Hesperian Health Guides
Ƙuna
Ƙaramar ƙuna
Domin ƙaramar ƙuna, nan take a kwarara ruwan sanyi akan ƙonanniyar fatar har tsahon minti 15 zuwa 30. Wannan zai sanyaya kuma ya tsaftace fatar kuma zai taimaka wurin rage zugi.
A riƙa tsaftace wurin da sabulu marar zafi dakuma ruwa a lokacin da take warkewa. Zuma ko ruwan aloe vera suna gaggauta warkar da ƙaramar ƙuna, amma za’a sa ne kawai bayan ƙunar tayi sanyi.
Ƙaramar ƙuna yakamata ta warke a cikin sati 1 zuwa 3.
Ƙuna mai hatsari
Ƙuna masu hatsari sun haɗa da:
- Ƙuna mai zirfi (wadda ake kira ƙuna mai cikakken kauri). Bata ciwo har sai in an danna, saboda jijiyoyin aikawa da saƙwanni na wurin sun lalace. Bata canja launi idan aka danna.Launinta zai iya kasancewa dishi-dishi ko kuma idan zirfin yayi yawa zata iya kasancewa fari kamar kyandir, ko ruwan toka-toka ko ƙonannan baƙi.
- Babbar ƙuna. Babbar kuna itace wadda ta mamaye kaso 10% (kashi goma) ko fiye da haka na jiki. Koda kuwa bata da zirfi, babbar ƙuna kamar haka tana da hatsari. Zaka iya kintatar iya faɗin jiki daya ƙone ta amfani da fadin tafin hannu wanda ya kone. Shin kunar ta mamaye girman tafin hannu ɗaya? Wannan shi ne kwantankwacin kaso 1% na fadin jikin. Tafi 10 kuma shi ne kaso 10%.
- Ƙuna wadda ta rufe gaɓa, ko fuska, ko al’aura. Wannan zata iya yin mummunan tabo kuma zata iya nakasa mutumin, musamman yaro.
- Kuna haɗi da wasu raunukan.
- Ƙunar yara. Yara sun fi samun matsala wurin warkewa daga ƙuna, kuma idan har zai yiwo to a kula dasu a asibiti wanda yake da kayan kula da ƙuna.
Idan an sami kuna mai hatsari to a nemi taimako. A hanyar zuwa cibiyar lafiya, a ɗan riƙa bawa mutumin ‘yar maƙwarwa ta ruwa idan a faɗake yake. A rufe wurin daya ƙone da ƙyalle mai tsafta. Idan an sami ƙuna mai hatsari a guji tsoma wurin daya ƙone a cikin ruwan sanyi-zai iya sa yanayin zafin jiki yayi ƙasa sosai wannan zai iya sa mutumin ya kamu da sanyi mai hatsari. Yi ƙoƙarin kwantarwa da mutumin hankali.
Hanyar warkarwa
- Mutumin da yake da ƙuna babba ko mai zirfi nan da nan zai iya rasa ruwa a jikinsa, domin ruwan jiki ma yana ƙonewa ne a lokacin da yake fitowa daga ƙunar. A bashi ƙarin ruwa. Zaifi kyau ayi masa ƙarin ruwa ta jijiya, amma ruwan gishiri-da-sukari (ana kan aikinsa) mai yawa zai iya yin amfani ga wanda yake cikin hayyacinsa, kuma zai iya sha. Rashin ruwa zai iya haifar da girgiza sabodahaka, a lura da alamomin da aka jera a baya. Duba Kula da marasa lafiya (ana kan aikinsa) domin bayani akan ƙarin ruwa.
- Wurin da ya ƙone dakuma kewayensa su na da saurin kamuwa da cuta. A tsaftace ƙuna a wanke shi kullum da ruwa me gudana ko kuma a ɗan tsoma shi cikin ruwa mai tsafta na ɗan wani lokaci. Ɗan sabulu marar karfi zai taimaka amma kada ayi amfani da sabulu me hana ɗaukar cuta, ko iodine-zasu jirkinta warkewa. A hankali a cire yar matacciyar fatar kaɗan.
- A lulluɓe ƙunan da man antibiotic (me kashe ƙwayoyin cuta), sannan kuma a saka bandeji mai raga-raga tsaftatacce ko wani ƙyalle mai tsafta. A nannaɗe sosai, amma kada a hana kewayar jini. A sauya bandejin kullum, kuma koda yaushe idan yayi dauɗa. Bandeji mai datti zai iya jawo kamuwa da cuta. Zaka iya buƙatar jiƙa bandejin da ya maƙalƙale domin yayi saurin fita. A tabbatar da an nannaɗe kuma an raba kowanne ɗan yatsan hannu ko na ƙafa daya ƙone.
- A bada antibiotic idan ɗaya daga cikin waɗannan alamomin kamuwa da cutar ya bayyana: idan fata tana wari, ko tana fitar da ruwa, ko kuma ta ƙara ja ko zafi ko kuma mutumin ya fara zazzabi. A duba bayani akan antibiotics. A tabbatar rigakafin cutar tetanus bata lalace ba. Duba Rigakafi (ana kan aikinsa).
- Idan inda ya ɗuri ruwa ya fashe, to sai a tsaftace kewayen. Idan bai fashe ba, to kada ace za’a fasa. Buɗaɗɗun wuraren da suka ɗuri ruwa sun fi damar kamuwa da cuta.
- Kuna tana da matukar zafi. Kada ayi sakaci wurin bada maganin rage zafin ciwo mai karfi, irin su morphine ko kuma sauran magunguna nau’in opiates.
- Abinci mai gina jiki mai ɗauke da ƙarin yawan protein shi ake buƙata domin taimakawa ƙuna ta warke. Koda kuwa baka ji yunwa ba, to kaci abinci mai dauke da abubuwa masu ƙara kuzari sosai, sau 4 ko fiye da haka a rana da kuma ƙarin yan soye-soye. Abinci masu ɗauke da abubuwa masu ƙara kuzari sosai wanɗanda aka yi bayaninsu a sashin “Kyakkyawan abinci shi ke samar da kyakkyawar lafiya” (ana kan aikinsa) na musamman ne wurin gina jiki.
- Bangarorin da suka ƙone zasu iya sandarewa a kasa motsa su a yayin da suke warkewa, musamman ma idan ƙunar a kan gaɓa take. Sabodahaka, waɗannan gaɓoɓi dole ne a riƙa motsa su duk bayan ‘yan sa’o’i. Idan mutumin ba zai iya motsa wata gaɓa ba da kanta, to a taimaka masa a hankali.
Kamar yadda yake ga duk wani rauni mai tasiri, ka nemi taimako idan rashin lafiyar ta tsananta, ko kuma idan ba zaka iya bada taimakon da ake bukataba.