Hesperian Health Guides

Raunuka masu zurfi

A wanna kashin:

Kowanne irin rauni mai zurfi ana barinsa ne a bude har ya warke. Raunukan da ba’a rufe su yadda ya dace ba nan-da-nan suke kamuwa da cuta. Hargitsatstsu, cakalkalallun raunuka musamman ma raunin suka, yakamata a riƙa tsaftace su sau biyu a rana da tafasashshen ruwa kuma a barsu a bude, ko a sake bude su, domin su warke daga ciki.

Raunuka masu zurfi za su iya kamuwa da cutar tetanus. To yakamata ayiwa mutumin rigakafin tetanus (Duba Rigakafi-ana kan aikinsa) dakuma maganin dafi na tetanus.

Idan baka da tabbas din ko rufe rauni abu ne mai kyau, to watakila ba haka bane.

Kada a rufe cizon dabba, raunukan suka, ko hargitsatstsu kuma cakalkalallun raunuka.


Cizon dabba

A tsaftarce cizon dabba sosai da sabulu da ruwa har tsahon minti 15. Cizon dabba yafi yiwuwar ya kamu da cuta, sabodahaka, a bada antibiotics.

Domin cizon kare, biri, jemage da
raccoon, nemi regakafin cutar rabies da
kuma immunoglobulin nan-da-nan
.
NWTND fa Page 16-1.png
Alamomin cutar rabies sunyi kama dana mura, amma ba kamar na mura ba na rabies suna da hatsari. Sabodahaka, idan baka da rigakafin cutar rabies ko immunoglobulin, nemi ma’aikatar lafiyar ku nan-da-nan.
NWTND fa Page 16-2.png

Raunukan wuka

Raunukan wuka masu zurfi yakamata a barsu a bude kuma a rika tsaftace su akai-akai. A bada cloxacillin ko clindamycin ana ganin alamar kamuwa da cuta.

Raunukan wuka a ƙirji ko ciki suna da matuƙar hatsari. A nemi taimakon likita. Domin sanin abin da za’a yi akan hanya, duba raunin wuka ga ƙirji, ko raunin wuka ga ciki.

Raunukan harbin bindiga

NWTND fa Page 17-1.png

Bi ƙa’idar tsayar da zubar jini ta matsewa—ta inda harsashen ya shiga data inda ya fita. Idan babu raunin wurin fita, to sai an cire harsashin. A nemi taimakon likita.

A kowanne irin yanayi, a wanke raunin sosai sannan a bada cloxacilin, clindamycin, KO cephalexin.

Idan akwai harsashi acikin ka, to a nemi taimako. Akan hanya, a ɗaga kan kaɗan da ‘yan nannaɗaɗɗun zannuwa ko filalluka. A rufe raunin da bandeji mai tsafta.

Akwai damar raunin harbin bindiga ya kamu da cuta. A nemi taimakon likita idan zai yiwu, tun kafin wata alamar cuta ta nuna.

harsashi ya daki ƙashin ƙafa ya tsaga shi.
Batu: Idan da akwai damar harsashi ya daki ƙashi, ƙashin zai iya tsagewa ko karyewa ta ciki. A ɗaure gaɓar kuma kada ayi amfani da ita har tsahon satuttuka. Duba karyayyon ƙasusuwa.
harsashi ya shiga cikin ƙashin ƙafa ya karya shi.


Fatsar kamun kifi

Mataki na 1: Mataki na 2: Mataki na 3:
Tura fatsar cikin fatar domin ta fito ta ɗaya gefen kamar haka: Yanke kan fatsar. Fito da sauran jikin fatsar.
ana tura fatsa cikin fata.
ana yanke kan fatsar.
za’a fito da sauran jikin fatsar.



This page was updated:10 Yun 2024