Hesperian Health Guides

Makaman ‘yan sanda

A wanna kashin:

NWTND fa Page 41-1.png

Kayi a hankali: mutanen dake taimakon waɗanda ‘yansanda suka raunata sau dayawa suna faɗawa matsanancin tashin hankalin ‘yan sanda su da kansu. Yi kokarin fitar da kanka dakuma mai raunin daga cikin matsalar da zata iya faruwa.

Barkonon tsohuwa dakuma iskar-gas-mai-yaji

Idan zaka iya barin wurin da aka saka iskar-gas-mai-yaji ko aka fesa barkonon tsohuwa, to a hankali zaka washe Iskar-gas-mai-yaji tafi saurin washewa, barkonon tsohuwa yakan ɗau tsahun sa’a ɗaya ko fiye.

Kada ka taba kwanson iskar-gas-mai-yaji da hannayenka. Suna da zafi kuma zasu ƙona ka idan ka ɗauke su nan take.

NWTND fa Page 41-2.png

Hankicin da aka jiƙa shi da ruwa ko kal (vinegar) aka ɗaura saman baki da hanci yana bada kariya ‘yar kadan.

  1. A lura da numfashi. Barkonan tsohuwa zai iya haifar da matsananciyar matsalar numfashi, musamman a wurin mutane masu ciwon asma. Wannan zai iya zama abin tsoro mai girma. Taimaki mutumin ya sami nutsuwa.
  2. A watsa ruwa mai yawa a cikin idanuwa (kusa da hanci) zuwa wajen (idanuwa).
  3. Cire tufafi waɗanda ke ɗauke da barkonon tsohuwar kana isa wurin da babu shi ko wani sanadarin.
  4. Tsaftace fata, wuri-bayan-wuri (ko kuma a jira har sai an daina jin yajin: Jika tsumma da man sinadari ko man girki. Goge wani ɓangare na fata da wannan tsummnan me mai. Sannan ka goge man da sauri da wani tsumman wanda aka jiƙa da sinadarin alcohol. Idan aka bar maikon sama da tsahon daƙiƙa 30, to zata hadu da sinadarin kuma su ƙona fata. Idan baka da mai da spirit, to yi amfani da ruwa mai yawa. Ko kuma ka jira, a hankali yajin zai huce.


Wanke ido da baki domin rage radadin barkonon tsohuwa

A sami ƙaramar kwalaba a cika ½ da ruwa, ½ da maganin ciwon ciki ‘antacid’ (me dauke da sinadarin aluminum ko magnesium kamar Maalox).

Domin maganin yajin a ido, a buɗe idon a kwara (wannan haɗin da aka anbata a sama) ya shiga ta ciki (kusa da hanci) ya fito ta ɗaya gefen (kusa da kunne).

Domin maganin yajin baki kuma, a umarci mutumin ya guntsi haɗin a bakinsa ya kuskura ya fesar.

Wannan haɗin zai iya taimakawa wajan wanke yajin daga jikin fata.

Ƙarin waɗansu makaman na ‘yansanda

Harsashin ruba, kwanson iskar-gas-mai-yaji, bindigar ruwan zafi, da kuma kulake duk waɗannan na iya haifarda zubar jini, karayar ƙasusuwa ko raunika ko taruwar jini a cikin jiki. Raunikan ido da kai suna da hatsari. A duba mutun daga sama zuwa ƙasa. A lura da alamomin taruwar jini a cikin jiki ko girgiza: (kamar su) alamun suma, ɗashewar fata, ko jin kasala. Duba sashin Matsalolin idanu (ana kan aikin sa) domin (bayani) akan raunukan ido.


This page was updated:05 Jan 2024