbin ko cizon ba, sai dai ma ya haifar da babbar matsala.
Mafiyawancin harbi da cizo suna da zafi amma basu da hatsari, kuma koda halittu masu hatsari ba kasafai suke sakawa mutum dafin da zai kashe shi ba. Abin da zaka yi shi ne ka kasance cikin nutsuwa kuma ka lura da inda aka harba ko ciza. Idan babu waɗansu matsaloli ko kuma idan aka fara samun sauƙin matsalolin bayan ‘yan sa’o’i (wannan ya danganta da halittar datayi harbin ko cizon), to akwai damar babu wani abin damuwa. Amma, saboda ƙanƙantar yara, dafin na iya yimusu illa kuma ya cutar dasu sosai. Sabodahaka, sun fi buƙatar kulawa.
Kanun bayannai
Saran Maciji
- Nesanta kanka daga wajen macijin. Waɗansu macizan na iya yin sara bayan ‘yan mintina koda kuwa sun mutu.
- A cire kayan ado (yari) ko tufafi dake kusa da gurbin harbin/cizon, saboda jiki zai iya kumbura.
- A karkatar da gurbin harbin/saran ya zamo ƙasa da zuciya. Kuma a tabbatar da gurbin a wuri guda tayin amfani da itatuwa ko maƙale.
- A tsaftace raunin a hankali. Kada a mulmula.
- Ga mafiyawancin macizai ko kuma idan baka san nau’in su ba sai a jira, a kuma lura na ‘yan sa’o’i. Idan akwai ɗan kumburi ko kuma babu zugi ko jaja-jaja to babu matsala. Alamomi masu hatsari sun haɗa da kumburi sosai ko zogi, ko gani garara-garara, ko rufewar idanu, ko jiri, ko kasala, ko jin amai, ko zubar jini daga baki ko hanci.
Kuma a saka mutum ya guntsi ruwa cikin bakinsa ya kuma fesar da ruwan cikin wani mazibi mai hasken launi. Idan ruwan daya fesar launinsa ya koma ruwan-bila ko kuma jini-jini, to dadashin yana fitar da jini. Wannan alamace ta hatsari.
Idan wadannan macizan sun yi sara, to a nannaɗe gurbin da ƙarfi.:
- Macizan kwazazzaban teku
- Mamba
- Macizai masu kada jelarsu na ƙasashen Kudancin America
- Macizan cikin teku
- Mafiyawancin gamsheƙa-irin waɗanda ke illata dukkan jiki.
A naɗe sosoi-domin dakatar da yaɗuwar dafin, amma kada ya zama sosai ta yadda zai dakatar da gudanar jini gaba ɗaya. A taɓa domin jin bugawar gudun jini a ƙarƙashin naɗin da akayi wa ƙafar. | ||
Ayi amfani da itace domin hana gaɓar motsi. |
Mafiyawancin viper dakuma waɗansu daga cikin gamsheƙa suna illata kewayen da suka sara ne basa yin illa ga sauran jiki. Ga irin wadannan macizan kada a nannaɗe gurbin saran.
Akwai maganin dafin mafiyawancin macizai masu guba da ka iya taimakawa. Idan ka sami cibiyar lafiya yi musu bayanin nau’in macijin iya yadda zaka iya domin su yi amfani da maganin dafin da ya dace. Idan da hali cika akwatin magungunan ka da magungunan dafin macizan da ake samu a kewayen ku kafin bukatarsu ta taso.
Domin gamsheka mai fesa dafi cikin ido: zuba ruwa mai yawa. Idan babu ruwa, madara ko giya zasu yi amfani. Kada ayi amfani da sinadarai masu ƙarfi da raɗaɗi.
Mesa da boas basu da dafi, amma saransu zai iya haifar da matsanantan cututtukan fata. A lura da raunin, kuma idan da akwai alamomin kamuwa da cuta kamar-jaja-jaja, zafi, kumburi, ko ɗiwa (ruwan ciwo), to ayi magani kamar yadda akewa rauni mai cuta. Wani lokacin waɗannan macizan sukan haifar da rauni saboda matsar da sukayi wa mutum.
