Hesperian Health Guides
Fita daga hayyaci
Kundin bayanan lafiya na Healthwiki > Sabon littafin A inda babu likita > Taimakon farko > Fita daga hayyaci
Abubuwan da sukafi jawo fita daga hayyaci sune:
- jijjiaga
- buguwar kai
- bugun zuciya
- mutuwar barin jiki
- cin guba
- karacin siga a cikin jini
- suma
- bugun zafi
- shan giya ko kwaya ko magani dayawa
Idan mutum ya fita daga hayyacinsa kuma baka san dalili ba, to a duba wadannan abubuwan nan take:
- Shin yana yin numfashi da kyau? Idan ba haka ba, a karkatar da kansa baya a sannan a jawo mukamikinsa da harshensa gaba. Idan wani abu ya makali a makogwaronsa sai a fitar da shi. Idan haryanzu baya numfashi to ayi masa busar numfashin cito nan take.
- Shin yana zubar da jini dayawa? Idan haka ne, ayi kokarin tsayarda jinin.
- Shin yana cikin halin jijjiga ne (wato fatarsa a dashe, kuma zuciyarsa tana bugawa bada karfi ba amma da-sauri-da-sauri)? Idan haka ne, a kwantarda shi a daga kafafunsa su zamo a tudu sama da kansa kuma a sassauta matsiwar kayan dake jikinsa.
- Shin ko bugun zafi ne (wato ya zamo fata ta kasanci babu gumi, amma ta kasance me zafi kuma tayi ja) idan haka ne, a saka shi a cikin inuwa, a daga kansa ya kasance a sama da kafafunsa, kuma a sanyaya masa jiki da jikakken tsumma (ayi amfani da ruwan kankara idan da hali) kuma ayi masa fifita.
Yadda ake kwantar da wanda baya cikin hayyacinsa:
fata ta dashe sosai alamar: (jijjiga, suma da sauransu) |
fata tayi ja kuma bata canja ba alamar: (a bugun zafi, mutuwar barin jiki, matsalar zafi,rauni a ka) |
Idan wanda ya fita daga hayyacin nasa yana da rauni a wuya ko gadun baya:
Yafi kyau kada a motsa shi har sai ya dawo cikin hayyacinsa. Kuma idan ana da bukatar a motsa shi, to a motsa shi a cikin matukar kulawa,domin idan wuyansa ko kuma kashin bayansa a karye yake, duk wani kokari na canja masa wuri zai iya haifarda karuwar matsalar da yake ciki. A duba raunuka ko karaya, amma a motsa mutumin a hankali gwargwadon iyawa. Kada a lankwasa bayansa ko wuyansa.
Kada a sake a bawa wanda baya cikin hayyacinsa wani abu ta baka.