Hesperian Health Guides
Raunukan kai
Kundin bayanan lafiya na Healthwiki > Sabon littafin A inda babu likita > Taimakon farko > Raunukan kai
Kanun bayannai
Alamomin sauƙaƙaƙƙen raunin ƙwaƙwalwa
- Ruɗewa ko fita daga hayyaci wanda yake warke wa da kansa bayan ɗan lokaci.
- Rashin tuna abin da ya faru.
- Disashewar gani na wani lokaci ko kuma ganin taurari.
- Jin amai ko kuma ma yin aman wanda baya jimawa.
- iwon kai, jiri ko jin kasala.
A huta har tsahon sa’o’i 24 sannan a sha matsaƙaicin maganin rage zogi kamar paracetamol ko acetaminophen, amma kar a sha ibuprofen ko aspirin domin zasu iya ta’azzara zubar jini a cikin ka. A lura da mutumin a sa’o’i 24 na farko. Idan ya yi barci, a riƙa tashin sa duk bayan ‘yan sa’o’i domin ganin ko zai iya amsa tambayoyi kuma yana iya yin tunani sosai. A ‘yan sa’o’i bayan jin raunin, idan mutumin ya ƙara ruɗewa, kuma ciwon kansa ya daɗa ta’azzara ko kuma ma ya fita daga hayyacinsa ko kuma yake yin kamar mai farfaɗiya, to akwai damar yana zubar da jini a cikin ƙoƙon kansa, sabodahaka ana buƙatar taimakon gaggawa na likita.
Alamomin raunin ƙwaƙwalwa matsananci
A nemi taimako idan anga wani daga cikin waɗannan alamomin:
- Fita daga hayyaci
- Ciwon kai matsananci ko mai ƙaruwa, canjawar gani ko rashin samun dai-daito
- Jin amai ko kuma yin aman
- Ruɗewa, canjawar hali, neman tashin hankali
- Bugun zuciya marar dai-daito (a hankali-a hankali ko da sauri-da-sauri)
- Numfashi da sauri-da-sauri marar shiga ciki ko kuma numfashi marar dai-daito (wani lokacin da sauri, wani lokacin a hankali)
- Fata mai danshi da ɗumi
- Yin kamar mai fyarfyaɗiya
- Jini ko ruwa mai haske me fitowa daga kunnuwa ko hanci
Waɗannan alamomin zasu iya faruwa sa’o’i bayan jin rauni:
- Baƙin cikin ido na tsakiya ɗaya-yafi-ɗaya girma
- Taruwar jini a kewayen idanuwa ko bayan kunne
Zubar jini daga kai
Raunukan kai suna da yawan zubar jini. Idan ka tabbatar babu rauni a ƙashin baya, to ka umarci mutumin ya zauna, ko ka tallafe shi yayi sama domin zubar jinin ta ragu. A matse wurin domin a tsaida zubar jinin, sannan a wanke raunin sosai kafin a rufe shi da dinki ko gam. Idan baka da kayan aiki zaka iya ɗaure gashin dake kewaye da wurin daga sama domin kame raunin, dakuma taimakawa wajan rufe shi, kamar wannan (hoton dake kasa):
Idan kai ya yanke sosai, to a lalibi rauni a jikin ƙoƙon kai. Idan kana kyautata zatun akwai rauni a kokon kai, to a matse kowanne gefe na kan, amma a guji danna ɓangare mai rauni na kan da ƙarfi.
Haɓo
A matse hanci sosai, kasan guringuntsin hancin.
A matse sosai har minti 10 — kada a tsaya wai domin a duba ko jinin ya dena zuba ko kuma jinin ya cigaba da fitowa. Idan jini ya cigaba da fita har bayan minti 10, to a sake matsewa har wani minti 10.
Duk da cewa haɓo yana yin sauƙi (nan-da-nan), amma duk wani zubar jini da aka kasa tsaidawa yana da hatsari. A lura da haɓo sosai musamman a wurin tsofaffin mutane.
Kariya
Shafa ɗan man basilin kaɗan a cikin hancin zai iya hana bushiwar da hanci yake yi ta sake haifar da zubar jinin.
Ƙwaƙwular hanci na daga cikin abubuwan dake haifar da haɓo.