Idan gurbin saran ya nuna alamar haƙora, to macijin yana da dafi. Amma idan babu alamar haƙora, to ba dole bane macijin ya zamo mai dafi, amma zai iya kasancewa.
Giza-gizai da Kunami
Duk da cewa cizon su yana da zafi sosai, yawancin cizon gizo-gizo dakuma harbin kunama basa haifar da wata cuta babba ko mai ɗaukan lokaci. Tabbatar da gurbin a wuri guda sannan ayi amfani da ƙanƙara ko ruwan sanyi domin rage zugin. Kada a yanka domin buɗe gurbin ko kuma ayi amfani da abin tsaida jini ko bandagi. Amfani da zafi baya taimakawa, amma tabbata a wuri guda yana taimakawa.
Idan kasan gizo-gizon ko kunamar nau’i ne masu hatsari, ko kuma bayan cizon ko harbin akwai alamar matsaloli kamar; ciwon ciki, ƙaiƙayi, gumi dakuma wahalar yin numfashi, to sai a nemi taimakon likita. Watakila akwai maganin dafin.
Ga cizon nau’in gizo-gizon da ake kira da Black Widow ko kuma harbin kunama, zaka iya bada diazepam akan hanyar (neman taimako), domin hana matsalar tsokar jiki kuma sai a kwantar da mutumin hankali.
Kudan zuma da rina
Bayan harbin a duba a ga ko abin harbin yana maƙale a jikin fata kuma a cire shi nan-da-nan. Gurbin harbin zai iya yin ja, ya kumbura kuma yana zafi. Saka kwabin hodar biredi da ruwa ko kuma wani abu mai sanyi a gurbin zai taimaka wurin rage kumburin dakuma zugin.
Ba kasafai akesamun matsanancin alaji ba a dalilin harbin zuma kona rina, amma zasu iya kasancewa masu hatsari. Duba bayani akan alamomi dakuma maganin alaji me tsanani.
Kaskoki
Kaskoki zasu iya yaɗa cututtuka dayawa idan suka cije ka. Domin ƙarin bayani akan kaskoki da kuma yadda ake cire su cikin sauƙi duba, sashi akan sashi akan Fata (ana kan aikinsa).
Kifaye
A nesanta kai daga nau’in kifi me fitar da wani ruwa mai yauki, a kuma cire duk tantanin da ya maƙale a jiki. Ayi amfani da ruwan teku domin wanke wurin. Ga nau’in kifi me harbi kuma, a cire kayar da basilla ko filaya.
A kuma saka gaɓar a cikin ruwan zafi na tsahon mintina 20 domin samin sauƙin zugin,amma a tabbatar baya tsananin zafi. Wannan zai fi amfani ga cizon kifi mai harbi fiye da mai fitar da ruwa me yauƙi.
A kwai hanyoyin waraka na gargagajiya dayawa, amma basa aiki ga dukkan kifaye ko kuma kifi mai fitar da ruwa mai yauki. Misali harbin nau’in kifin da ake kira da box jellyfish (sea wasp) wato rinar teku, idan an wanke wurin da ruwan khal yana taimakawa. Amma ruwan khal yakan saka harbin waɗansu kifayen masu fitar da ruwa mai yauki ya ta’azzar. Papaya ko meat tenderizer sanannin magani ne na harbin kifi mai fitar da ruwa mai yauki, amma baya aiki ga harbin kowanne kifi me fitar da yauki, kuma wani lokacin ma yakan sa zugin ya ƙaru.
A bar mutumin (da kifin ya harba) ya motsa gabobin-Saɓanin saran maciji ko cizon gizo-gizo, rashin motsin gaɓa baya taimakawa. A nemi taimako idan akwai matsalar yin numfashi ko kuma wasu alamomin suka ta’azzara.