Hesperian Health Guides

Raunukan ƙashin baya dakuma wuya

A wanna kashin:

A cikin kashin baya akwai laka, wadda haɗe take da ƙwaƙwalwa. Rauni ga laka zai iya haifar da naƙasa ta tsahon rayuwa ko mutuwa. Idan akwai dama to zaka iya taimakon wanda ya ji rauni a laka ta hanyar hana shi ƙara jin wani raunin ta hanyar tsaida wuyansa da bayansa cak!

Mu ɗauka ƙashin bayan ya sami rauni bayan hatsarin mota, babir, ko faɗuwar keke, kowacce irin faɗuwa babba ko duka a baya ko kai. A riƙe wuyan da bayan cak ta yadda baza su iya juyawa gefe-da-gefe ko ƙasa-da-sama ba, wanda zai iya haifar da ƙarin rauni ga ƙashin bayan. Ɗaura naɗin kaya, ko soso ko wani abun kewaye da wuyan domin hana shi motsi.

an nannaɗe riga an saka a kewayen wuyan mutum.


Kada a bada maganin zogi har sai an tabbatar babu rauni a ƙashin bayan. Zogi yana sa mutumin ya tsaya cak.

Alamomin rauni a ƙashin baya
  • Ciwo ko laushin wuya ko ƙashin baya.
  • Rashin ƙarfi ko rashin motsi a hannuwa ko ƙafafu.
  • Sagewar hannaye ko ƙafafu.


Waɗansu alamomin raunin ƙashin bayan sun haɗa da rashin iya riƙe fitsari ko kashi, wahalar yin numfashi, ko girgiza. Idan ana shakka, yafi cancanta a kula da mutumin kamar yana da rauni a ƙashin baya.

ga wani mutum kwance akan bayansa, yana ɗaga hannayensa.

Domin binkicen raunin ƙashin baya,ace da mutumin ya kwanta a rigingine akan bayansa yakuma ɗaga gwiwowinsa na ƙafa. Sannan ace ya ɗaga hannuwansa. Shin yana iya motsa su? Shin yana jin ciwo? Taɓa ‘yan yatsunsa na hannu da na ƙafa. Shin yana jin taɓawar? Shin yana jin mintsinin ka?

Idan akwai wani wuri a jikin daga ƙasa inda mutumin baya iya motsawa ko kuma ji, idan an taɓa,to ƙashin bayan ya karye. Amma da taimakon wadɗansu za a iya taimaka masa kada matsalar ta sake dagulewa.

wani mutum yana magana da waɗansu mutane 2 a lokacin da suke shiryawa domin juya wata mata (saboda taji cewa a kashin bayanta).
A juya “uku”. ɗaya, biyu...
A riƙe kan a miƙe da sauran jikin, a tsai da wuyan ƙyam.
mutanen suna juya jikin alhalin mutumin farko yana magana.
uku

Idan yana ji idan an taɓa shi kuma yana iya motsi, to a taɓa ƙashin bayan shi kansa. A hankali a juya shi gefensa domin a duba bayansa gaba ɗaya kamar yadda aka nuna a sama.

A riƙe kan da wuyan da bayan a miƙe a lokacin da ka ke juya shi. Sannan a tsayar da jikin a kuma taɓa duk tudun ƙashin bayan, tun daga bayan kai har zuwa tsakanin ɗuwaiwaka. Domin aji ƙashin da ya fita daga inda yake, ko ya karye ko zogi.

A sake yin amfani da ƙarfi na bai ɗaya a juya shi yadda yake a hankali.

(Idan mutumin yana amai, to a motsa hannunsa ko kuma a saka wani abu a ƙarƙashin kansa domin ya kasance a gefensa.)

Idan da akwai zuge ko laushi, to mutumin yana bukatar hoton kashi domin ganin ko da ‘yan ƙananan karaya a ƙasusuwan. Yana da buƙatar ya huta a wuri ɗaya, ana juya shi duk bayan ‘yan sa’o’i amma a tsaida wuyan dakuma bayan wuri guda, har sai cewon ya ragu a cikin sati ko makamancin haka

NWTND fa Page 22-3.png

Domin motsa mutumin, a juya shi gefe sannan a saka dogon katako mai faɗi, kamar ƙofar katako a ƙarƙashin sa. Sannan a juya shi zuwa kan katakon. Ayi amfani da ‘yan dogwayin tef ko ƙyallaye masu ƙarfi domin tabbatar da kai, ƙirji dakuma cinyoyinsa a kan katakon. Idan ya zama dole a barshi akan katakon har zuwa tsahon lokaci, to sai a riƙa juya shi gefe-da-gefe duk bayan ‘yan sa’o’i.

Mutumin daya sami rauni a ƙashin bayansa yana buƙatar dogon-lokaci na waraka ta zahiri. A nemi taimako daga waɗanda suke da ƙwarewa, ko kuma ayi amfani da littafi kamar Disabled Village Children (Yaran Ƙauye masu Nakasa) ko A Health Handbook for Women with Disabilities (Littafin Hannu na Mata masu Nakasa)], dukkaninsu ana samu a Hesperian Foundation.


This page was updated:05 Jan 2024