Hesperian Health Guides

Zubar jini

A wanna kashin:

Matsa

Matsa da karfi tana iya tsayar da kusan kowacce irin zubar jini, ko da babban rauni mai ƙwararar da jini. Ko da mutum yana zubar da jini ne daga kai, to a matse wurin.
  1. A ɗaga ɓangaren dake zubar da jinin ya zamo sama da zuciyar mutumin (da ke zubar jinin).
  2. Sami ƙyalle mai tsafta dake kusa da kai, ninka shi kamar girman raunin, sannan ka danna shi da karfi akan raunin kai tsaye. Nunawa wanda yaji raunin shima yadda zai iya matse (wurin dayaji raunin), idan har zai iya. Idan raunin yana da girma saka bandejin ko ƙyallen cikin sa. Cigaba da matsewa har sai jinin ya tsaya. Kada a cire ƙyalle idan ya jiki da jini. Mai makon haka, a kara wani kyallen a sama. Ga babban rauni, kada ka ɗaga hannuka har tsahun mintina 15 aƙalla, ko da kuwa dan aga ko jinin ya tsaya.


NWTND fa Page 8-1.png


Idan fitar jinin ya ragu ko kuma ya tsaya, to za’a iya samun damar ɗaura wani ƙyallen da ƙarfi a kewayen inda yake zubar da jinin. A saka nannaɗaɗɗan bandeji ko ƙyalle a cikin ko kuma kan raunin sannan a saki daɗa nannaɗewa da bandeji. A tabbatar bandejin ya ɗauru sosai ta yadda zai iya matse raunin, amma ba sosai ba ta yadda zai hana gudanar jini zuwa sauran (bangarorin) hannun ko ƙafar.

Matse (rauni) domin tsaida jini aiki ne mai wahala. Kada ka gaza!


Kada ayi amfani da datti, kalanzir, lemon tsami, ko kofi (na sha) nikakke domin tsaida jini. Jini kan iya ɓata wuri sosai tayadda sai ka ga kamar mutum ya zubadda jinin sama da yadda ya faru (a zahiri). Amma a lura da mutumin (daya zubar da jinin) sosai domin ganin alamun zubar da jini mai yawa, kamar haka:

Alamomi masu hatsari
  • Ruɗewa ko fita daga hayyaci
  • bugun zuciya da sauri
  • Sanyi, danshi dakuma ɗashewar fata


Idan kaga waɗannan alamomin, sai ka daga kafafun mutumin sama kan wani abu domin so zamo sama da zuciyar (sa), sannan ka nemi taimakon (matsalar) girgiza.

Koda baka ga waɗannan alamomin ba, to ka kasance tare da mutumin ko kuma ka riƙa duba shi duk minti 10 zuwa 15, domin tabbatarwa yana lafiya kuma ka ƙara masa ƙwarin gwiwa. Ka cigaba da dubawa har sai ya fara harka kuma ya fara jin dai-dai.

Ɗaurin tsaida zubar jini

Yi amfani da ɗaurin tsaida zubar jini a matsayin mataki na karshe, idan ana ganin babu yadda za’a yi sai an rasa hannu ko ƙafa wajan ceton ran mutumin.

Yi amfani da ɗaurin tsaida zubar jini idan:

  • Gaɓa ta yanke ko kuma tayi lalacewar da baza a iya kuɓutarda ita ba.
  • Zubar jinin da baya ƙaƙƙautawa daga hannu ko ƙafa, duk da matsewa da ƙarfi. (An gwada matsewa da ƙarfi tun farko?)
  • Akwai babban rauni, mai zirfi a cinya, kamar idan harsashi, birbishin bam ko wani abu wanda ya shiga can cikin tsoka, kuma mutumin yana nuna alamon rashin jini, kamar rashin ƙarfin jiki, ruɗewa ko ɗashewar fata. (Yakanyi wahala a iya matse ƙatuwar cinya sosai domin tsaida zubar jini.)


Yi amfani da maɗaurin wando mai faɗi, ko wani ƙyalle wanda aka nikkashi ya zamo maɗauri mai faɗi, ko abin ɗaurawa na ma’aunin gwajin hawan jini wanda aka hura masa iska, domin ɗaure inda yake zubar da jinin. Kada ayi amfani da igiya ko waya siririya. Zata iya yanka fata.

Atafi asibiti da sauri. Kana da sa’a 2 ko 3 kafin (mai raunin) ya rasa gaɓa.

Mataki na 1:
A saka abin ɗaurin tsaida zubar jinin daga sama amma kusa da raunin, tsakanin raunin da (sauran) jiki. (Wani kuskuri da ake yawan yi shi ne saka abin ɗaurin tsaida zubar jinin can nisa da raunin.)

Mataki na 2:
Daura abin ɗaurin tsaida zubar jinin kewaye da gabar ninki biyu. Sannan kayi kulli.

Mataki na 3:
Saka ɗan itace gajere mai ƙarfi a saman kullin. Ɗaura wasu ƙullina guda biyu a saman icen.

Mataki na 4:
Murda itacen domin ɗaure abin tsaida zubar jinin har sai jini ya tsaya.

Mataki na 5:
Ɗaure itacen a wurin da wani ƙyallen.
NWTND fa Page 10-1.pngThis page was updated:05 Jan 2024