Hesperian Health Guides

Karayar ƙasusuwa, targaɗe dakuma kumburin gaɓa

A wanna kashin:

Daga farko a fara tabbatarwa karaya ce ko targaɗe (fitar gaɓa daga wurinta) ko kuma buguwar tsoka ce. Yana da wahala a iya banbance ɗaya daga cikin waɗannan abubuwan, sabodahaka, wataƙila hoton (x-ray) ya zama dole domin tabbatarwa. Idan bazaka iya tan-tance karaya ko targaɗe ko buguwar gaɓa ba, to sai a bar gaɓar a kuma nemi taimako. Kuma zai iya yiwuwa a sami haɗin waɗannan raunuka.

A bada maganin rage zogi irinsu acetaminophen ko ibuprofen domin sauƙaƙa raɗaɗin

karyayyan hannu.
Karaya

Karkacewa a tsakiyar ƙashi ko kuma zogi a wani wuri a jikin ƙashin, wanda ke ɗan yin zafi ko kuma ma babu zafin idan an barshi shi kaɗai. Wani lokacin ƙashi zai iya karyewa ba tare da karkacewa ba. Hoton x-ray zai iya tabbatar maka idan da akwai karaya.
Kafaɗa me targaɗe.
Targaɗe

Kumburi a kan gaɓa ko kuma rashin iya motsa gaɓa.
kumburin gaɓar tsintsiyar hannu.
Kumburin gaɓa

Kumburi dakuma zogi kusa da gaɓa.

Karayar ƙasusuwa

A bar ƙashin da ya karye a wuri guda har sai wanda ya iya gyaran karaya ya zo ya gyara sannan a saka filasta. Domin a taimaka wajan tsaida shi (ƙashin), a yi maratayi da nannaɗaɗɗiyar takardar kwali ko katako mai faɗi ko ganyen bishiyar kwakwa mai ƙarfi ko kuma wani abun miƙaƙƙe mai ƙarfi.

Yadda akeyin ɗaurin karaya

Mataki na 1:
A tsaida hannun a yadda yakamata ya tsaya. A ɗan lanƙwasa gwiwar.
NWTND fa Page 29-1.png
Mataki na 2:
A nannaɗa bandiji naɗi ɗaya ko kuma wani ƙyalle marar kauri ko kuma a yi amfani da hannun riga.
NWTND fa Page 29-2.png
Mataki na 3: A kwantar da hannun a kan katakon ɗaurin. A saka nannaɗaɗɗen ƙyalle a cikin tafin hannun. Idan ƙafa ce sai ayi ɗaurin ta gefe.
NWTND fa Page 29-3.png
Mataki na 4: A nannaɗe katakon ɗaurin da bandiji ko tsagin wani ƙyalle domin a ɗaure shi a wuri guda.
NWTND fa Page 29-4.png

A bar yatsun hannu dana ƙafa a buɗe, kuma a riƙa yawan dubawa domin a tambatar suna da ɗumi kuma suna nan kamar yadda ya kamata.

NWTND fa Page 29-5.png
A ɗaure karyayyen ƙashin cinya tun daga kan cinya har zuwa idan sawu.
NWTND fa Page 29-6.png
A ɗaure dan yatsan hannu ko na ƙafa tare da nakusa da shi. A saka ɗan wani abu mai laushi a tsakaninsu.

Yadda ake yin maratayi

Za a iya amfani da maratayi domin tallafa dakuma kare hannu mai rauni ko kafaɗa.

a maida ƙyalle mai kusurwa huɗu zuwa kusurwa uku;a kwantar da hannun akan nannaɗaɗɗen ƙyallen.
A tallafi
gwiwar
hannun.
A ƙulle a
bayan wuya

Dai-daita ƙashi

A bari kumburi ya saɓe kafin a dai-daita ƙashi.

Idan ƙashi ya fita daga wurinsa na ainahi, dai-dai ta shi zai taimaka masa ya warke. Amma idan baka san yadda ake dai-daita ƙashi dai-dai ba, zaka iya haifar da ɓarna mai yawa idan kayi ba dai-dai ba. In dai zai yiwu wanda ya ƙware shi ne zai dai-daita ƙashi. Al’ummu dayawa suna da ƙwararrun masu dai-daita ƙashi ko kuma ma’aikatan lafiya na al’umma wanda suka san yadda akeyi sosai.

