Hesperian Health Guides

Sepsis (cutar cikin jini)

A wanna kashin:

Sepsis na nufin cutar da ta yaɗu cikin hanyar jini. Tana da hatsari ,saboda ta na iya haifar da girgiza. Idan kana zargin akwai sepsis, to a nemi taimakon likita da sauri kuma a bada magani akan hanya.

NWTND fa Page 19-1.png
Alamomin cutar sepsis
 • Zazzaɓi ko kuma zafin jiki yayi ƙasa sosai
 • Bugun zuciya da sauri- wato bugun ya zarce sau 90 a minti ɗaya
 • Numfashi da sauri-wato sama da sau 20 a minti ɗaya
 • Wahalar yin numfashi
 • Fata ta dashe
 • Fitsari kaɗan
 • Ruɗewa ko fita daga hayyaci
 • Ƙarfin bugun jini yayi ƙasa


Alamomin da suka fi muhimmanci su ne zazzabi ko yanayin zafin jiki yayi ƙasa sosai, zuciya ta riƙa bugawa da sauri, da kuma numfashi da sauri. Idan mutum yana da 2 ko sama na waɗannan alamomin, to ayi masa maganin sepsis.

Magani

A nemi taimakon likita. A hanya:

 • A lura kuma ayi maganin duk wasu alamomin girgiza.
 • A bada ceftriaxone, ko ciprofloxacin dakuma clindamycin.
 • A tsaftace duk wani raunin da ya kamu da cuta, a cire matacciyar fata, a matse ɗiwa da ruwan ciwo. Domin koyon yadda ake matse ruwan ciwo, duba Matsalolin fata (ana kan aikin).
 • Idan mutumin yana numfashi sosai, a bashi abu mai ruwa-ruwa. A bashi yana kurɓa akai-akai.This page was updated:05 Jan 2024