Hesperian Health Guides
Ciwon zuciya
Kundin bayanan lafiya na Healthwiki > Sabon littafin A inda babu likita > Taimakon farko > Ciwon zuciya
Alamomi
- Dannewa, matsewa, ɗaurewa, ƙuna, zugi a cikin kirji.
- Zogin zai iya yaɗuwa har zuwa wuya, kafaɗa, hannaye, haƙora ko muƙamuƙai.
- Zogin yakan zo a hankali, wani lokacin ma yakan zo kwatsam kuma da tsanani.
- Ƙarancin numfashi
- Gumi
- Jin amai
- Jin jiri
Ciwon kirji shi ne mafi gama-garin alama a wurin maza da mata, amma saudayawa mata basu fiya jin ciwon ƙirji ba. Mai makon haka sai su rika jin ƙarancin numfashi, gajiya, jin amai, amai ko kuma ciwon baya ko muƙamuƙi.
Magani
A bada ƙwayar aspirin 1 nan take. A umarci mutumin ya taune ta ya haɗiye da ruwa. Ko da baka da tabbas ko mutumin yana da ciwon zuciya aspirin ba zai yi illa ba.
Idan da akwai ka bada nitroglycerine a saka a ƙarƙashin harshe har ya narke. Morphine yana taimakawa wajan maganin zogi dakuma tsoro. Kwantarwa da mutumin da hankali kuma a nemi taimako.