Mataki na 1:
Da farko a bada maganin rage zugi. Za a iya kuma bada maganin rage damuwa kamar lorazepam ko diazepam domin mutumin ya sami nutsuwa.

Mataki na 2:
A sami mataimaki ya riƙe shi kyam, ko kuma a ɗaure ɓangaren jikin da za ayi wa ɗorin a jikin wani abu da baya motsi.

hoton dake kasa: ana jan karyayyen hannu.

Mataki na 3:
Aja ɓangaren dake nesa da ƙarfi amma a hankali. Kada a fizga, amma aja da ƙarfi sosai ta yadda ƙasusuwan zasu rabu.

hoton dake kasa: ana dai-daita ƙasusuwa.

Mataki na 4:
Idan ƙasusuwan sun rabu, sai a dai-daita geffan su guda biyu a hankali sannan a barsu su hade wuri guda.

Kada ayi kokarin dai-daita ƙashi idan karayar ta haɗa da gaɓa ko kuma akwai alamun samun sama da karaya ɗaya, wadda zata bar wani ƙashin a tsakiya yana yawo. Kada a fizgi ƙasusuwa ko kuma a takura waɗansu ƙasusuwa su shiga wani wuri. Wannan zai iya haifar da illa ta din-din-din. A nemi taimako.

Yadda ake yin filasta

Za’a iya yin filasta daga ‘yan gutsatstsarin ƙyallaye da kuma gam ko kuma filasta wadda take bushewa tayi tauri.

A ƙasar Mexico, ana amfani da tsire-tsire nau’i-nau’i kamar su tepeguaje (bishiya ce dangin wake) dakuma bishiyar solda con, solda (wani tsiro ne mai hawa kan katuwar bishiyar arum lily) domin yin filasta. A ƙasar India kuma, masu ɗorin karaya na gargajiya sunayin filasta da farin ruwan cikin kwai dakuma wadansu tsire-tsire. Hanyoyin sunyi kama da juna. Kowanne tsiro zai iya yin filasta matuƙar zai iya samar da ruwa-ruwa mai kauri da yauƙi kamar gam, wanda idan ya bushe zai yi ƙarfi, kuma ba zai cutar da fata ba. Sau dayawa akan tafasa tsiron ne acikin ruwa har sai ya samar da ruwa mai kauri da yauƙi. Ko kuma ayi amfani da garin filasta na bature a haɗa shi ruwa.

A bari har sai kumburi ya saɓe kafin ayi filasta. Wannan zai iya ɗaukan sati. Kafin nan, sai a tallafi gaɓar da ɗauri dakuma rataye.

Mataki na 1:
A tabbatar kasusuwan sun dai-daita. A danganta ɓangare mai rauni da marar rauni domin a tabbatar duk suna kama da juna, kuma in an taba su aji dai-dai suke.

Gwiwar hannu a karkace, baban ɗan yatsan hannu ya kalli sama, sannan ‘yan yatsun hannu sun ɗan tanƙwari, kamar ana riƙe da kufi.
NWTND fa Page 31-1.png
Gwiwar ƙafa ta ɗan tankwara. Idan sawu ya tanƙwara kamar mutumin yana tsaye.
NWTND fa Page 31-2.png


Mataki na 2:
A sanya gaɓa a irin wannan yanayin:


Mataki na 3:
A nannaɗe wurin da ake san ayiwa filasta acikin sakakken ƙyalle marar kauri ko ɗan nannaɗen abin ɗauri mai raga-raga. A haɗa da gaɓar da take a sama da kuma ƙasa da wurin da karaya take.


Mataki na 4:
Sannan a nannaɗa audiga mai laushi. A ƙara ninka naɗin a wuri mai ƙashi, amma kada a nannaɗe dayawa, musamman ma wurin da ya karye.


Mataki na 5:
A tsoma ƙyalle mai tsafta ko bandeji acikin ruwan ko filastar.


NWTND fa Page 31-3.png

Mataki na 6:
Ayi filastar a duk kewayen ta amfani da sala-salar bandijin. A bar ‘yan yatsun hannu da babban dan yatsa a buɗe. Ayi filastar dai-dai kar ta matse sosai.

