Hesperian Health Guides

Alaji (sauyin dake faruwa ga jiki saboda canjin yanayi da jiki baya so): Me sauƙi ko me tsanani

A wanna kashin:

Alaji me sauki na faruwane sanadiyar ƙura, garin jikin fure, cizon ƙwari ko kuma waɗansu nau’uka na abinci, ko sinadarai ko magunguna. Irin waɗannan ana yin maganinsu ta amfani da antihistamines.

Alamomi na alaji me sauƙi
Mutum me ɗauke da alaji me sauƙi.
Kumburarrun idanuwa jajaye masu ƙaiƙayi
Ƙuraje ko kuma jaja-jaja
Atishawa
kumburarrun guraben cizo dayawa a ƙafar wani mutum.
idan akwai cizon ƙwaro to wurin zai iya kumbura

Alaji me tsanani yafi hatsari sosai kuma zai iya tsaida numfashin mutum a cikin hanzari.

Alamomin alaji me tsanani (anaphlaxis)

  • Jaja-jaja, ƙaiƙayi ko ƙurji.
  • Kumburin leɓe,b aki ko maƙogwaro, wahalar haɗiya.
  • Wahalar numfashi.
  • Kumbirin hannaye ko ƙafafu.
  • Jin amai ko ciwon ciki.


Gama-garin alamomin sune ƙuraje da matsalar numfashi.

Idan mutumin ba zai iya haɗiya ba, ko kuma yana da matsalar numfashi, to a bashi epinephrine nan take. Ayi allurar mg 0.3 zuwa 0.5. Zaka iya mai-maitawa adadin bayan mintina 5 idan ya zama dole.

Epinephrine yana zuwa ƙarfi daban-daban, kuma za’a iya buƙatar adadi daban-daban domin bayarwa a kowanne sha. Sabodahaka, adadin da yakamata a bayar yakamata ya zamo a cikin akwatin magani domin saboda shirin ko-ta-kwana. Ko kuma a ɗura maganin a cikin allura a ajiye, wannan shi ake kira da EpiPen ko kuma wani sunan.

Ayi allurar epinephrine a tsokar cinya, kamar haka:

Kibiya tana nuni da cinyar wata mata ,wadda ƙafafunta suke kan tarin matasan kai.
A ɗage kafafu suye sama da zuciya

Domin matsalolin numfashi, zaka iya bada salbutamol. Kuma yana da kyau a bada antihistamine.

Sau dayawa, idan har ka taɓa samun matsalar alaji saboda wani magani, ko abinci, ko harbin zuma ko kuma wani abin daban to ka guje shi har abada. Idan alaji ya sake faruwa akanka to zai iya jawo maka matsananciyar matsalar da tafi ta da.


This page was updated:05 Jan 2024