Hesperian Health Guides
Matsalolin hankali dake buƙatar kulawa cikin hanzari
Kundin bayanan lafiya na Healthwiki > Sabon littafin A inda babu likita > Taimakon farko > Matsalolin hankali dake buƙatar kulawa cikin hanzari
Idan tunanin mutum yana raya masa ya cutar da kansa ko wani, to wannan ya zama harkar gaggawa, saboda haka yana bukatar taimako cikin gaggawa. Kamar yadda yake ga duk harkar gaggawa (ta lafiya) da farko sai a fara duba numfashi, a tsaida zubar jini, sannan a duba waɗansu raunukan na zahiri. Kwantar wa da mutumin da ke da matsalar da ta shafi tunani hankali zai iya ceto rayuwarsu.
Idan wani yace zai cutar da kansa ko waɗansu, to ku yarda da shi.
Idan mutum ya zamo hatsari ga sauran jama’a, to zai fi sauki a nesanta mutane da shi maimakon a nisanta shi da su. Za ka iya buƙatar taimako wajan kubutar da shi dakuma kewayen da yake. Kuma kaima ka nemi hanyar kare kanka.
Duk wanda yace yana so ya cutar ko kashe kansa, abinda yake so da farko shi ne wanda zai saurare shi a cikin nutsuwa. Ayi masa nutsatstsun tambayoyi, domin nuna masa an damu da shi kuma an fahimce shi. Tambayoyinka za su iya taimakawa wajan daƙile tunaninsa, kuma su kautar da shi daga abinda ya ƙudere.
- A tambaya ko yana shirin cutar da kansa ko wani, ko kuma ma ya aiwatar.
- A tambaya yaya ya tsara yin hakan, kuma yanada halin yin hakan. Iya kyawun tsarin (nasa) iya girman matsalar.
- Ka nemi mutumin da yayi alƙawarin cewa ba zai cutar da kansa ba ko waɗansu. Kuma a kauda duk wata hanya da zai iya amfani da ita wurin cutar da kan nasa ko wasu.
Ka yarda yau baza ka cutar da kanka ba?
Amma yau kaɗai. |
To zaka bani bindigar ka na ajiyeta — yau kaɗai? |
Irin waɗannan alƙawuran zasu iya dai-daita mutum na tsahon lokacin da za a sami taimako mai ɗorewa. Kada a barshi shi kaɗai. A zauna tare da shi, ko kuma a sa wani daga cikin yan uwa ko abokai su zauna tare da shi. A tabbatar yana cikin hayyacinsa kuma kada yasha giya ko ƙwayoyi. Giya ko ƙwayoyi zasu iya dagula masa tunani, kuma su daɗa tunzirashi wurin cutar da kansa. Kuma zai taimaka a nemi taimakon shugabannin addini ko na al’umma waɗanda yake girmamawa. Bibiyarsa domin ganin yana samun tallafi zai nuna masa cewa ka damu da shi, kuma yana da muhimmanci. A duba sashin Lafiya tunani (ana kan aikinsa) domin ƙarin bayani kan yadda za’a cigaba da tallafawa (masu irin wannan matsalar.)
Tambayar mutum ko yana so ya kashe kansa baya tunzira shi yayi hakan.