NWTND fa Page 31-4.png
hoton dake ƙasa: ana nannaɗe naɗin ciki na kan filastar.


Mataki na 7:
Lallausa naɗin ciki na gefen filastar, kamar haka:

Bayan an gama filastar, a kwantar da gaɓar kuma a ɗan ɗaga ta kaɗan duk sanda za’a iya. Ayi amfani da sanduna domin kare karyayyar kafa daga nauyi.

A kowanne irin lokaci bayan anyi filasta, idan aka ga ‘yan yatsun hannu ko na ƙafa sun fara kumburi,k o kuma suna ƙara zugi, ko sunyi ja, ko ɗashewa, ko ruwan bula, ko rashin ji idan an taɓa, to a cire filastar nan-da-nan. Rashin cire filasta wadda ta matse sosai zai iya sa mutum ya rasa gaɓa.

Wane tsahon lokaci ne karyayyen kashi yake ɗauka kafin ya warke? Yaro yana warkewa a ‘yan satuttuka. Kashin tsoho yana ɗaukar watanni, kuma ba dole ne ya warke yadda ake so ba. A bar filasta a jiki har akalla wata ɗaya. Filastar kafa a barta har zuwa wata 2.

Domin cire filasta, a tsoma ta a ruwa sannan a yanke ta a hankali. Bayan an cire filasta, a yi hankali wurin amfani da gabar har kwatankwacin tsahon lokacin da tayi tana cikin filasta. Sannan a hankali a cigaba da amfanin da aka saba da ita, kamar ɗorawa ƙafa mai rauni nauyi.

Ƙashin da ya karye ya fito wajen fata (budaddiyar karaya)


NWTND fa Page 32-1.png

Buɗaɗɗun karaya sun fi damar kamuwa da cuta. A wanke raunin sosai da ruwa mai gudana dayawa har tsahon minti 5 ko sama da haka. A ɗauri gabar, a bada ceftriaxone, cloxacillin, clindamycin, KO cephalexin sannan a nemi taimako.

Idan ba za’a iya samun taimako cikin gaggawa ba, a tsaftace raunin sosai sannan a rufe shi acikin sassauƙan bandiji mai shara-shara wanda aka kashe ƙwayoyin cutar dake jikinsa. A riƙa yawan canza bandijin. Idan babu alamomin kamuwa da cuta har kwana 3, to a ɗora karayar, a rufe raunin sannan ayi filasta.

Targaɗe (ƙashi ya fita daga cikin gaɓa)

NWTND fa Page 32-2.png

A dai-daita ƙashin da yayi targaɗe da gaggawa. Iya daɗewarsa, iya wahala dakuma zafin da za’a ji wurin gyara.

Hanyar da aka fi bi ita ce a ja ƙashin ya rabu da gaɓar a hankali, sannan a saketa ta ɗanyi kara “ƙas” wurin komawa wurinta da ya dace. Bada maganin fita daga hayyaci kamar diazepam, dakuma maganin zugi kamar ibuprofen rabin sa’a kafin a gyara targaɗen. Idan aka kasa maida kashin cikin gabar, to a nemi taimako.

Bayan an gyara gaɓa mai targaɗe, a barta ta huta har sati 2 ko 3 ta amfani da ɗauri ko rataye. Ayi amfani da gamammen maganin zogi kamar ibruprofen gwargwadon buƙata. Zogin yana raguwa ta yadda za’a iya yin motsi, sai a raƙa fitar da gaɓar daga rataye duk bayan ‘yan sa’o’i sannan a juya ta a hankali. Idan kafaɗa ce, sai a saki hannun a barshi yana motsi gaba zuwa baya kuma a rika juya shi yana yin ‘yar da’ira. A yi a hankali da motsa gaɓar a cikin watanni 2 ko 3 masu zuwa. Targaɗe yana ɗaukar dogon lokaci kafin ya warke.

Idan zogi yayi tsanani bayan an gyara gaɓa me targaɗe, to wataƙila akwai karyayyen ƙashi.


