Domin kare kai daga mafiyawancin guba, a sha ruwa mai yawa cikin gaggawa domin fitar da ita (daga cikin jiki). Shan ‘activated charcoal’ zai taimaka wajan zuƙe gubar (daga cikin jiki) wadda zata fita ta bayan gida daga baya. Idan kuma an san gubar da aka sha, duba jadawalin dake ƙasa domin bayanin abinda yakamata ayi.
Ga babba: A bada ma’aunin gram 50 zuwa 100 na activated charcoal wanda aka cuɗanya da ruwa.
Ga yaro: A bada ma'aunin gram 1 (na activated charcoal) ga duk kilo 1 na nauyin (yaro) a cuɗanya da ruwa.
Activated charcoal bashi da tsada kuma magani ne mai mahimmanci da yakamata a ajiye shi a cikin magungunan (bada taimakon farko).
Kada a bada ruwag awayi ko wani abu ga wanda baya numfashi sosai ko ya fita daga hayyacinsa. A tuna: tabbatar da numfashi a koda yaushe, shi ya fi komai muhimmanci.
Yin amai ba koda yaushe ne yake taimakawa ba idan an hadiyi guba, kuma zai iya zama hatsari. Idan wani ya haɗiyi sinadarai masu guba kamar acid ko lye ko fetir ko kananzir ko turpentine ko kuma yana samun matsala wurin numfashi (a dalilin hadiyar gubar) to kada yayi ƙoƙarin aman gubar.
Idan ana so a gwada yin amai (saboda hadiyar guba) to ayi shi da gaggawa a ‘yan sa’o’in farko (daga hadiyar gubar). Domin a jawo amai a taɓa bayan maƙogwaro da ɗanyatsa ko kuma a haɗiye cikin cokalin gishiri.
A nesanta duk wani abu mai guba daga yara.
Kariya
Za a iya kare kai daga guba. Ayi wa duk wata guba da kuma magani fitacciyar alama. A nesanta su daga yara a kullanlan wuri ko mai tsaho. Kada ayi amfani da mazuban guba wajan ajiye abinci ko abin sha koda kuwa an tsaftace su tun farko. Har’ilayau kuma kada a ajiye guba a cikin mazuban abinci ko abin sha.
Guba gamagarin hanya ce da mutane ke amfani da ita wajan kashe ko cutar da kansu. Kulle gubobi, bindigogi da kuma sauran abubuwa masu hatsari hanya ce mai matuƙar tasiri wurin hana kashe kai. Domin ƙarin bayanin kulawa da wanda yake so ya kashe kansa, duba Lafiyar tunani (ana kan aikinsa).
GUBAR SINADARAI
Nau’o’in sinadarai
Alamomin amfani da guba
+ Abinda ya kamata ayi
Sinadarai masu zaizayewa ko ƙona:
Sanadarin Amoniya
Batira
Sanadarin acid
Ababan wanki
Sodar wanki
Lye
Ƙarin yawu.
Zafin baki, maƙogwaro, ƙirji, ciki ko baya.
Amai.
Wahalar hadiya.
Kada ayi ƙoƙarin amayarwa.
Activated charcoal amfaninsa kaɗanne anan.
A bada ruwa gwargwadon iyawa. Kuma a nemi taimako.
Acids ko bases. Waɗannan sinadaran suna ƙona cikin jiki.
Dangogin man fetir:
Fetir
Turpentine
Sinadarin rage kaurin fenti
Kerosene
Kananzir
Phenol
Carbolic acid
Camphor
Pine oil
Wahalar yin numfashi.
Tari, ƙwarewa, kakari.
Zazzabi.
Fita daga hayyaci.
Numfashin zai riƙa warin gubar.
Kada ayi ƙoƙarin yin amai.
Kada a bada activated charcoal.
A bada ruwa mai yawa.
A wanke dangogen fetir daga jikin fata da gashi sannan a cire gurɓatattun kaya.
Kunna wuta a cikin gida zai iya sa mutum ya shaƙi sinadarin cynanid wanda yake cikin abinda ake konawa. Zaka iya jin maƙaƙin almond me ɗaci a cikin hayakin dake ɗauke da cyanide.
Organophosphates da carbamate: Ana samun Organophosphates da carbamates a wadansu daga cikin magungunan kashe ƙwari wadanda suka haɗa da:
malathion
parathion
Rage bugun zuciya, raunin tsoka, matsalolin numfashi.
Zubar da majina, hawaye, dalalar da yawu.
Suma
Numfashi zai riƙa warin makamashi ko tafarnuwa.
Matsaloli masu hatsari ga rayuwa zasu iya faruwa bayan ‘yan kwanaki da cin gubar. Matsalolin jijiyoyin sadarda saƙwanni masu ɗaukar lokaci basu warke ba zasu iya bayyana bayan ‘yan makwanni.
A lura da matsalolin numfashi kuma a bada numfashin ceto idan da buƙatar hakan.
Kada a bar mutumin ya sha ko ya haɗiyi wani abu har sai anga yana numfashi.
Sha ya wuce ƙa’ida zai iya jawo mutum ya daina numfashi.
Giya:
Sha dayawa zai iya jawo mutum ya daina numfashi.
Amai.
Ruɗewa.
Fita daga hayyaci.
Numfashi a hankali ko marar dai-daito.
Fita daga hayyaci. Ruɗewa, ko kuma canjawar tunani, numfahi ba akai-akai ba ,ji ko kuma kama da marar lafiya, duk za su iya zamowa alamun ciwon siga mai bukatar taimakon gaggawa
A lura da numfashin mutumin kuma a busa numfashin ceto idan ya zamo dole.
A juya shi ta kwibi daya domin hana ƙwarewa idan yayi amai.
A bashi ɗumi (ta hanyar lulluɓewa ko kuma wani abun.)
Idan mutumin zai iya shan wani abu, to a bashi ruwan-gishiri-da-suga (ana kan aikinsa).