Hesperian Health Guides

Matsalolin zafi dake buƙatar gaggawa

A wanna kashin:

Ƙandarewar tsoka saboda zafi, raguwar kuzari saboda zafi, da kuma rashin lafiyar da zafi yake haifarwa

NWTND fa Page 55-2.png

Yin aiki mai tsanani a cikin yanayi na zafi zai iya haifar da ƙandarewar ƙafafu, hannuwa, ko kuma ciki. Wannan wataƙila ya faru ne saboda jiki ya rasa gishiri dayawa a dalilin yin gumi.

Alamomi

Raguwar kuzari saboda zafi (cutar zafi) tana haifarda:

 • Jin ƙishirwa mai tsanani.
 • Rashin kuzari.
 • Ciwon kai.
 • Jin amai ko kuma ƙandarewar tsokar ciki.
 • Saudayawa fata takan zamo da gumi kuma zata iya kasancewa mai sanyi kuma a ɗashe.
 • Fata zata iya kasancewa birɗinɗin ko kuma tayi ƙuraje.
Ha NWTND fa Page 55-3.png
Magani
 • Huta a wuri mai sanyi. Cire ƙarin kayan dake jiki.
 • A bada ruwan gishiri-da-suga- cuɗanya ½ cokalin-shan-shayi na gishiri da lita 1 ta ruwa.
 • Bada wani abu mai ruwa-ruwa mai sanyi sosoi.
 • A hankali a mikar da in da ya ƙandare, a motsa ƙafafu ko kuma ayi tafiya a hankali.

Idan ba’a yi maganin raguwar kuzari saboda zafi ba zai iya tsanani ya koma mutuwar ɓarin jiki (wadda zafi yake haifarwa).

Harbin zafi (Mutuwar wani bangare na jiki saboda daina aikin kwakwalwa)

Harbin zafi wani irin yanayi ne mai matuƙar hatsari wanda yake faruwa saboda kasancewa cikin zafi na lokaci mai tsaho. Idan aka barshi ba tare da yin magani ba zai iya yin kisa.

Alamomi
 • Bugun zuciya da sauri dakuma saurin numfashi
 • Fata tayi ja, ɗumi (zafin data), bushewa ko kuma tayi danshi
 • Amai ko gudawa
 • Ruɗewa
 • Gajeriyar suma
 • Zazzaɓi mai zafi sama da 40° C
wata mace mai jiki tana riƙe da mahuci kuma kamar bata jin daɗi.
wani matashi yana gumi a lokacin da yake aiki a sarari.
Harbin zafi yana faruwa ne ga mutanen da suka kasa dawo wa dai-dai a cikin hanzari a lokacin da suka ji tsananin zafi:tsofaffin mutane, jarirai, marasa lafiya,mutane masu matuƙar ƙiba, dakuma mashaya giya su suka fi kamuwa. Harbin zafi yana iya faruwa ga matashi mai lafiya wanda yayi aiki ko motsa jiki na tsahon lokaci a cikin zafi. Irin waɗannan sukanyi ta yin gumi mai makon fatarsu ta bushe.


Magani

A sanyaya mutumin a cikin gaggawa:ta hanyar matsarwa zuwa cikin inuwa. A cire kayan jiki idan suna da yawa. Ayi masa fifita, kuma a goga musu ruwa mai sanyi da jiƙaƙƙen ƙyalle. A sa musu tarin ƙanƙara ko kuma kaya musu sanyi a wuya, hammata da kuma jikin al’aurarsu. Ko kuma a saka su cikin ruwan ƙanƙara, amma wannan yana da hatsari ga tsoho ko kuma wanda dama can bashi da lafiya.

Idan ya farfaɗo a bashi ruwan-gishiri-da-siga. Ko kuma a bashi duk wani abu ruwa-ruwa mai sanyi. Ayi a hankali kada ya ƙware:matsalar numfashi tana yawan faruwa ga wanda zafi ya harbe su.

Wanda ya samu bugun zafi ciwon zai iya ta’azzara a cikin gaggawa,sabodahaka yafi kyau a sami taimakon likita idan da hali.

Riga kafi

Domin kariya daga matsalolin da suke da alaƙa da zafi, a saka kaya masu launi mai haske kuma ayiwa fuska dakuma bayan wuya inuwa da malafa. Wuraren ayyuka da suke a rufe to a samar musu da isassun hanyoyin iska dakuma fanka. A riƙa yawan samun hutu akai-akai kuma asha ababen sha masu sanyi akai-akai. Amma a takaita shan giya a lokacin aiki ko kuma idan ana wasa a cikin zafi. Giya tana jawo rashin ruwa a jiki.

Kunar Rana

Matsalolin kunar rana sunfi tsananine ga masu farar fata. Sai fatar ta yi ja, tana ciwo, kuma tayi zafi, a waɗansu lokutanma ta ɗuri ruwa ta kumbura. Ɗurar ruwa saboda ƙunar rana kamar sauran ɗurar ruwa ce nan-da-nan zata iya kamuwa da cuta. Ƙunar rana a gurbi ɗaya bashi da hatsari, amma ƙunar rana mai yawa idan ya dau lokaci zai iya haifar da ciwon jejin fata. Duba Sashin Cutar Jeji (ana kan aikinsa).

NWTND fa Page 57-1.png

Ƙunar rana tana iya warkewa a karan kanta bayan ‘yan kwanaki. Aleovera ko kuma maganin zogi marar ƙarfi zai iya taimakawa. Wataƙila akwai hanyoyin waraka na gargajiya a wurin ku wanda zasu iya sanyaya dakuma warkar da fatar.

Kariya

A saka kaya ko malafa wadda zata lulluɓe fata a lokacin da rana tayi tsanani. Manshafawa na maganin rana wanda ake shafawa fata kafin a shiga cikin rana zai iya taimakawa wurin kariya daga ƙunar rana.


This page was updated:05 Jan 2024