Kafaɗa mai targaɗe

A ja ƙassan gaɓar saman da ƙarfi ayi ƙasa da ita. Ko kuma a sa mutumin ya riƙe bukiti mai ɗauke da ruwa me nauyin kilo 5 ko 7 har tsahon mintina 15 zuwa 20. Wannan zai ja gabar tayi ƙasa sannan zai sa gaɓar ta koma wurin ta.

hoto dake sama: wani mutum yana kwance akan tebur,alhali wani mutumin yana jan hannunsa ƙasa
hoton dake sama: ana jan allon kafaɗa.
Idan kafaɗar bata koma inda take ba, to ka tura saman allon kafaɗar da manyan ‘yan yatsun ka. Hannun zai yi ƙara ‘ƙat’ domin komawa inda yake.
KO KUMA

Juya hannun a hankali zuwa gareka, kamar haka. Yafi kyau a sami wani mataimaki wanda zai riƙe jikin mutumin kyam, domin ya zamo hannunsa ne yake motsi kaɗai.
wani mutum yana kwance akan bayansa, alhalin wani mutumin yana juya masa hannu.
rataye domin gaɓar dake riƙe da kafaɗa.

Bayan nan, ayiwa hannun rataye kamar haka domin kare shi daga fita daga jikin gaɓar:


Gwiwar hannu mai targade


Mataki na 1:
A saka mutumin ya kwanta, sannan a miƙar da gaɓar hannun tare da dantsen domin a dai-daita ƙasusuwan.

NWTND fa Page 34-1.png


Mataki na 2:

A sami mataimaki ya riƙe dantsen hannun sosai. Ja zira’in hannun zuwa gareka, sannan ka lanƙwasa gwiwar a hankali.
NWTND fa Page 34-2.png


Mataki na 3:

Yanzu kuma danna dantsen hannun ƙasa a lokacin da kake lanƙwasa gwiwar hannun. Zaka ji ƙara “ƙat”. A ɗaure gwiwar hannun domin gudun sake fitar ta daga mahaɗar.

hoton dake sama: an rataye hannu daga tsintisyar hannu zuwa gwiwa.

Faɗakarwa! Idan akwai tirjiya mai yawa, to a dakata! Domin zaka iya karya ƙashin. Sabodahaka, a rataye gwiwar hannun a haka sannan a nemi taimako.

Ɗanyatsan hannu mai targade

A ja ɗanyatsan hannu mai targaɗe daga jikin mahaɗarsa, sannan a tura ƙarƙashin sa ya koma wurin sa domin gyara shi.

NWTND fa Page 34-4.png
A ɗaure ɗanyatsa mai targaɗe
tare da na kusa da shi.

Murguɗewa ko kujewa a ƙarƙashin fata

NWTND fa Page 35-1.png
Alamomi
  • Kumburi
  • Zogi
  • Baƙi-baƙi ko jaja-jajan fata
Hanyar warkarwa
  • Huta: Kada ka danne ɓangaren dakaji rauni. Yi amfani da rataye ko sanduna har tsahon sati 3 ko 4.
  • Saka ƙanƙara: har tsahon mintina 30 duk bayan sa’a 2 zuwa 4. Sai a rage yawan sawar bayan ‘yan kwanaki.
  • Matsewa: a matse wurin sosai da bandiji.
  • Ɗagewa: a ɗage wurin akan matashi ko nannaɗaɗɗen zani a kodayaushe da farko, bayan nan kuma duk ‘yan sa’o’i na ‘yan kwanaki.


Waɗannan matakan zasu rage zogin dakuma kumburin. Idan akayi shi nan take kuma akai-akai, zai taimakawa raunin ya warke da wuri dakuma ƙaranta matsaloli masu ɗorewa.

Kada a matse ko danne raunin. Lanƙwashewa ko kujewar ƙarƙashin fata takan warke cikin sati 1 zuwa 2.

Yadda ake naɗa bandeji

nannaɗa bandiji a ƙafa dakuma idon sawu.
A fara kusa da ‘yan
yatsun ƙafar ko hannun.
A ɗaure sosai, amma kada a tamke. ’Yan yatsun ƙafar ko na hannun yakamata su zamu cikin ɗumi kma su kasance cikin dai-daitaccen yanayi.


This page was updated:05 Jan 2024